Ministoci 2 sun halarci taron bai wa matasa 1000 tallafi a Kano

Ministoci biyu na Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da tawagar APC, sun isa Jihar Kano, domin halartar taron bai wa matasa da mata 1,000 tallafi.

Ministoci 2 sun halarci taron bai wa matasa 1000 tallafi a Kano

Ministoci biyu na Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da tawagar APC, sun isa Jihar Kano, domin halartar taron bai wa matasa da mata 1,000 tallafi.

Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman, da Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, sun halarci taron ne, domin shaida bai wa matasa 1000 tallafin Naira 50,000.

Mamba a Kwamitin Gudanarwa na Kwalejin Ilimi (FCT), Potiskum, Yobe, Nasir Bala Ja’oji, ya shirya.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Ja’oji ke bai wa matasa da mata tallafi ba.

A watan Satumban 2024, ya tallafa wa mutum 484 tallafin kuɗi.

A rabon tallafin, mutum huɗu, sun amfana da Naira miliyan ɗaya kowannensu, yayin da mutum 200 suka samu Naira 100,000 kowanne.

Har ila yau, mutum 100 sun samu Naira 50,000 kowanne, wasu kuma 100 sun samu Nairs 20,000 kowanne.

Haka kuma, mutum 30 sun samu babura, yayin da 50 suka samu keken ɗinki.

Da ta ke jawabi a wajen taron, Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman, ta bayyana cewa wannan tsari ya nuna karfin haɗin kai da jajircewa wajen tallafa wa mata da ci gabansu.

“Yayin da muke murnar tallafa wa matasa da mata 1,000 a yau, muna tunatar da kanmu cewa har yanzu akwai aiki da yawa a gaba.

“Duk da haka, tare da jagoranci da hangen nesan Shugaba Tinubu, muna da ƙwarin gwiwar cewa Najeriya za ta ci gaba da samun nasarori wajen tallafa wa mata.

“Ina yaba wa Honarabul Ja’oji saboda ƙoƙarinsa wajen tallafa wa matasa da mata. Shirinsa na wannan tallafi yana nuna kishinsa wajen bai wa mata damar cin gajiyat tattalin arziƙin ƙasa.”

Ta ƙara da cewa ma’aikatarta a shirye ta ke don yin aiki tare da Ja’oji da sauran masu ruwa da tsaki don ci gaban mata.

A nasa ɓangaren, Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, ya yaba wa Ja’oji saboda tallafa wa matasa.

Ya ce irin wannan shiri ya dace da manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu na tallafa wa matasa.

“Mun yi imanin cewa tare da haɗin gwiwa, za mu iya gina kyakkyawar makoma ga matasan Najeriya. Ma’aikatarmu tana jajircewa wajen tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta ci gaban matasa, kasuwanci, da ƙirƙire-ƙirƙire.

“Irin wannan ƙoƙari abin koyi ne ga duk wanda ke sha’awar samar da ci gaba. Muna fatan cewa dukkanninmu za mu haɗa kai don ganin cewa matasa suna samun dama mai kyau don cimma burinsu.”

Tun da farko, Nasir Bala Ja’oji, ya bayyana cewa wannan taro wani ɓangare ne, na burinsa na tallafa wa matasa da mata don ci gaba da goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa, a baya-bayan nan na bayar da tallafin Naira miliyan 88 ga gamayyar matasan APC na Kano don ƙara wa wannan ƙoƙari armashi. Burina shi ne ci gaba da bai wa shugaban ƙasa gudunmawa don cimma manufofinsa.

“Mun tsara wannan shiri ne domin rage raɗaɗin matsalolin tattalin arziƙi da ake fuskanta. Ta hanyar tallafa wa matasa da mata, ba wai kawai muna inganta rayuwarsu ba ne, har ma muna bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.”

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, Daraktan Cibiyar Samun Nasara ta Ƙasa, Baffa Babba Danagundi, da sauransu.