‘‘Ministocin Buhari kalubale ne ga yarbawa’’

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Aremu Olusegun Osoba ya bayyana mukaman manyan ministocin da Shugaba Buhari ya bai wa yankin Kudu maso yamma a matsayin kalubale ga kabilar Yarabawa. Don haka ya zama wajibi a kansu da su tabuka abin kirki, domin makomar siyasar yankin  ta ta’allaka ne a kan irin kwazo da bajintar da za […]

‘‘Ministocin Buhari kalubale ne ga yarbawa’’
‘‘Ministocin Buhari kalubale ne ga yarbawa’’

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Aremu Olusegun Osoba ya bayyana mukaman manyan ministocin da Shugaba Buhari ya bai wa yankin Kudu maso yamma a matsayin kalubale ga kabilar Yarabawa. Don haka ya zama wajibi a kansu da su tabuka abin kirki, domin makomar siyasar yankin  ta ta’allaka ne a kan irin kwazo da bajintar da za su nuna, don haka dole ne su himmatu don ganin sun samar da sauyin da ’yan Najeriya ke muradi.
Ya kuma ba tsohon Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Fashola shawarar da ya yi aiki kafada da kafada da Ministan Sufuri, Rotumi Amaechi, don ciyar da kasa gaba saboda da muhimmancin ma’aikatun da ke a karkashin kulawarsu da kuma rawar da za su iya takawa wajan ci gaban kasar nan.
“A matsayina na shugaba a kabilar Yarbawa kana datijjo mai fada a ji, ina sanar da ku cewa mukaman manyan ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ba Yarabawa, kalubale ne a gare su, dole ne su jajirce su ba mara da kunya,” inji shi.
Shi ma Gwamnan Jihar Oyo, mai makwabtaka da Jihar Ogun, Sanata Abiola Ajimobi, yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bisa ba dan jihar, Adebayo Shitu Ministan Sadarwa. Ya kuma ba da tabbacin cewa daukacin jama’ar jihar za su ba ministan cikekken goyon baya, domin ganin ya samu damar gudanar da aikinsa cikin nasara.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a sa’ilin da sabon Ministan Sadarwar ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa. Kana ya kara da cewa dole ne su yaba wa Shugaba Buhari, su kuma nuna godiyarsu a fili domin Jihar Oyo ta dade ba ta samun manyan ministoci sai dai kawai kananan da ake ba ta, sai ga shi a yanzu Shugaba Buhari ya ba su babban minister; don haka dole ne su yaba masa.
A nasa bangaren, Ministan Sadarwa Adebayo Shittu ya nuna godiyarsa ga Gwamnan Jihar Oyo bisa gudunmowar da yake ba shi, wanda ya ce kyakkyawar alakarsu ba ta yau ba ce. Ya kuma sha alwashin ba jihar kyakkywan wakilci a majalisar zartarwa.