Ministoci: Me ya sa Tinubu ya damƙa tsaro a hannun ’yan Arewa?
Shin haƙa za ta cim-ma ruwa a ɓangaren tsaron Najeriya da Tinubu ya damƙa wa ’yan Arewa?
Yankin Arewacin Najeriya mai fama da ta’addancin ’yan bindiga da masu iƙirarin jihadi ne zai jagoranci ɓangaren tsaron kasar a sabuwar Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shin da hakan za a kawo ƙarshen abin da ke ci wa yankin tuwo a ƙwarya na ayyukan ta’adancin ’yan bindiga da masu iƙirarin jihadi irinsu ƙungiyar Boko Haram da ISWAP da sauransu?
- Tinubu ya ba Badaru Ministan Tsaron Najeriya
- Sojoji sun kama jirgin ruwa makare da lita 350,000 na man dizel din sata
A jerin ministocin na Tinubu, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ne sabon Ministan Tsaro.
Takwaransa na Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ne karamin minista, kuma daga jihar da ’yan bindiga suka fi ci wa tuwo a ƙwarya.
Wannan ne karon farko bayan dawowar Najeriya kan tafarkin dimokuraɗiyya da irin haka ta faru, aka samu ministoci biyu a ma’aikatar tsaro kuna dukkansu ’yan Arewa.
Wannan ƙari ne a kan Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Christopher Musa wanda Tinubu ya nada daga yankin na Arewa.
Hassan Abubakar daga Jihar Kano shi ne Babban Hafsan Sojin Sama, sai Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaron, Nuhu Ribadu, duk daga yankin.
A cikin minstoci kuma Tinubu ya damƙa Ma’aikatar Harkokin ’Yan sanda a hannun yankin, inda tsohon gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Geidam yake minista, tare da Iman Sulaiman-Ibrahim a matsayin ƙaramar minista.
Bugu da ƙari, Sa’idu Alkali daga yankin na Arewa shi ne Ministan Harkokin Cikin Gida.
Shin kuna ganin haƙa za ta cimma ruwa, wajen murƙushe matsalolin tsaro a yankin da ma Najeriya?