Ministocin Tinubu: Babu Kano, Adamawa, Lagos
Jihohi 11 da suka haɗa da Kano, Adamawa da Lagos ba su samu wakilci ba a jerin sunayen ministocin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aikewa Majalisar Dattawa domin tantancewa. Sashe na 147(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya ce “wajibi ne shugaban ƙasa ya naɗa aƙalla minista ɗaya daga kowacce jiha.” Sai […]
Jihohi 11 da suka haɗa da Kano, Adamawa da Lagos ba su samu wakilci ba a jerin sunayen ministocin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aikewa Majalisar Dattawa domin tantancewa.
Sashe na 147(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya ce “wajibi ne shugaban ƙasa ya naɗa aƙalla minista ɗaya daga kowacce jiha.”
Sai dai ƙididdigar Aminiya ta nuna cewa babu sunayen ministoci daga jihohi 11.
Ministocin Tinubu: El-Rufai, Wike, Badaru sun samu shiga
Ministocin Tinubu: Ta leƙo ta koma
Jihohin su ne Adamawa, Bayelsa, Gombe, Kano, Kebbi, Kogi, Plateau, Lagos, Osun, Yobe, da Zamfara.
Amma jihohin Katsina, Bauchi da Cross River sun samu ministoci biyu-biyu a cikin 28 ɗin da aka sanar.
A ranar Alhamis ne shugaba Tinubu ya aike da sunayen zuwa ga Majalisar Dattawa, ana jajiberin cikar wa’adin kwanaki 60 da doka ta tanada.
Don haka ana sa ran daga baya zai tura kashi na biyu na sunayen domin tabbatar da cewa kowacce jiha ta samu aƙalla minista guda.