Ministocin Buhari 5 sun rasa tikitin neman Gwamna a APC
Biyar daga cikin ministocin Buhari sun rasa samun tikitin neman takarar Gwamna a Jihohinsu daga jam’iyyar APC kamar yadda maiyar mu ta sanar. Bayan kammala zabukan fidda gwani na jam’iyyar APC ministocin dai sun yi tunanin zasu iya amfanin alfarmar Shugaba Buhari don samun tikitin takarar Gwamna daga jam’iyyar APC amma aka samu aka sin […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Biyar daga cikin ministocin Buhari sun rasa samun tikitin neman takarar Gwamna a Jihohinsu daga jam’iyyar APC kamar yadda maiyar mu ta sanar.
Bayan kammala zabukan fidda gwani na jam’iyyar APC ministocin dai sun yi tunanin zasu iya amfanin alfarmar Shugaba Buhari don samun tikitin takarar Gwamna daga jam’iyyar APC amma aka samu aka sin haka.
Ministocin sun hada da: Adebayo Shittu jihar Oyo da Aisha Jummai Alhassan jihar Taraba da Mustapha Baba Shehuri jihar Borno da Mansur Dan-Ali jihar Zamfara da kuma Usani Usani jihar Kuros Ribas.