Misis Mbantira D. Baido: Kada a ci zarafin mata

Misis Mbantira danladi Baido,ta yi aikin Banki,amma ba ta dade ba ta bari ta koma kasuwanci inda ta bude kamfani mai suna Maycon Farm. Kuma ita ce Shugabar Cibiyar Trustcare Foundation da ke Abuja. Tarihin rayuwata Sunana Mbantira danladi Baido ,mahaifina soja ne,dan jihar Borno ya fito daga karamar hukumar Chibok. An haife ni a […]

Misis Mbantira D. Baido: Kada a ci zarafin mata

Misis Mbantira danladi Baido,ta yi aikin Banki,amma ba ta dade ba ta bari ta koma kasuwanci inda ta bude kamfani mai suna Maycon Farm. Kuma ita ce Shugabar Cibiyar Trustcare Foundation da ke Abuja.

Tarihin rayuwata

Sunana Mbantira danladi Baido ,mahaifina soja ne,dan jihar Borno ya fito daga karamar hukumar Chibok. An haife ni a Garkidada da ke jihar Adamawa kasancewar mahaifiyata daga can take, bayan haihuwata da sati biyu iyayena suka koma jihar Legas,na yi makarantar firamare a makarantar ‘ya’yan sojoji da ke Apapa a Legas .Daga nan na tafi makarantar sakandare ta gwamnati da ke garin Mubi a jihar Adamawa.Na je jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na yi karatun difuloma a fannin Aikin Banki.Daga nan kuma sai na yi karatun digiri a fanin Akanta a jami’ar Abuja.Na yi karatun babbar difuloma a bangaren Gudanarwa a jami’ar Calabar da ke jihar Cross Riber.Na yi aiki a bankin Nageriya na kasuwanci da masana’antu da ke jihar Legas,kuma na yi aiki a bankin Gamji da ke Abuja .Daga nan sai na bari na fara kasuwanci, na bude kamfani mai suna Maycan farm, ina kiwon kifaye da kaji har awaki ina kiwo ina sayarwa. A shekarar 2008 na bude cibiyar Trustcare foundation. Dalilin bude wannan cibiya shi ne, na je wajen wani biki da ya shafi ‘yan mata, inda aka ce duk wadda aka taba cin zarafi ta tashi sai na ga kusan duk ‘yan matan sun tashi wasu ma kanana ne.Sai na tambaya cewa wane irin taimako ake bai wa irin wadannan’yan mata,sai aka ce addu’a ake yi musu kawai su koma inda suka fito.Sai na ce bai kamata a bar su haka ba.Tun daga wannan lokaci na fara tunanin cewa ya kamata a sami muryar da za ta rika taimakon wadannan ’yan mata. Na nemi shawarar maigidana ya ba ni hadin kai.Amma ya ce mu fara daga gida, saboda haka muka tafi Taraba muka fara kaddamar da wannan cibiya domin shi dan can ne. Muka ba da sanarwa a coci da masallatai.Nan da nan wuri ya dinke da mata.Na fara da tambayarsu da ba su shawarwari.Wadansu iyayensu sun mutu ba halin ci gaba da makaranta.Akwai wata yarinya na gan ta da jaririya na tambaye ta dalilin zuwanta wurin sai ta ce ta ji an ce ina ba da taimako ne.Sai na tambaye ta irin taimakon da take bukata ,ta ce tana so ta ci gaba da makaranta har zuwa Jami’a, amma ba yadda za ta yi.Sai ta ci gaba da cewa iyayenta sun mutu ta zo nan Abuja gidan Antinta sai mijin ya neme ta amma ta gudu gidan wata Antin tata,ta fara sayar da kunun zaki , a nan ne ta hadu da wani ya yaudare ta ya biya mata kudin makaranta naira dubu daya kudin zangon karatu daya , ya yi mata ciki.Kuma aka neme shi aka rasa.Saboda haka ta zama abar tausayi.Haka ire-iren wadannan ‘yan mata suka yi ta ba ni labari, ban san lokacin da na fara kuka ba saboda tausayi.Kuma ga shi kudin makarantar tasu bai wuce dubu daya ko dubu daya da dari biyar ba, abin da bai fi mutum ya sayi katin waya ba.Me zai hana mu taimake su?Saboda haka akwai wadanda muka mayar da su makaranta wadansu kuma muka koya musu sana’o’in hannu kamar dinki da sana’ar gyaran gashi kuma muka ba su jari.Bayan wata shida na koma wajensu,suka ce rayuwarsu ta canza kuma nima na ga hakan. Akwai wata yarinya a Buwari Babanta ya mutu mahaifiyarta gurguwa ce ,tana son ta zama likita, ga shi ba halin karatu , mun sa ta a makaranta har ta fara yin nisa.Idan ba a taimaka wa irin wadannan yara ba, haka rayuwarsu za ta lalace. Saboda haka yawancin yaran da muka sa a makaranta,yanzu duk sun canza kamar ba su ba.
Abin da yake faranta min rai
Duk lokacin da na ga ‘yan matan nan da kayan makaranta a cikin aji suna karatu domin su cika burinsu ina mutukar farin ciki.Domin kuwa muna zuwa duba su duk bayan wata daya domin mu tabbatar suna zuwa kuma suna kokari .kuma na gaya musu idan suna so su zama farfesa, ko su fita kasar waje su yi karatu, matukar ina da hali zan taimaka musu.Ina farin ciki cewa Allah ya ba ni iko in taimaki wadanda suka kasa.
Hada aikin gida da aikin wannan cibiya
Ni mace ce wadda nake lissafin duk abin da zan yi.Misali muna zuwa kasuwa sau daya a wata mu sayo kayan da ba za su lalace ba.Kin ga ba zuwa kasuwa kullum.Ina zuwa ofis karfe sha daya zuwa karfe biyar.Kafin in fita sai na shirya gida na sallami mai gida .Idan na dawo lokacin ‘ya’yana sun dawo daga makaranta, sai in duba aikinsu na makaranta.Saboda haka aikin cibiyar Trustcare foundation ba ya hana ni aikin gida.
Iyali
Maigidana shi ne danladi Baido dan jihar Taraba ne,kuma dan siyasa ne,’ya’yana uku mace daya maza biyu.’Yata ta farko shekararta bakwai, na biyu shekararsa biyar,karamin shekararsa biyu.
Burina ina karama
Da ma can ina sha’awar taimakon mutane.Domin ba na mantawa akwai wani almajiri a kusa da gidanmu Babansa gurgu ne mahaifiyarsa makauniya.Nakan taimaka masa har na san sunansa.
Yadda nake hutawa
Kowace rana ina hutawa,kuma a karshen sati ban cika fita ba sai ta kama.Kuma ina cin abinci mai kyau ba na wasa da abincina.Ina cin abinci mai gina jiki ba komai nake ci ba.Kuma a shekara mukan je kasar waje sau daya.
kasashen da na ziyarta
Na je kasahe kamar Sifen da Amurka, na je Italiya da Faris da Yuro da Romaniya,na je Isra’ila da Sinigal da China da Laberiya da Dubai. Na je Ghana,na je Holland na je Landon wadanda zan iya tunawa a kaina ke nan.
Nasarori
Akwai nasarori domin mun mayar da wasu yaran makaranta,duk da wasu iyayen ba sa ba mu hadin kai wajen amsa kiranmu. Wani lokaci shugabanin makarantu ne suke nuna mana wadanda iyayensu suka kasa.Saboda haka nasarorin kadan ne.Amma idan aka san mu,kuma ana ba mu tallafi,na tabbata za a sami nasarori masu yawa.