Misis Finney Dabid: Mata a yi ilimi don a dogara da kai

Misis Finney Dabid, ba ta taba yin aikin gwamnati ba amma ta yi gwagwarmayar rayuwar da ya kai ta ga tsayawa da kafafunta har ta kafa kamfanin sarrafa waken suya Finney. ’Yar asalin karamar hukumar Balanga a jihar Gombe ta yi fice a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya har ta yi kokarin ganin ta zama […]

Misis Finney Dabid: Mata a yi ilimi don a dogara da kai
Misis Finney Dabid: Mata a yi ilimi don a dogara da kai

Misis Finney Dabid, ba ta taba yin aikin gwamnati ba amma ta yi gwagwarmayar rayuwar da ya kai ta ga tsayawa da kafafunta har ta kafa kamfanin sarrafa waken suya Finney. ’Yar asalin karamar hukumar Balanga a jihar Gombe ta yi fice a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya har ta yi kokarin ganin ta zama zababbiyar ’yar majalisar wakilai ta tarayya da za ta wakilici yankin Billiri da Balanga a zaben da ya gabata a jam’iyyar APC amma aka samu akasi.

Tarihin rayuwata
Sunana Finney Dabid, ni Bachamiya ce kuma Balungudiya, domin mahaifina dan kabilar Cham ne mahaifiyata kuma Balungudiya ce, duka a karamar hukumar Balanga a jihar Gombe, amma ni an haife ni ne a garin Kaltungo a shekarar 1976.
Na yi kuruciyata har na kai lokacin shiga makaranta a garin Nyuwar da ke yankin karamar hukumar Balanga sannan iyayena suka saka ni a makarantar firamare ta Central da ke Nyuwar, bayan na gama sai na tafi makarantar sakandaren ’yan mata ta WTC da ke Kaltungo na yi aji daya na fita na koma karamar sakandaren al’umma ta Nyuwar na karasa shekara biyu, daga nan sai na tafi babbar sakandaren ’yan mata ta GGSS Tafawa Balewa da ke Bauchi na gama a shekarar 1991, ina gamawa sai na wuce Kwalejin fasaha da kere-kere ta gwamnatin tarayya Federal Polytechnic Bauchi a tsakanin shekarar 1993 zuwa 1995 inda na samu takardar shaidar karatu ta Difloma a bangaren harkar kasuwanci (Business administration).
Ina nan ina gwagwarmayar rayuwa a shekara ta 2004 na sake tafiya jami’ar Jos na samu takardar shaidar digiri na farko a bangaren wasan kwaikwaiyo ,na kammala a shekarar 2008.
Aiki
Ban taba yin aikin gwamnati ba sai dai bayan na gama karatuna na fara gudanar da al’amuran kasuwanci ne a shekara ta 2000 zuwa ta 2003 bayan nan sai na kafa wata kungiya wacce ba ta gwamnati ba mai suna Adbancement for women and Youth Initiatibes (JOWYO ) na fara tafiyar da wannan kungiya daga shekarar 2008 zuwa 2013. Na bude wani kamfani nawa mai suna Scale up farms Limited a nan Gombe da muke noma waken suya da sarrafa shi zuwa man girki sannan kuma dusar muke yin abincin kaji da ita.
A wannan kamfani muna da ma’aikata na dindindin guda goma sha takwas sannan akwai wadanda ba na dindindin ba guda goma sha biyar da su kuma a kullum ake biyansu idan an yi aiki.
A cibiyar mun yi hadin gwiwa da Bankin duniya da UNICEF da UNFPA da Sabe the Children da MSH da UNDP da Abuntu for Debelopment wata kungiya ce dake kasar Afirka ta kudu don gudanar da ayyuka daban daban wa al’umma musammam ma a yankunan karkara sannan kuma akwai wata kungiya mai suna Unities ta turawa ce ita ma wanda su kuma aiki suka sa nake yi musu a bangaren na’ura mai kwakwalwa IT akan harkar sadarwa a jihohi 19 na Arewacin Najeriya.
kalubale
A gaskiya na samu kalubale sosai duk da ma aikin dana dinga yi din ba aikin gwamnati ba ne aiki ne da kungiyoyi na Turawa wanda idan za a gudanar da wani aiki, kafin na shawo kan jama’a su yarda su amince da abin da aka kawo musu sai na yi da gaske.
Kuma da yake harkokin na Turawa ne kafin gwamnati ita ma ta amince a yi hadin gwiwa da ita a gudanar da wasu aiyukan suna ba mu wahala.
Kasancewar a wasu lokutan mukan samu gwamnati tana gudanar da nata ayyukan.Wani abu kuma shi ne ganin cewa ni mace ce ,zuwa na da irin wannan kungiya,kafin a amince da hakan yakan kara zama da matsala.
Nasara
Na samu nasara ba ’yar kadan ba domin na iya shawo kan mata da dama sun rungumi wasu daga cikin aikace-aikacen da muka bullo da su.
Kuma da ma burin Turawan shi ne mata su ci moriyar shirin.
Sannan ni kaina na samu karin ilimi da wayewar kai inda na cimma wasu burina a rayuwa da kuma kara sanin yadda ake mu’amala da mutane iri-iri.
Abin da ya ba ni sha’awar shiga siyasa
Aiyukan da na yi da kungiyoyin nan na Turawa da nawa wadanda ba na gwamnati ba su ne suka kara min kwarin gwiwar shiga siyasa bisa ga yadda na ga an bar mata a baya sosai .
Saboda haka na ce bari in shiga siyasa gadan-gadan don kwato musu ‘yanci.
Sannan kuma su samu wakilci nagari daga mace ‘yar uwarsu domin babu namijin da ya san damuwar mace sai mace ’yar uwarta.Kuma har yanzu mu mata ba mu samu wakilci na kashi 35 cikin dari da muke nema ba daga wajen gwamnati, na tsaya takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya ne daga yankin Billiri da Balanga amma maza suka nuna min halinsu.
Burina a rayuwa
Babban burina shi ne ina so in ga mata sun samu wakilci sosai kuma ya zamana ana damawa da su a duk wani bangaren gwamnatin jihohi da na tarayya tun da ba abar mu mun yi takara sosai ba ko za mu cike wannan gurbi na kashi 35 da muke nema da mukaman siyasa.

kungoyiyi da kasashe
Ina cikin kungiyoyi masu yawa amma wasu daga cikin su ne ina zaman mai binciken kudi na kungiyar Coalition of cibil society Organisation of Nigeria.
Sannan kuma Sakatariyar kudi da mai bincike a Nynetha Network of Youth Organisation against Hib/ aids.Har yanzu ni ce mai binciken kudi ta Cis hand , sannan jagora kuma wacce ta kafa kungiyar hadin kan matan tangale waja da ake kira Tawada, a fadin kasar nan kuma ni ce mai kula da shiyar Arewa maso Gabas na NAPED/ CRUDAN mai rajin ganin an samu karuwar shigar mata harkar siyasa a Najeriya.
kasashen da na ziyarta
Na je kasar Ingila ne kawai na samu biza ta zuwa Chaina har yanzu ban tafi ba saboda wasu aikace-aikace da suke gabana.
Mukaman siyasa da na rike
Da hawan gwamna Ibrahim Hassan dankwambo, ya nada ni a matsayin mamba a wani kwamiti da za mu tabbatar da ayyukan ma’akatun gwamnati inda aka sani a kwamitin mata da kananan yara cikin kwamitocin goma sha biyu da ya kafa a shekara ta 2012. Sannan ni board mamba ce a hukumar ba da tallafin guraben karo karatun dalibai (Scholarship).
Shawara ga iyaye
Ina mai bai wa iyaye shawara kan yadda ilimi yake da muhimmanci ga rayuwar ‘ya mace don haka nake kira da babbar murya da cewa iyaye ku yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin kun ilimantar da ‘ya’ya mata saboda ilimin ‘ya mace abin alfahari ne gare ta da kuma iyayenta saboda idan mace ta samu ilimi za ta iya dogara da kanta ta hanyoyi daban-daban a rayuwa sannan ni a matsayina na ’ya mace ba na goyon bayan iyaye wajen dora wa ‘ya’yansu talla saboda ta nan suke fara lalacewa saboda haka iyaye a yi hattara a kiyaye.