Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama
Gwamnatin ƙasar ta shiga jimami tare da sauƙe tutarta zuwa ƙasa.
Wasu manyan jami’an gwamnati biyu a Ƙasar Ghana, sun rasu tare da wasu mutum shida a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a ranar Laraba.
Hatsarin ya faru ne a yankin Ashanti da ke Kudancin ƙasar.
- Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina
- Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato
Ministan Tsaro, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Mohammed, na cikin jirgin soja tare da wasu fasinjoji uku da ma’aikatan jirgin guda uku.
Jirgin ya tashi daga birnin Accra, babban birnin Ghana, zuwa garin Obuasi lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa.
Rundunar Sojin Ghana ta ce sun daina samun saƙo daga jirgin yayin da yake cikin tafiya.
Julius Debrah, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar, ya bayyana a cikin wani saƙon bidiyo cewa wannan hatsarin babban rashin ne ga ƙasar.
Ya kuma ce dukkanin tutocin ƙasar za a yi ƙasa da su har sai an bayar da sanarwa domin girmama wadanda suka rasu.
Sauran waɗanda suka rasu sun haɗa da Alhaji Mohammed Muniru Limuna (muƙaddashin mai kula da harkokin tsaron ƙasar), Samuel Sarpong (mataimakin shugaban jam’iyyar National Democratic Congress), da Samuel Aboagye (tsohon ɗan takarar majalisa).
Sunan ma’aikatan jirgin da suka mutu su ne Squadron Leader Peter Bafemi Anala, Flying Officer Malin Twum-Ampadu, da Sergeant Ernest Addo Mensah.