Ministocin da za a zuba wa idanu

Yanzu tunda Shugaba Buhari ya rantsar tare da kaddamar da sabuwar Majalisar Zartarwar ta tarayya, bayan ya bayyana wa kowane minista ma`aikatar da aka tura shi da kuma yin gargadi gare su da sababbin da tsofaffin manyan Sakatarorin ma`aikataun gwamnatin tarayya, a kan lallai su tsaya tsayin daka su yi wa kasa aiki, bisa ga […]

Ministocin da za a zuba wa idanu
Ministocin da za a zuba wa idanu

Yanzu tunda Shugaba Buhari ya rantsar tare da kaddamar da sabuwar Majalisar Zartarwar ta tarayya, bayan ya bayyana wa kowane minista ma`aikatar da aka tura shi da kuma yin gargadi gare su da sababbin da tsofaffin manyan Sakatarorin ma`aikataun gwamnatin tarayya, a kan lallai su tsaya tsayin daka su yi wa kasa aiki, bisa ga kamanta gaskiya da adalci, don samun CANJIN da jam`iyyarsa ta APC, ta yi wa `yan kasa alkawaringwamnatinta za ta kawo. To, bari mu duba wasu daga sababbin ministocin da aka nada da ma`aikatun da aka tura su da kalubalen da za su fuskanta. Jama`ar ciki da wajen kasar nan sun san dai cewa, babban kalubalen da kasar nan take ciki yau sama da shekaru shidda, shi ne, na tabarbarewar matakan tsaro, musamman daga rikicin `yan tada kayar baya na kungiyar Jama`atu Ahlis Sunnah Lid-Da`await Wal Jihad, wato Boko Haram da suke cin karensu ba babbaka, musamman a jihohin Barno da Yobe da Adamawa na shiyyar Arewa maso Gabas, da ma wsu sauran sassan kasar nan. Hare-haren da gwamnatin Buhari ta sha alwashin kawo karshensu nan da karshen wannan shekarar. Akwai kuma batun tabarbarewar tattalin arzikin kasa da na zamantakewar yau da kullum da rashin ayyukan yi, musamman tsakankanin matasa, da suka kwashi kashi 60 cikin 100 na mutanen kasar nan, koma baya ga ayyukan noma da kiwo, da suke haddassa wa kasar nan kasha sama da Naira biliyan 22 duk shekara, wajen shigo da nau’in abinci da abin sha, alhali za mu iya noma abincin da muke bukata, har mu fitar da rara zuwa kasashen waje.

Bari mu fara da wanda aka nada sabon Ministan tsaro, wato Birgediya Janar Mansur dan-Ali mai ritaya, da ake sa ran ya kawo karshen wannan ta`addanci na `yan kungiyar Boko Haram da ire-irensa. Masana harkokin tsaro suna hasashen cewa, idan har sabon Ministan tsaron ya iya kwantar da hankalinsa wajen yin aiki, tare da manyan Hafsoshin Dakarun kasar nan da ya tarar suna wannan yaki, tare da kara sama musu wadatattun kayayyakin yaki da horarwa da kula da jin dadinsu, sannan kuma ya hada kai wajen yin aiki tare da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, to, kuwa da yardar Allah zai kai ga cimma nasarar kawo karshen rikicin Boko Haram din nan da karshen wannan shekarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya debar wa dakarun.
Wani babban kalubale da kasar nan ta ke fuskanta, shi ne, na faduwar tattalin arzikin kasa, tun daga lokacin da farashin danyen man fetur ya fadi kasa warwasa a kasuwar duniya daga farashin $115, a watan Yunin bara, zuwa $50, a yau kan kowace ganga. Ga kuma kudaden ajiyar rarar man fetur ba su wuce $2biliyan, yayin da na ajiyar kasashen waje ba su haura Dala biliyan 30 ba. A gefe daya kuma ana bin gwamnatin tarayya da jihohi bashin Dala biliyan 60, jihohi kuma suke ta rige-rigen karbar lamuni daga gwamnatin tarayya da sunan su biya albashi da basussukan `yan kwangila da kuma kashe wutar gabansu ko da kuwa ba mai muhimmanci ba ce.
Sannan ga koma bayan masu zuba hannun jari, musamman daga wajen kasar nan. Idan ka tattara wadannan matsaloli da na ambata da ma wadanda ban iya ambatawa ba, kai tsaya kasan kasar nan da al`ummarta suna cikin tsananin rashin kudin kashe wutar gabansu. Don haka akwai bukatar wanda duk ke shugabantar Ma`aikatar Kudi, ya kwan da sanin yadda zai dora cikin inganta hanyoyi shigowar kudi, tare da ririta wadanda suka shigo da toshe dukkan hanyoyin da suke zurarewa.
Misis Kemi Adeosun masaniya akan fannin tattalin arzikin kasa, kuma tsohuwar Kwamishiniyar Kudi a Jihar Ogun, ita aka ba jan ragamar wannan Ma`aikata ta Kudi, wadda Masana ke ganin tamfar karin maganar nan ce ta Bahaushe da ya ke cewa, ‘ko ba a fada ba, “Linzami ya fi karfin bakin kaza,” bisa ga karancin iliminta da rashin gogewarta, da kuma la`akari da wadda ta gada, wato Misis Dokta Ngozi Okonji Owella, shararriya ce kuma gogaggiya ce a duniya baki daya akan fannin tattalin arzikin kasa . Amma duk da haka Masanan suka ce da taimakon shugaban kasa da na wasu shugabannin ma`aikatun gwamnati da na hukumominsu, kai har ma da na masu zaman kansu, ita ma sabuwar Ministar Kudin za ta iya kai labari.
Wani fannin da yake matukar bukatar kulawa cikin hanzari shi ne, ayyukan Noma da Kiwo, ba wai don kasar nan tana da wadatar filin noma da yanayi mai kyau madatsun ruwa da ma albarkar mutanen da za su yi noman ko kiwon, a`a, sai don ittifakin da masana a wannan fanni da ma na tattalin arzikin kasa suka yi cewa, shi ne fanni daya tak da ke kai kowace kasa tudun mun tsira, saboda albarkatun da yake tattare dasu daban-daban.
Masanan sukan kara da cewa, fannin ayyukan noma da kiwon shi ne mafi a`a`la a cikin ci gaban kowace kasa, idan aka yi la`akari da cewa arzikin man fetur mai karewa ne, amma arzikin fannin ayyukan noma da kiwo, bayan kodayaushe yana nan, a kullum kuma dada bunkasa yake I bisa ga dabarun kimiya da fasaha da kullum ake kara zakulowa don bunkasar sa. A kan wannan fanni a wannan karon a kasar nan masanansa, suna ganin an yi sa`ar danka Mai`aikatar Ayyukan Gona da Albarkatun kasar nan ga shahararren masani, kuma kwararren fannin, wato Mista Audu Ogbeh, da kuma irin aniyar wannan gwamnatin na farfado da wannan fanni ta bayyana a fili yanzu a lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shugabanci kaddamar da shirin farfado da noman alkama da shinka a noman ranin bana a Jihar Kebbi, ranar Talatar nan da ta gabata. A wajen bikin Shugaba Buhari ya ce an zabi jihohi tara ciki har da jihar ta Kebbi, Babban Banki zai bayar da bashin Naira biliyan 20 ga manoman da za su shiga cikin shirin. Lokaci kawai ake jira wajen ganin ko shirye-shiryen wannan gwamnatin akan ayyukan gona za su zarta na gwamnatocin da suka rigayeta wajen samun nasara.
Wani ministan da za a zuba wa idanu, shi ne tsohon Gwamnan Jihar Legas, Mista Babatunde Fashola sabon Ministan Ayyuka da Gidaje da Wutar Lantarki, ma`akatar da kafin wannan lokaci ma`aikatu uku ne, wannan ya sa masana a wadannan fannoni suke ganin, tabbas din Mista Fashola zai iya ya sa Shugaba Buhari ya danka masa su, amma dai suna ganin taura ba ta taunuwa koda kuwa bakin kura ne. Amma ni ina tsammanin Shugaba Buhari zai rinka daukar ayyukan ma`aikatar ne daya-bayan-daya. Wata babbar Ma`aikata kuma da yanzu ita ake dogaro da kudin shigarta ita ce ta man fetur, wadda Shugaba Buhari ya tabbatar da ikirarin da ya yi ta yi, na cewa shi zai rike mukamin ministanta, amma yanzu don saukin samun gudanarwa ya nada Manajin Daraktan Rukunin Kamfanonin man fetur na kasa, Dokta Emmanuel Ibe Kachukwu, a zaman karamin Minista a Ma`aikatar.
Ko kusa ba cewa, nike ba sauran ma`aikatu ba su da muhimmanci ba, don haka ba za a zuba wa ministocinsu idanu ba, wajen ganin irin rawar da za su taka, a`a, sai don wadannan da na gabatar a sama su ne ginshikan tada komadar da kasar nan ta fada. Don haka su nike ganin ya kamata a zuba wa wadanda aka dankawa amanar gudanar da su idanu akalla nan da shekara daya zuwa biyu, wajen ganin ko sa kai mu ga tudun mun tsirar da muke bege.