Misis Sara Pane: Iyaye su bai wa ’ya’ya mata ilimi

Misis Sara Pane, kwararriyar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ta yi gwagwarmaya a harkar koyarwa har ta shugabanci makarantar sakandare kafin ta ajiye aiki sanda ta kai matakin Babbar Sakatariya tun tsohuwar Jihar Bauchi, yanzu haka kuma ita ce mai bai wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin ci gaban al’umma da ayyuka na musamman. […]

Misis Sara Pane: Iyaye su bai wa ’ya’ya mata ilimi
Misis Sara Pane: Iyaye su bai wa ’ya’ya mata ilimi

Misis Sara Pane, kwararriyar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ta yi gwagwarmaya a harkar koyarwa har ta shugabanci makarantar sakandare kafin ta ajiye aiki sanda ta kai matakin Babbar Sakatariya tun tsohuwar Jihar Bauchi, yanzu haka kuma ita ce mai bai wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin ci gaban al’umma da ayyuka na musamman.

Tarihin rayuwata
Kafin na yi aure sunana Sara dan’azumi amma da na yi aure sai na koma amfani da sunan maigidana shi ya sa ake kirana Serah Pane, ni haifaffiyar
garin Rinjin gani ce a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi kuma ni ‘yar asalin kabilar Jarawa ce, amma mijina Batangale ne dan asalin karamar hukumar Billiri a jihar Gombe. An haifeni a nan garin Rinjin gani a garin Toro a shekarar 1952 na fara makarantar Firamare dina a garin Fobor dake Jos ta gabar lokacin tana karkashin Bauchi N.A (Natibe Authority) amma a shekarar 1976 sai aka mayar da ita garin Jos na Jihar Filato. A 1963, na samu shiga aji biyar zuwa bakwai a wannan makaranta a Bauchi, tsararriyar Firamare ce wacce take karkashin N.A ,daga cikin malamanmu har da Turawa. Daga kan mu ne aka fara bangaren sakandare sai aka canza mata suna ta koma Probisional Girls Secondary School a shekarar 1966 .Ana nan ba’a dade ba aka mayar da makarantar ta gwamnati inda gwamnati ta karba daga wajen Turawan N.A ta koma GGSS Bauchi. Mune daliban farko da aka fara yayewa a shekarar 1970. Bayan da na gama Sakandare sai na samu tafiya makarantar HSC wato makarantar share fagen shiga jami’a wacce ita ce madadin IJMB a wancan lokacin inda na je Maiduguri a shekarar 1971 zuwa 1972 .Bayan na gama a lokacin, idan mutum ya gama gwamnati ba ta barinsa ya bata lokaci sai a tura ka koyarwa na wata tara ,saboda haka sai aka tura ni WTC Azare kafin na shiga jami’a. Ina gama wata tara sai na tafi Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU ) inda na samu shaidar digiri dina na farko a bangaren Turanci( English Education) na gama a shekarar 1976, amma kafin na gama a 1974 aka yi min aure .A lokacin da na kammala jami’a a shekarar na haifi ‘yata ta fari ,ga digiri ga ‘ya, sannan aka tura ni hidimar kasa a nan jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya amma da yake matan aure ana tura su inda mazajensu suke sai aka dawo da ni garin Bauchi kusa da maigidana.
Aiki
Na fara aiki ne da ma’aikatar ilimi ta Jihar Bauchi bayan na gama hidimar kasa lokacin a TC Bauchi , ban dade ina koyarwa ba a watan Janairu na shekarar 1979 sai aka ba ni mukamin mataimakiyar shugabar sakandare wato (bice Principal) a sakandaren ‘yan mata ta Kaltungo WTC. Daga nan sai aka dawo da ni Bauchi saboda maigidana yana aiki a can, aka mai da ni GGSS Bauchi a 1980 a wannan matsayi na mataimakiyar shugaban makarantar bayan shekara biyu. A 1982 sai aka sake mai da ni WTC Nabordo nan kuma a matsayin shugabar makarantar wato Principal, na je na yi wasu ‘yan watanni kadan a inda makarantar take na wucin gadi a Toro.A watan Satumba na dawo da makarantar matsuguninta na dindindin na yi shekara biyar ina Principal, daga na sai aka dawo da ni hedkwatar Ma’aikatar
ilimi a lokacin mulkin farar hula na marigayi Alhaji Dahiru Muhammad Deba a watan Janairu na 1992 ya ba ni mukamin Babbar Darakta wanda yake daidai da matsayin babban sakatare don lokacin babu babban sakatare, kuma ko hutu Kwamishinanka ya tafi kai za ka iya rikon kwarya, bayan na yi shekara daya sai aka tura ni Ma’aikatar Ciniki da Kasuwanci nan ma na yi shekara biyar . Bayan Janar Sani Abacha ya bai wa Gombe jiha a shekarar 1996 sai aka dawo Gombe kuma ni na dawo da ma’aikatar daga Bauchi a matsayin babbar Sakatariya, nan ma ban dade sosai ba sai aka kai ni Ma’aikatar Lafiya a 1997 na yi shekara daya, aka sake mai da ni Ma’aikatar Ilimi ,daga nan aka sake mai da ni Ma’aikatar Watsa Labarai, sai aka sake mai da ni Ma’aikatar Ilimi a karo na uku. Bayan da siyasa ta dawo lokacin danjuma Goje ya karbi mulki daga wajen Habu Hashidu a jam’iyyar ANPP sai ya yi min ritaya duk da
cewa a lokacin ina da sauran shekara tara na aiki, domin shekaruna na aiki 26 ne, na haihuwa kuma ina wajen 51. Daga nan sai na dawo gida na zauna wajen shekara takwas a billiri har na fara taba siyasa. Ina nan ina siyasa kwatsam sai maigirma Shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya
ba ni mukamin mai taimaka masa a bangaren harkokin ci gaban al’umma. Daga baya aka kara min da na ayyuka na musamman shekara uku da rabi ke nan yanzu, an ba ni mukamin ne a watan Yuni na shekarar 2011.
kalubale
Na fuskanci kalubale mai yawa domin tafiyar da aikin gida da na ofis ga goyon ’ya’ya ba karamin aiki ba ne ga matsayi domin ina cikin tashena lokacin ban wuce ‘yar shekara 24 ba na fara haihuwa domin ban jima ina koyarwa ba aka ba ni matsayi wanda tafiyar da wannan matsayi kasancewa ta mace babban kalubale ne domin ina da maigidana ga yara sannan ga kula da yara ’yan mata a makarantar kwana kuma kullum sai ka san halin da dalibanka suka kwana suka tashi.
Nasarori
Na samu nasara a aikin da na yi na Malanta saboda wasu kungiyoyi da yawa sun karramani sannan kuma har yanzu idan maigirma gwamnan Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo zai gudanar da wani abu yakan dauko ni ya sa ni a kwamiti wanda ya shafi ci gaban ilimi ko na al’umma . Kuma tun a lokacin mulkin soja ma ina samu ana sa ni kwamitoci daban- daban saboda kwarewata a aiki wajen gudanar da tsare-tsare kan ilimi ko na kula da ma’aikatan gwamnati.

Lambar yabo
Na samu lambar yabo ta Principal Emeritus, wanda kungiyar tsofaffin shugabanin makarantun sakandare ta kasa suka ba ni.
Abin da na fi so a tuna ni da shi
Ina son ko bayan ba ni a dinga tuna ni a matsayin uwa wacce ta damu da son ganin ’ya’ya sun sami ilimin zamani musamman ma ’ya mace wacce aka bar ta a baya, kuma ina son kafin na bar duniya in kirkiro wata cibiya da za ta koya wa matasa sana’oi wanda yanzu haka ina shirin kafa gidauniya wanda za ta ba ni dama na koya wa matasa ayyukan yi don dogaro da kansu ba sai sun jira gwamnati ta yi musu ba.
Siyasa
Na shiga siyasa ne domin ina tuna abokan aikina da aka yi mana ritaya tare da su a lokacin da muke aiki .Wanda kuma an yi mana ritayar ne saboda siyasa bayan na zauna a gida na tsawon wasu shekaru sai ga shi Allah Ya sa siyasar ta zamo mini alheri, domin na zama mai bai wa shugaban kasa shawara, wani abu kuma shi ne wasu na ganin duk macen da take siyasa ana yi mata kallon marar daraja ,ba haka bane, inda a wasu wuraren hakan ne yakan hana wasu matan fitowa takara ko kuma su shiga a dama da su.
Iyali
Ina da ’ya’ya bakwai, maza shida mace daya,dan autana shi ne mai shekara 28 na haifeshi ina da shekara 33 kuma duka sun kammala jami’a.
kasashen da na taba ziyarta
Na je kasar Isra’ila, na je Swaziland, na je Habasha, na je Afirka ta Kudu, na je Amurka da Ingila da sauransu. Sannan kuma na taba zama mamba a
kungiyar Malaman Makaranta lokacin ina aikin koyarwa. Sai dai ina da wata gidauniya mai suna World Poberty Foundation da nake kokarin kafa ta don taimakawa talakawa wajen magance musu radadin talauci.
Tufafin da na fi kauna
Kasancewa ta mace ’yar Arewa mai daraja da kima na fi sha’awar sutura wanda zata rufin dukkan jikina domin mace ko ina tsiraici ne ba kamar
namiji ba.
Shawara ga iyaye
Ya kamata a ce iyaye yanzu sun gane muhimmanci karatun ’ya mace ba sai kullum ana ta nanata musu ba. Saboda kamar ni yanzu mai bai wa shugaban kasar Najeriya shawara ce kan harkokin ci gaban al’umma da ayyuka na musammam. Kuma daga kauye na fito Ubana talaka ne da ban yi karatun nan ba da ya ya za’ayi a san ni har na samu wannan matsayin da nake kai? Ashe ko don irin haka ya kamata a ce iyaye suna hankalta wajen bai wa ’ya’yansu ilimi musamman ’ya’yan mata, talla kuma da iyaye suke dora wa ’ya mace ba abin dogaro ba ne saboda wajen talla jami’a ce mai zaman kanta na lalacewar tarbiyar ’ya’ya mata kuma hanya ce ta jawowa a yi wa yarinya fyade. Sannan ina kara kiran iyaye da cewa su dinga jan ’ya’yansu a jiki wanda hakan zai sa ko sun shiga matsala za su iya gayawa iyayen don shawo kan lamarin cikin sauki ba kamar idan suna korarsu a kusa dasu ba.