Ministocin Buhari: Kaza a kan baragurbin kwai
Tun lokacin da aka ce Shugaba Buhari ya aikawa da majalisar dattijai sunayen ministocinsa na shiga du’a’in Allah yasa a fiddo a’i daga rogo, kasancewar ana gane mutum ne daga abokansa, kamar yadda wani malami ya ce “ka nuna min abokanka ni kuma zan gaya maka ko kai waye” lokacin da na ga sunayen ministocin […]
Tun lokacin da aka ce Shugaba Buhari ya aikawa da majalisar dattijai sunayen ministocinsa na shiga du’a’in Allah yasa a fiddo a’i daga rogo, kasancewar ana gane mutum ne daga abokansa, kamar yadda wani malami ya ce “ka nuna min abokanka ni kuma zan gaya maka ko kai waye”
lokacin da na ga sunayen ministocin shugaba Buhari na dade ban gusa daga inda nake zaune ba, saboda ganin sunayen da ban yi zato ba.
Zance na gaskiya mafi yawa daga cikin ministocin da Shugaba Buhari ya zaba ba su cancanta ba, saboda mafi yawa daga cikinsu babu wanda bai rike babban mukami ba a kasar nan ba, amma me za a ce ya yi wa yankinsa da ba za manta da shi ba?
Shin wai ina mutanenka na tun asali wadanda suke tare da kai kuma kake da yakinin gaskiyarsu?
Shin ka tuna mafi yawa daga cikin wadannan ministocin naka daga jam’iyyar adawa suka fito sakamakon gaza cimma burinsu na samun mukamai, kuma sun yi mulki a baya tare da shugabannin da suka shude? Shin me ya sa har yau dai su ne?
Na dauka duk wanda Shugaba Buhari zai yi mulki da shi sai ya tabbatar da cikakkiyar cancantarsa da kuma yadda jama’ar gari ke da kyakkyawan yabo a kansa?
Kafin bayyana sunayen wadannan ministoci na ji ra’ayoyin mutane da yawa game wadanda suke hasashen Shugaba Buhari zai nada a matsayin ministocin nasa bisa yarda da nagartarsu da al’ummar ta yi, amma bayan bayyanar waccan jadawali sai na ga bai fi mutum biyu ba daga cikin fatan da jama’ar gari ke yi ba.
Babu shakka a farkon al’amari Shugaba Buhari ya soma da abin yabo da yabawa a lokacin da ya yi nadin wadannan mukamai.
1.Shugaban Hukumar Hana Fasakwauri (Costom)
2.Shugaban Hukumar Sojojin kasa.
3. Sakataren gwamnatin tarayya, da dai sauraransu.
Duka wadannan mukamai da ya bayar mafi yawa daga cikin ’yan Najeriya sun yi farin ciki da su,
amma me ya sa a zaben ministoci aka samu kawalwalniya?
An ya Shugaba Buhari ne ya zabi wadannan ministoci da kansa kuwa? Idan kuwa har da gaske shi din ne babu abin da zan ce sai dai Allah ya sa ‘tsakuwar ido kar ta hana ido budewa.’
Mai girma Shugaban kasa na san kana sane da cewa gaskiyarka da amanarka yasa ’yan Najeriya suka cure waje guda suka zama tsintsiya madaurinki daya, suka ce sun ji, sun gani sai ka yi shugabancin kasar nan, har ila yau bayan zamanka shugaba a Najeriya suna da kyakkayawan zaton za ka yi aiki kafada da kafada da mutanen da suka cancanta don ganin an samu sabuwar Najeriyar da ta dade a cikin karakainar firgicin rayuwa.
Na ji wasu na cewa wai ka zabi wadannan mutane ne a matsayin ministocinka bisa irin gudummuwar da suka ba ka a lokacin yakin neman zabenka, shin hakan da gaske ne ko a’a?
Koma dai yaya ne kada ka manta talakawan kasa su ne suka yarda cewa, wannan karon dole sai kai, ko kuma a yi juyin juya hali, saboda tsanani da ukubar da suka fuskanta a hannun gwamnatin da ka gada.
Kuma kar ka manta duk wanda ya zama wani a shekarar 2015 Allah ne ya zabe shi kuma kai ne sanadi, saboda haka babu wanda ya maka alfarma kai ne ka yi masa.
A karshe ina bai wa Shugaba Buhari shawara a cikin ragowar ministocin da bai nada ba don Allah ya yi kokari ya ga ya cika wa ’yan kasa burinsu na ganin ya yi aiki da wadanda ake kyautata musu zato. Na gode.
Abu Hidaya ya rubuto makalar daga birnin Kano, kuma jigo ne a Tsangayar Adabin Hausa.