Misis Lydia Lodam: Mata a kama sana’a da karatu

Misis Lydia Lodam ita ce Babbar Sakatariyar Hukumar Fansho ta Ma’aikatar kananan Hukumomin Jihar Filato. Ta ce takan taimaka wa mata musamman wadanda suka shiga cikin wani mawuyacin hali, wajen daukar nauyin karatun ‘ya’yansu. Tana cikin kungiyoyi da dama,wadanda suke ayyukan ci gaban al’umma. Ta ce Lokacin da mata za su tsaya su zuba wa […]

Misis Lydia Lodam: Mata a kama sana’a da karatu

Misis Lydia Lodam ita ce Babbar Sakatariyar Hukumar Fansho ta Ma’aikatar kananan Hukumomin Jihar Filato. Ta ce takan taimaka wa mata musamman wadanda suka shiga cikin wani mawuyacin hali, wajen daukar nauyin karatun ‘ya’yansu. Tana cikin kungiyoyi da dama,wadanda suke ayyukan ci gaban al’umma. Ta ce Lokacin da mata za su tsaya su zuba wa maza ido don su tallafa musu ya wuce.

 

Tarihinta
Sunana Lydia Lodam, an haife ni a shekarar 1947 a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, iyayena sun je garin Saminaka ne aikin bushara. Mun dawo gida garin Du da ke karamar Hukumar Jos a Jihar Filato a shekarar 1949. Na yi makarantar firamare a Du, bayan na kammala sai na wuce makarantar sakandire ta garin Gindiri, ana cikin haka ne kuma sai na koma makarantar sakandire a Oturkpo da ke Jihar Binuwai, inda a can na kammala karatuna na sakandire.
Daga nan na wuce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na yi digiri, sannan na sake halartar jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi na kara karatu.
Aiki
Na fara aiki a karamar Hukumar Jos a shekarar 1964, wanda a lokacin ba a raba karamar hukumar zuwa kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da kuma Jos ta Gabas ba. Na yi aiki a wannan karamar hukuma na tsawon wasu shekaru har na kai matsayin ma’aji a 1976.
A shekarar 1977 aka dawo da ni ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta Jihar Filato, na yi aiki a wannan ma’aikata har na kai matsayin darakta. Daga nan na yi ritaya a watan Disamba a shekarar 1990.
Bayan na dawo gida ne sai aka kira ni aka ba ni rikon shugabancin karamar Hukumar Jos ta Arewa daga watan Afrilu zuwa Oktoba duk a shekarar 2008.
Bayan haka cikin Oktoba a shekarar 2012 aka sake nada ni Babbar Sakatare a Hukumar  Fansho ta Ma’aikatar kananan Hukumomin Jihar Filato. Mukamin da nake kai har ya zuwa wannan lokaci.
Nasarori
A gaskiya na samu nasarori da dama a rayuwa ciki har da wuraren da na yi aiki. Kamar a lokacin da na yi shugabancin karamar hukumar Jos ta Arewa na tarar da basussukan albashin ma’aikata da alawus-alawus dinsu masu yawa da ba a biya su ba, amma na yi kokari na biya dukkan wadannan basussuka. Na yi ayyukan raya kasa da dama a wannan karamar hukuma kamar gina rijiyoyi da kwalbatoci da gyara gine-ginen ofisoshin sakateriyar karamar hukumar. Haka kuma a lokacin da na zo Hukumar fansho ta ma’aikatan kananan hukumomin Jihar Filato, na tarar da ma’aikatan ba su da ofisoshin da za su gudanar da ayyukansu, kuma da dama ba su san ma aikin da suke yi a wannan ma’aikata ba. Na samar wa kowanne ma’aikaci ofishin da zai gudanar da aikinsa, kuma na ba kowane ma’aikaci aikin da zai yi. Don haka a yanzu komai yana tafiya daidai a wannan ma’aikata.
A lokacin da na zo ma’aikatar fansho na tarar da sunayen wasu tsofaffin ma’aikatan da tun a shekarar 1980 suka yi ritaya, amma ba a biya su hakkokinsu ba. Amma wannan gwamnati ta Jonah Jang ta taimaka mana wajen biyan ma’aikatan da suka yi ritaya hakkokinsu. Bayan haka, sakamakon halin matsin rayuwa da muke ciki, a kullum ina taimaka wa mata musamman wadanda suka shiga cikin mawuyacin hali, wajen daukar nauyin karatun ‘ya’yansu da dai sauransu.

kalubale
Duk da cewa ni mace ce ban fuskanci wani kalubale ba a dukkan wuraren da na yi aiki ba, domin na tafiyar da ma’aikatata ta hanyar gudanar da ayyukana tsakani da Allah.
kungiyoyi
 Ina cikin kungiyar zumuntar mata ta cocin COCIN da kungiyar Sabon Rai da kungiyar samar da zaman lafiya da sauran kungiyoyi da dama.
Iyali
Na haifi ’ya’ya shida amma na farkon wanda yake namiji ne ya rasu, a yanzu saura guda biyar, kuma na shaku da wadannan ‘ya’yana kwarai  da gaske.
kasashen da na ziyarta
 Na ziyarci kasashe da dama da suka hada da Ingila da Poland da Kamaru da Nijar da Afrika ta Kudu da dai sauransu.
Shawarata ga mata
A kullum nakan ba mata shawara su tashi tsaye su yi karatu, domin matar da ta yi karatu za ta iya yin abubuwa da dama wadanda idan har ba ta yi karatun ba, to ba za ta iya yin su ba. Idan mace ta yi karatu za ta taimaki ‘ya’yanta da mijinta, kuma musamman a wannan lokaci da maza suke yawan mutuwa idan miji ya mutu ya bar mata ‘ya’ya to za ta iya taimaka musu ba tare da sun rika bara ba. Lokacin da mata za su tsaya su zuba wa maza ido don su tallafa musu ya wuce.
Burina
Babban burina bayan na kammala wannan aiki shi ne na koma gona, domin ina da gonar da nake zuwa duk ranar da ba na aiki.
Sutura
Ina sha’awar sutura mai rufe jikin mace. Amma ba na sha’awar irin kayayyakin nan da yaranmu na zamani suke sanyawa, wadanda ba sa rufe jiki. Don haka ina shawartar matasa maza da mata su rika sanya suturar da za ta rika rufe jikinsu.
Abincin da na fi so
Ni Birom ce don haka ina sha’awar gwate da kunu da tuwo.