Misis Hannatu George Ardo: Ya dace mata mu dogara ga Allah
Tarihin rayuwata An haifi ni a karamar hukumar Kagarko da ke Jihar Kaduna.Na yi karatun firamare a makarantar “St Augustine” a Kaduna ,na yi karatun sakandare a makarantar “S.I.M”, daga nan kuma na wuce kwalejin kimiyya da fasaha da ke Zariya.Sai kuma na tafi Jami’ar Bayero da ke Kano,inda na karanci Kimiyyar Siyasa.Na yi aikin […]
Tarihin rayuwata
An haifi ni a karamar hukumar Kagarko da ke Jihar Kaduna.Na yi karatun firamare a makarantar “St Augustine” a Kaduna ,na yi karatun sakandare a makarantar “S.I.M”, daga nan kuma na wuce kwalejin kimiyya da fasaha da ke Zariya.Sai kuma na tafi Jami’ar Bayero da ke Kano,inda na karanci Kimiyyar Siyasa.
Na yi aikin gwamanati a wurare daban –daban ,kuma ni mata ce ga marigayi George Ardo,muna da ’ya’ya biyu.
Na yi digiri na biyu a kan aikin Jarida kuma ina da difiloma a bangaren Hulda da Jama’a wanda na yi karatun a makarantar Hulda da Jama’a da ke birnin Landan.
A yanzu ni ce mataimakiyayar Ganaral Manaja na Aiyuka na Musamman na Hukumar Inshorar lafiya a Abuja.
Abubuwan da ba zan manta da su ba
Akwai su da yawa,mu goma ne kuma mun taso a gida mai raha sosai saboda mahaifinmu ya kasance mai son nishadi, yana da mutane,mun tashi mun gan shi yana siyasa.Siyasar wancan lokacin ta kasance mai karfi da ban sha’awa ,ina nufin lokacin Sardauna,gidanmu ya kasance tamkar gidan baki,ba ma zama mu kadai ,muna da ’yan’uwa da abokan arziki da suke kawo mana ziyara ko da yaushe.
Na tashi da sanin cewa ko da yaushe mutane za su iya kasancewa tare da mu,kuma na kasance yarinya mai annashuwa kasancewar akwai nishadi matuka a gidanmu,kuma yaran gidanmu duk mun shaku da juna.Lokacin da na yi aure mijina ya sami matsala saboda ya raba ni da gida ,duk karshen sati sai in ce zan je gida, sai wata rana ya tunatar da ni cewa yanzu fa ni matar aure ce ya kamata in koyi zaman gidan miji.Na tashi da sanin muhimmanci ’yan’uwa kuma nasan ’yan’uwana ko da yaushe suna tare da ni.
Burina ina karama
A gaskiya na so na zama lauya saboda antina da ta mutu lauya ce.Duk lokacin da ta sa rigarta da hularta tana ba ni sha’awa.Bayan na gama sakandare sai na koma sha’awar aikin jarida.Sai na kasance mai sha’awar rubutu da kuma damuwa da abin da yake gudana a kasa.Na zabi Jami’ar Bayero ne saboda in yi karatun koyon aikin jarida domin a lokacin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ba sa yin wannan karatu.Bayan na yi karatun sharer fage a Jami’ar sai aka ba mu zabi,to sai na tsinci kaina a karatun Kimiyyar Siyasa.
Amma da yake ina da sha’awar karatun aikin jarida, sai na yi shi a digiri na biyu .Lokacin da na tsinci kaina a matsayin jagora ta sashen Labarai na ji dadi. Domin dakin Labarai ya kasance wuri mai sanya ni matukar farin ciki .
Kasancewa ta uwa
Na yi aure a shekarar 1984,ban sami haihuwa ba sai a shekarar 1987,lokacin da na samu ciki ban sani ba,bayan na sani,na yi matukar fari ciki.Idan na tuna wahalhalun da na sha a baya,kuma sai in ji dadi ganin cewa ina da da ga shi har ya girma,sai na rika yi wa Allah godiya da na kawo har wadannan shekarun.Babban dana ya gama bautar kasa kwanan nan. Mace ba za ta kasance uwa ba sai ta iya fuskantar duk kalubalen da yake ciki da kuma duk wani abu da ya biyo baya.Akwai jin dadi a duk lokacin da ka ga ’ya’yanka suna girma suna zama manyan gobe.
Wanda ya yi matukar tasiri a rayuwata
Mahaifina zan ce,saboda mahaifiyata ta kasance mai shiru-shiru amma akwai yadda take kula da mu.Ta koya mana karatun Baibul kuma tana hora mu yadda ya kamata.Mahaifinmu ba ya yi mana komai,amma yana wurin yana nuna mana yadda za mu yi abubuwa.Muna tashi kullum da karfe shida na safe domin yin addu’a.Na fahimci Baibul shi ne littafin da zan rikedomin iyayena sun nuna mana yadda za mu yi addu’a da kuma imani Allah.Na tuna lokacin ina karama ina aji shida na yi azumi tare da addu’ar neman nasara a jarabawar karshe ta fita daga firamare.Na ce zan yi azumin ne kamar yadda na ga mahaifina yana yi domin neman nasara.Bayan na ci jarrabawar sai na ca ashe idan mutum ya yi azumi kuma ya yi addu’a Allah yana karba.Mahaifina ya yi matukar tasiri a gare ni, saboda yana son yaransa kuma yana kyakkyawan fata a gare su.Kuma yakan ce duk abin da mutum yake so ya zama zai iya, matukar ya mayar da hankali.
Yadda na hadu da maigidana
Lokacin ina Jami’ar Bayero,akwai kawuna a Kano wanda yake ziyarta ta .Yana kai ni in sayo abubuwan da nake so.Wata rana sai ya zo da wani muka fita tare domin cin abincin rana,sai na lura ni kadai nake cin abinci suna kallona,sai na ce ba za ku ci ba? Sai suka ce sun ci nasu ,sai suka mayar da ni makaranta.
Bayan an yi haka,sai ga wannan mutumin ya zo shi kadai wurina,da na tambaye shi game da kawuna sai ya ce zazzabi ne yake damunsa kuma yana son gani na .Sai na bi shi na tarar da kawuna lafiya kalau a gida,dabara ce kawai domin ya hada ni da wannan mutumin.
Daga nan sai ya fara zuwa gani na a makaranta shi kadai.Lokacin da muka fara fita ya sa kidan Barry White a motarsa,sai ya ba ni kaset din saboda ina son kidansa.Muna yawan fita amma bai nuna min ya sona ba sai bayan na gama makaranta ina shirin tafiya bautar kasa.Daga nan sai muka yi aure.
Babbar kyautar da ya yi mini
Lokacin da na haifi ’yata ta biyu,ya ba ni sabuwar mota,a ranar na dawo gida na tarar da mota a kofar gidana ,sai na tambayi direba ko ya san mai motar ,amma sai ya kama dariya.Ban ankara ba sai na ga mijina ya miko mini makulli ya ce”sabuwar jaririya, sabuwar mota”,sai farin ciki ya kama ni.
Bayan wannan kuma duk lokacin murnar bikin haihuwata,yakan saya mini tsalelen agogo.
Hada aiki da aikin gida
Ina da yara da miji masu fahimta,domin kuwa lokacin mijina yana raye, shi ne makamin ci gabana a matsayina na ma’aikaciya.
Mutanen da nake son koyi da su
Ina so in zama kamar Fasto dina,ta yi nisa a rayuwa,ta rasa mijinta,amma duk lokacin da na ganta ,a matsayina na wadda ta rasa miji,sai in ji babu abin da zai hana ni aiki tukuru kamar ita.Lokacin da mijina ya mutu,sai ta ce min “Kin ga Hannatu,in dai zan iya jurewa ke ma za ki iya”.A watan Jun ne mijna ya cika shekara daya da mutuwa,duk lokacin da na ji abin duniya ya yi mini zafi sai in tuna ta.
Akwai antina Rhoda ta rasu,mace ce mai dabara da juriya.Nakan fada mata yadda nake so in zama kamar ita.A wajen kwalliya ma ta kware.Wadannan su ne mutanen da nake so in yi koyi da su.Ina so in yi koyi da cikakkiyar rayuwa kamar Isa Al-masihu.
Yadda nake hutawa da iyalina
Ina son zama tare da ’ya’yana domin suna da ban mamaki,akwai lokacin da suka ba ni mamaki da wani bikin tuna ranar haihuwa kwanan nan.Bikin ya kayatar kuma kowa ya yi farin ciki.
Makadin da na fi so
Panam Percy, yana daya daga cikinsu .Sai Barry White kamar yadda na fada a baya ,kuma ina son kida mai sanyi mai shiga zuci,wasu lokutan nakan saurari kidan Juju na Yarbawa na yi rawa.Kuma ’ya’yana sukan kawo irin nasu kidan mu yi rawa tare da su.
Abin da na fi tsoro
Ina tsoron mutuwa,ina tsoron wata rana kada mijina ya mutu ya bar ni ni kadai ,hakan ce kuwa ta kasance.Amma daga nan kuma sai na daina jin tsoron mutuwa.Yanzu ina kokarin daina jin tsoron komai,kuma ina ci gaba da aiki da imani da AIIah domin shi ne mai komai.
Abin da na koya a rayuwa
Ka dogara ga Allah ,ka rabu da mutum domin kada ka ji kunya.
Wurin da kika fi so ki shakata
Mun je wurare da yawa tare da mijina,amma yanzu na fi son kauyena in da zan ci abincin gargajiya.Duk ranar farkon watan Janairu ka tsince ni a can kauyenmu Kagaro.
Abin da ya sa nake ci gaba
’Ya’yana sun kasance duk abin da suka sa a gaba suna ba shi matukar muhimmanci, don haka nake godiya ga Allah.Yanzu da mijina ya mutu su ne suke faranta min rai.
Abubuwan da nake so a tuna ni da su
Sadaka-Na kasance ina cikin aiyukan wasu daga kungiyoyi masu zaman kansu a yanzu.A shekarar 2003,mun fara dan wani abu da kawayena guda biyu,game da marayun da suka rasa iyayensu sakamakon cuta mai karya garkuwar jiki.Mun fara da mutanen da ba su wuce talatin ba,duk shekara muna shirya musu liyafa kuma mu ba su kyauta domin kada su ji kamar an manta da su.
Amma yanzu wannan kungiya ta kara girma domin yanzu muna da mutane sama da dari hudu,lokacin da muka fara mun sami taimako kadan muka dafa abinci a gidana.Yanzu ga shi muna da yaran da muke daukar nauyinsu a makaranta kuma suna kokartawa.