Misis Hannatu D. Ayagas: Mata a shiga siyasa a yi dama-dama
Misis Hannatu Daniel Agyas ‘yar siyasa ce. daya ce kuma daga cikin wadanda suka kirkiro jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa da a yanzu ta fito takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar a inuwar Jam’iyyar PDM daga APC. Za ta wakilci mazabar Obi ta 2 a Majalisar Dokokin a wannan shekarar da ake ciki 2015. Tarihin rayuwataSunana […]
Misis Hannatu Daniel Agyas ‘yar siyasa ce. daya ce kuma daga cikin wadanda suka kirkiro jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa da a yanzu ta fito takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar a inuwar Jam’iyyar PDM daga APC. Za ta wakilci mazabar Obi ta 2 a Majalisar Dokokin a wannan shekarar da ake ciki 2015.
Tarihin rayuwata
Sunana Misis Hannatu Daniel Agyas. An haifi ni a shekarar 1967 a Unguwar Doko da ke nan Lafiya jihar Nasarawa. Na yi makarantar firamare a ‘St. James’ da ke nan Lafiya. Daga baya na koma makarantar firamare ta’St. Williams’ ita ma a nan garin Lafiya inda na kammala. Daga nan na shiga makarantar sakandare da ke Musha a yankin Rayawa na Jangwe a jihar nan, inda na kammala a sakandaren gwamnati da ke garin Obi.
Zan iya tunawa a lokacin da nake makarantar sakandare na sha wahala sosai domin da kaina nake biyan kudin makarantata. Don a lokacin mahaifina ya yi hatsari ya samu mummunar karaya, sannan ita kuma mahaifiyata ta rasu sakamakon wannan hatsarin da ya rutsa da su a nan take. Saboda haka na yi tallace-tallacen lemo da masara da sauransu. Da haka dai har Allah cikin tausayinsa ya taimaka mini na kammala karatun sakandare dina. Bayan na kammala na ci gaba da tallace-tallace a kofar gidanmu na wasu lokuta kafin daga baya na samu aiki da ‘Lower Benuwai Riber Basin’ inda ake biyana naira 180 a matsayin albashi. Koda yake wannan kudi kalilan ne. Amma a gurina a lokacin tamkar miliyan ne. Da wannan kudi ne na fara daukar nauyin kannena ,domin a lokacin kamar yadda na bayyana maka a baya mahaifina ba ya aiki sakamakon hatsari da ya yi. Kuma kamar yadda ka sani shi aikin ‘yan sanda ba kamar sauran aiyuka ba ne, da zarar ka samu wata matsala irin wannan to, ba kai ba aiki. Daga nan sai na samu damar tafiya wani karatu da ake kira Clerical Course a Turance a jihar Legas. Bayan na kammala sai na sake yin wani karatu da ake kira ‘Edecutibe Clerical Course’, duka dai sun shafi aikina ne. Da na kammala ne sai na sami aiki a makarantar kimiya da fasaha da ke jihar Filato. Daga nan sai wata kawata ‘yar siyasa da ake kira Madam Tariza Wuya ta shawarce ni cewa in koma makaranta in ci gaba da karatu ta kuma yi alkawari cewa za ta taimaka mini a fannin karatun. Bayan na je na yi karatun difuloma dina a fannin kasuwanci wato (Business Administration), na kammala sai na ci gaba da aikina a wannan makarantar kimiyya da fasaha inda daga baya aka daukaka matsayina zuwa mai biyan albashi a wannan makaranta.
Daga nan na sake komawa makaranta na karanci fannin lissafi, bayan shekaru 2 na samu babbar difuloma a jami’ar Abuja. Ina kammalawa sai na yi aure a wannan shekara. Ka ji kadan daga cikin tarihin rayuwata ke nan.
Abubuwan da na koya a gurin iyayena
Iyayena sun koya mini abubuwa masu muhimmanci a rayuwa sosai a lokacin da nake tasowa. Musamman shi mahaifina ban gaya maka ba kafin ya shiga aikin dan sanda ya taba siyasa. Kuma ya samu nasara sosai a harkar. Mutum ne mai son jama’a kuma ba ya nuna kabilanci ko addini. A koda yaushe za ka gan shi cikin jama’a kowa nasa ne. Saboda haka sai ya koya mini zama da jama’a ba tare da na samu matsala da su ba. shi ya ba ni sha’awar shiga siyasa. Don harkar siyasa da nake yi yau zan iya cewa na gaje shi ne ,domin sanannen dan siyasa ne a lokacin. Haka ita ma mahaifiyata Allah ya jikanta ta koya mini kyawawan halaye kafin ta koma ga Allah. Saboda haka a gaskiya alhamdullillahi na samu kyakkyawar tarbiya a lokacin da nake tare da su.
Abin da ya ba ni sha’awar shiga siyasa
Ni dai kamar yadda na bayyana maka a baya na koyi harkar siyasa a gurin mahaifina ne. Don kamar yadda na bayyana cikakken dan siyasa ne a da. Zan iya tunawa har ila yau a lokacin da yake siyasa akan ba shi babura da sauransu ya rarraba wa jama’a wato a lokacin NPN ke nan. Gwamna Umaru Tanko Al-makura mai ci yanzu a jihar nan shi ne sakataren jam’iyyar a lokacin. Abin da ya burge ni a siyasar mahaifina shi ne a duk lokacin da yake rarraba wadannan babura ga magoya bayan jam’iyyar, idan wasu suka ce masa ya dauki babur daya daga cikin baburan sai ya ki. Sai ya ce ai an ce ya bai wa jama’a ne, ba ya dauki nasa ba. Wadannan ire-iren kyawawan halaye nasa ne musamman na nuna gaskiya da rikon amana musamman a harkar siyasa da ya yi ne suka ba ni sha’awa ni ma na shiga siyasa.
Na biyu kuma abin da ya ba ni sha’awar shiga siyasa shi ne don in canza rayuwar al’ummata musamman mata in samar musu da ribar dimokuradiyya don su san ana yi da su a gwamnati. Na fara ne da jam’iyyar PDP sannan ina so in yi amfani da wannan damar in bayyana maka cewa ina daya daga cikin ’ya’yan jihar nan wadanda suka kirkiro jam’iyyar PDP a jihar nan. Amma da yake daga baya na gano cewa babu gaskiya da rikon amana a jam’iyyar musamman a wannan lokaci da muke ciki, sai ban yi wata-wata ba na canza sheka zuwa jam’iyyar APC inda kuma na fito takarar kujerar majalisar dokokin jihar nan don wakiltar mazabata wato mazabar Obi ta 2 a majalisar dokokin wannan shekarar da muke ciki. Koda yake ban yi nasara a zaben fid da gwani da APC ta gudanar ba. Amma kasancewa ina da kyakkyawar manufa ga al’ummata shi ya sa na ki karaya na canza sheka zuwa jam’iyyar PDM wato wadda aka fi sani da’ mai toci’inda na sake tsayawa takarar kujerar. Kuma da yardar Allah zan samu nasara. Kuma idan Allah ya ba ni nasara zan tabbatar na kawo ci gaba mai dorewa mai kuma ma’ana musamman a yankina in kuma gudanar da shugabanci na gari.
Nasarori
Ni dai nasarorin da na cimma a rayuwata galibinsu a fannin siyasa ne. Don kamar yadda na bayyana maka a baya ina daya daga cikin masu fada-a -ji ’yan jam’iyyar PDP da suka kirkiro da jam’iyyar a jihar nan. Kuma da yardar Allah a yau idan za a ambaci sunayen mata ’yan siyasa a jihar nan da suka taka mahimmiyar rawa a rayuwar musamman ’yan uwansu mata, to ya zama dole a ambaci sunana. Kai ba ma a jihar nan kawai ba har da kasar nan baki daya. Muna taimaka wa al’umma dai- dai gwargwado. Don idan ka bincika a duk jam’iyyar da na ke ina aiki ne sosai tsakanina da Allah wajen bauta mata. Nakan yi duk abin da zan iya wajen tabbatar na kawo wa jam’iyyar ci gaba masu ma’ana, a kowane fanni musamman ganin an samu hadin kan matan jam’iyyar.
Haka suma al’ummata nakan fafata in tabbatar cewa suma ana yi da su wato suma suna samun ribar dimokuradiyya ta hanyar bi musu hakkinsu yadda ya dace. Kuma a kullum suna yaba mini su kuma saka mini da fatan alheri don haka, ba yabon kai ko maganar ra’ayi nake yi ba, gaskiyar lamarin ke nan. Saboda haka a takaice dai na samu nasarori da dama a rayuwata musamman a bangaren siyasa.
Shawarata ga mata
Ina so in yi amfani da wannan damar a takaice in shawarci mata ’yan uwana da cewa su tashi su nemi ilimin addini da na zamani domin su ne gishirin zaman duniya. Mata a shiga siyasa a yi dama- dama don ta wannan hanya ce kawai za mu iya kwato ’yancinmu da na ’ya’yanmu. Mata mu kula da tarbiyar ’ya’yanmu sosai don wannan shi ne babban gado da za mu bar musu. Mata mu ci gaba da kare mutuncin aurenmu musamman yin ladabi da biyayya ga mazajenmu a koda yaushe don wannan hakki ne da Allah ya rataya a wuyanmu. A karshe mata kada mu kaurace wa umurnin Allah a kanmu maimakon haka mu yi iya kokarinmu mu cika su a koda yaushe.
Na gode.