Ministocin Jonathan hudu sun ajiye aiki

Shugaba Goodluck Jonathan ya amince da murabus din ministocinsa hudu da suka hada da Ministar Sufurin Jiragen Sama Stella Oduah da na Harkokin ’Yan sanda, Caleb Olubolade da na Harkokin Neja-Delta Godsday Orubebe da kuma Minista a Ma’aikatar Kudi Yerima Lawan Ngama.A shekaranjiya Laraba ne Shugaba Jonathan ya amince da murabus din ministocin hudu, wadanda […]

Ministocin Jonathan hudu sun ajiye aiki

Shugaba Goodluck Jonathan ya amince da murabus din ministocinsa hudu da suka hada da Ministar Sufurin Jiragen Sama Stella Oduah da na Harkokin ’Yan sanda, Caleb Olubolade da na Harkokin Neja-Delta Godsday Orubebe da kuma Minista a Ma’aikatar Kudi Yerima Lawan Ngama.
A shekaranjiya Laraba ne Shugaba Jonathan ya amince da murabus din ministocin hudu, wadanda aka ce an bukaci su yi murabus ne domin su kauce wa tozarcin saukewa.
Babu wani dalili kana bin da ya sa aka nemi Olubolade da Orubebe Ngama su yi murabus. Amma ita Misis Oduah tana faman shan caccaka kan zargin ayyukan almundahana da suka dabaibaye ta.
Kwamitocin Majalisar Wakilai da na Shugaban kasa sun same ta da laifin tilasta wasu hukumomi da suke karkashinta da suka hada da Hukumar Sufurin Jiragen Sama (NCAA) kan su saya mata motoci masu sulke masu dan Karen tsada ba tare da amincewar doka kan haka ba.
Sannan kafar labarai ta Premium Times ta fita da wani bincike da ya gano ta yi karya kan takardun iliminta da ta mika ga Majalisar Dattawa lokacin zama bahasin tabbatar mata da mukaminta. Binciken ya nuna ta yi da’awar wata jami’a da babu ita ta ba ta digirin dokta na girmamawa.