Ministocin Tinubu: Ta leƙo ta koma

Majalisar Dattawa ta kammala zamanta na wannan makon ba tare da bayyana sunan mutanen da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke neman naɗawa a matsayin ministoci ba. Hakan ya zama tamkar ba-zata ga al’ummar Najeriya bayan da rahotanni ke cewa tun ranar Talata shugaban ƙasa ya aikewa da Majalisa sunayen. A ranar  Laraba ne dai aka […]

Ministocin Tinubu: Ta leƙo ta koma

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Majalisar Dattawa ta kammala zamanta na wannan makon ba tare da bayyana sunan mutanen da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke neman naɗawa a matsayin ministoci ba.

Hakan ya zama tamkar ba-zata ga al’ummar Najeriya bayan da rahotanni ke cewa tun ranar Talata shugaban ƙasa ya aikewa da Majalisa sunayen.

A ranar  Laraba ne dai aka  sa rai shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio zai sanar da sunayen amma aka ji shiru.

Zaɓin Ganduje lalata tsarin APC ne – Salihu Lukman

Ganduje zai zama shugaban APC na ƙasa

Makomar Ganduje

Sai dai manazarta sun dangantaka jinkirin bayyana sunayen da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Rahotanni sun ce Dr Ganduje na cikin ƙunshin sunayen da shugaba Tinubu ke neman naɗawa minista.

Amma a ranar Larabar ya janye sunansa tare da yi masa tayin shugabancin jami’yyar APC na ƙasa bayan da tsohon shugaban Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus.

Don haka ranar Alhamis da Majalisar Dattawa ta zauna sai kowa ya buɗe kunne ya na jiran ya ji sunayen ministoci.

Amma da misalin  11:59am sai Sanatocin suka shiga zaman sirri inda suka fito da 1:41pm.

Duk masu bibiyar Majalisar sun yi zaton an shiga tattaunawa ne kan ƙunshin ministocin.

Tsaron Majalisa

Amma bayan fitowarsu sai shugaban majalisa Santa Akpabio ya bayyana cewa sun tattauna ne game da samar da tsaro a harabar Majalisar.

Har ma ya ce an kafa kwamitin wucin-gadi a kan hakan ƙarƙashin Sanata Ɗanjuma Goje.

Haka kuma Santa Victor Umeh mai wakiltar  Anambra ta Tsakiya ya shaidawa manema labarai cewa sam ba su yi maganar ministoci a tattaunawarsu ba.

Ya ma ce a iya saninsa shugaban ƙasa bai aike da sunayen ministoci zuwa ga Majalisar Dattawa ba.

Kamar yadda ta saba dai Majalisar ba za ta sake zama ba sai ranar Talata.

Wa’adin Tsarin Mulki

Wannan na nufin shugaba Tinubu na neman ƙure wa’adin da tsarin mulki ya tanadar masa na miƙa sunayen ga Majalisar Dattawa.

Tsarin Mulkin Najeriya ya tilastawa shugaban ƙasa ya miƙawa Majalisa sunayen ministoci cikin kwanaki 60 da hawa  kujerar mulki.

Shugaba Tinubu da aka rantsar da shi ranar Mayu 29, 2023 na da nan da zuwa Alhamis Yuli 27, 2023 ya miƙa sunayen ko ya ci karo da tsarin mulkin ƙasa.

 

 

 

 

 

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume