Ministocin Tinubu: El-Rufai, Wike, Badaru sun samu shiga

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kaduna, Rivers da Jigawa sun samu shiga cikin jerin sunayen  da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa domin tantancewa a matsayin ministoci. A ranar Alhamis shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana sunaye 28 da suka fito a kashin farko na mutanen da za a tantance domin naɗa […]

Ministocin Tinubu: El-Rufai, Wike, Badaru sun samu shiga

Tsofaffin gwamnonin jihohin Kaduna, Rivers da Jigawa sun samu shiga cikin jerin sunayen  da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa domin tantancewa a matsayin ministoci.

A ranar Alhamis shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana sunaye 28 da suka fito a kashin farko na mutanen da za a tantance domin naɗa su muƙamin minista.

Sunayen sun haɗa da Nasiru El-Rufa’i, Nyesom Wike, Badaru Abubakar, Ahmed Ɗangiwa, Hannatu Musawa, Uche Nnaji, Betta Edu da Doris Aniche Uzoka.

Akwai kuma David Umahi, Ekperipe Ekpo, Nkiru Onyeojiocha, Olubunmi Tunji Ojo, Stella Okotette, Uju Kennedy Ohanenye, da Bello Muhammad.

Sai kuma Dele Alake, Lateef Fagbemi, Muhammad Idris, Olawale Edun, Waheeb Adabayo Adelabu, Iman Suleiman Ibrahim, Ali Pate, Joseph, Abubakyar Kyari, John Eno, da Sani Abubakar Ɗanladi.

 

 

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume