Misis Eglah Sulaiman kasim: Burina in kasance gatan marasa gata
Misis Eglah Sulaiman D. kasim, Ta rike mukamin Babbar Sakatariya da kuma Kwamishina a Hukumar Kula da Tsara Dokokin Majalisar Jihar Gombe, ta jajirce wajen taimakon al’umma, inda a yanzu ta shiga siyasa gadan-gadan, ta ce burinta ta zama gatan marasa gata. Tarihin Rayuwata Sunana Misis Eglah Sulaiman D. kasim, an haife ni a garin […]
Misis Eglah Sulaiman D. kasim, Ta rike mukamin Babbar Sakatariya da kuma Kwamishina a Hukumar Kula da Tsara Dokokin Majalisar Jihar Gombe, ta jajirce wajen taimakon al’umma, inda a yanzu ta shiga siyasa gadan-gadan, ta ce burinta ta zama gatan marasa gata.
Tarihin Rayuwata
Sunana Misis Eglah Sulaiman D. kasim, an haife ni a garin Kalarin da ke yankin karamar Hukumar Kaltungo a Jihar Gombe a ranar 25 ga Disamba, 1953. A garin Kalarin na yi wayo har aka sa ni a makarantar firamare ta Kalarin, bayan na kammala sai aka kai ni sakandare a garin Ilorin da ke Jihar Kwara. Bayan na kammala sakandare ne na fara aiki a matsayin jami’ar walwala (Social Worker) a Maiduguri, ina kan aiki ne na koma karatu a Kaduna, wato na yi Difloma a kwas din Social Administration. Daga nan na yi digiri a kwas din Sociology a Jami’ar Jos, sannan na yi hidimar kasa ta a nan garin Jos din, wanda hakan ya ba ni kwarin gwiwa wajen ci gaba da aikina, kuma ina da aure na yi karatuna tare da tallafin maigidana Marigayi Sulaiman D. kasim.
Aiki
Bayan na kammala sakandare sai na fara aiki a matsayin jami’ar walwala a shekarar 1973 a garin Maiduguri a yankin Arewa maso Gabas a sashin kula da walwalar al’umma, har zuwa shekara ta 1978, inda aka mayar da ni Jihar Bauchi a shekarar 1979, wato na zama shugabar sashin a jihar. Ina nan ina aiki sai na samu karin girma zuwa babbar jami’ar sashin a shekarar 1982 ke nan. A shekarar 1988 na sake samun karin girma zuwa babbar shugaba (Principal Social welfare officer), inda a 1989 kuma na zama mataimakiyar babbar shugaba (Assistance Chief Social Welfare). A shekarar 1995 aka ba ni mukamin mataimakiyar darakta mai kula da sashin yara a Jihar Bauchi, bayan an kirkiro Jihar Gombe a shekarar 1996 sai na dawo gida, inda aka nada ni mukaddashiyar darakta mai kula da al’amuran yara a ma’aikatar mata, a shekarar 2000 kuma na zama daraktar jin dadin yara da walwalarsu ta wannan ma’aikata (Director Child), bayan shekara uku wato a 2003 ke nan aka nada ni babbar sakatariya (Permanent Secretary) a ma’aikatar mata da walwalarsu.
A shekarar 2004 sai aka mayar da ni babbar sakatariya kuma sakatariya a hukumar kula da malamai ta Jihar Gombe, inda daga shekarar 2007 zuwa 2008 aka mayar da ni Ma’aikatar Matasa har zuwa shekara ta 2010. A shekarar 2011 na zama Kwamishinar dindindin a hukumar kula da tsara dokoki ta majalisar jiha, wato (Permanent Commissioner 1 House of Assembly Serbice Commission), a shekarar 2012 kuma na zama mamba a wani kwamiti na farfado da da’ar matasa da samar musu aikin yi a 2012, na kuma zama shugabar wani kwamiti na mata da kananan yara a Jihar Gombe, a shekara ta 2013 na zama babbar Kwamishina ta dindindin ta 1 a hukumar kula da tsara dokokin majalisar jihar, inda na ajiye aiki na shiga siyasa gadan-gadan, yanzu nake takarar Sanata.
kalubale
Na fuskanci kalubale sosai musamman ma duk wani abu da ya hada da maza, amma da yake na tsaya ina gudanar da aikina yadda ya kamata, sai na ga kalubalen bai zama kalubale ba, domin hakan ya sa na yi ta samun ci gaba a wajen aiki har na zama babbar sakatariya, wanda burin kowane ma’aikacin gwamnati ya zama babban sakatare, kuma a lokacin da nake babbar sakatariyar ni kadai ce mace a Jihar Gombe duk sauran maza ne.
Nasarori
Na samu nasara sosai a wajen aiki, sai dai in fadi kadan, domin a wannan aiki na kula da jin dadi da walwalar mutane na sasanta jama’a sosai a bangarori da dama, inda hakan ya sa aka dinga ba ni lambobin yabo.
Lambar yabo
Na samu lambobin yabo kamar yadda na gaya maka a bangarori daban-daban, inda a shekarar 2004 aka ba ni lambar yabo ta shaidar zaman lafiya daga wata hukuma ta sadarwa, har ila yau a wannan shekarar aka sake ba ni lambar yabo ta iya shugabanci daga wata tsangaya ta kwararrun ma’aikata, na kuma sake samun yabo a shekarar na iya tafiyar da shugabanci a aikin gwamnati daga Cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Turawan Birtaniya, sannan a shekara ta 2005 wasu al’umma suka karrama ni da lambar yabo ta Fitacciyar Mace a Jihar Gombe, inda a shekarar 2009 kungiyar ci gaban yankin al’ummar karamar Hukumar Kaltungo ta kasa reshen Jihar Gombe suka karrama ni, daga nan Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa FRSC suka ba ni lambar yabo ta taimakawa wajen ciyar da al’umma gaba.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Na fi son a dinga tuna ni a matsayin mace mai kishi da taimaka wa al’umma, domin haka ne ya sa har na samu lambobin yabo masu yawa.
Tufafi
A matsayina ta ’ya mace mai kamala, ba ni da tufafi da na fi sha’awa, illa wanda zai rufe mini jiki, ya ba ni daraja, ba kamar yadda wasu suke sanya tufafin da yake nuna tsiraici, ka ga jikinsu a waje ba.
Siyasa
Abubuwan da suka sanya na shiga siyasa har na fito takara su ne, saboda siyasa hanya ce mai sauki da zan fi iya taimaka wa al’ummata, kuma na shiga siyasar ne domin bayar da gudumawata, zan hada kai da kowa-da-kowa wajen ganin na ba da shawarwarin da suka dace, don kara ba shi gwamna Ibrahim Hassan dankwambo damar ci gaba da samar da abubuwan more rayuwa, kuma idan na zama Sanata zan kawo canji mai ma’ana, wanda zai sa a gane mulkin mata ya fita daban da na maza in Allah Ya yarda.
kungiyoyi
Ni mamba ce a kungiyar wanzar da zaman lafiya ta Molmole, sannan mamba a kungiyar ma’aikatan jin dadin ma’aikata, kuma mamba a kungiyar ci gaban Tangale Waja, sannan ina cikin kungiyar mata ’yan siyasa.
kasashen da taba zuwa
Na je kasashe irin su Masar da Afirka ta Kudu da Ingila da sauransu.
Iyali
Ina da ’ya’ya uku maza, akwai kuma ’ya’yan maigidana da ’yan uwa da yawa wadanda suke karkashin kulawata, kuma duk sun kammala jami’a, wadansu sun yi hidimar kasa.
Shawara ga iyaye
Iyaye ku sa ’ya’ya mata a makaranta don su samu ilimi, saboda karatu abu ne mai kyau. Muddin mace ta yi karatu gida zai zauna lafiya, kuma ’ya’ya za su tashi cikin tarbiyya da sanin ya kamata, inda ko aurar da yarinya aka yi sai ta bambanta da wacce ba ta yi karatu ba, kuma idan mace ta yi ilimin zamani za ta tallafa wa maigidanta da kuma iyayenta, sannan idan aka yi ilimi ko matsala ta faru a tsakanin iyali, wannan ilimin zai sa a samu gyara ba tare da wani ma ya ji ba, sannan ina kira ga iyaye su daina dora wa ’ya’ya mata talla, ba abu ne mai kyau ba, tana bata tarbiyyar yara da sa wasu su shiga halin tasku.