Misbahu Ahmad zai yi karar tashar Africa Magic
Fitaccen mawakin fina-finan Hausa kuma daya daga cikin masu shirya fina-finan Hausa Misbahu M. Ahmad ya yi barazanar kai karar tashar talabijin din Africa Magic bangaren Hausa sakamakon haska fina-finansa ba tare da izininsa ba.Misbahu wanda shi ne shugaban Kamfanin Usmaniyya Production ya bayyana cewa an dauki tsawon shekaru uku ke nan tashar na haska […]

Fitaccen mawakin fina-finan Hausa kuma daya daga cikin masu shirya fina-finan Hausa Misbahu M. Ahmad ya yi barazanar kai karar tashar talabijin din Africa Magic bangaren Hausa sakamakon haska fina-finansa ba tare da izininsa ba.
Misbahu wanda shi ne shugaban Kamfanin Usmaniyya Production ya bayyana cewa an dauki tsawon shekaru uku ke nan tashar na haska fina-finansa wadanda suka hada da ‘Kansakali’ na daya da na biyu da ‘Kakaki’ na daya da na biyu da kuma ‘Basaja’ ba tare da izininsa ba.
Ya ce: “An dade ana gaya mini cewa tashar Africa Magic na haska fina-finaina, hakan ya ja hankalina na rika bin shirye-shiryensu har na ga sun nuna fina-finan nawa. Abin ya ba ni mamaki kwarai da gaske ganin cewa babu wanda ya nemi iznina a matsayina na mamallakin wadannan finafinai.”
Mawakin ya yi wa Aminiya karin haske da cewa duk da cewa a shekarar 2009 zuwa 2010 wani mutum ya karbi izini daga gare shi don samun damar haska fim din ‘Kansakali’ a Africa Magic.
“A shekarar 2009 zuwa 2010 akwai wani mutum da ya zo ya nemi iznina na cewa zai kai fim dina na ‘Kansakali’ tashar Africa Magic. A nan na amince. Sai dai tun daga wancan lokaci mutumin bai zo ya shaida min yadda suka yi ba. Haka na hakura da tunanin cewa abin zai tsaya zuwa shekarar 2010. Amma sai ga shi har yanzu ba su daina haskawa ba. Hakan ya sa na nemi wancan mutumin amma ya tabbatar mini cewa ko a shekarar 2010 din ma bai kai fim din nawa ba, don haka bai san da wannan magana kwata-kwata ba” Inji shi.
Ya kara da cewa a yanzu haka kamfaninsa da lauyoyinsa sun shirya tsaf don gurfanar da tashar Africa Magic gaban kuliya, don a cewarsa ba zai yiwu kura da shan bugu gardi da kwashe kudi ba.
A karshe Misbahu ya yi kira ga sauran masu sana’a irin tasa da su sa ido sosai a kan wannan gidan talabijin domin tabbatarwa ba a yi musu sojan gona ba. “Yana da kyau sauran masu sana’a irin tawa su sanya idanu a kan irin shirye-shiryen da tashar Africa Magic da makamanta suke gudanarwa don ganin ba a yi mana sojan gona ba da kuma don kare hakkin mallaka” Inji shi.