Misis Serah Yusuf: Burina in zama garkuwar mata

Misis Serah Yusuf, ita ce Kwamishinar Muhalli ta Jihar Filato, ta yi fice kan aikin jinya tare da  wayar  da kan al’umma kan mahimmancin tsafta  da kuma  tallafa wa mata wajen koyan sana’o’in da za su rike kansu. Ta ce burinta ta zama garkuwa ga mata.Tarihin rayuwataSunana Serah Yusuf, an haife ni a barikin sojoji […]

Misis Serah Yusuf: Burina in zama garkuwar mata
Misis Serah Yusuf: Burina in zama garkuwar mata

Misis Serah Yusuf, ita ce Kwamishinar Muhalli ta Jihar Filato, ta yi fice kan aikin jinya tare da  wayar  da kan al’umma kan mahimmancin tsafta  da kuma  tallafa wa mata wajen koyan sana’o’in da za su rike kansu. Ta ce burinta ta zama garkuwa ga mata.
Tarihin rayuwata
Sunana Serah Yusuf, an haife ni a barikin sojoji na garin Abeokuta a Jihar Ogun, kasancewar mahaifina ya yi aikin soja. Bayan ya bar aikin soja ne ya dawo gida, ya shiga aikin dan sanda, saboda a lokacin da yake aikin soja a kullum idan ya zo gida, sai mahaifiyarsa ta rika kuka saboda sun shaku sosai. Don haka ya yi ritaya ya dawo gida, ya shiga aikin dan sanda. Mu shida ne a wurin mahaifinmu kuma ni ce ta farko.
Na yi makarantar  St. Lus da ke Jos, bayan da na kammala sai na tafi makarantar koyan aikin jinya karkashin asibitin Murtala Muhammad da ke Jos. Daga nan na yi rijista da kungiyar ungozomomi  ta Nijeriya.
Bayan haka na tafi Ibadan, na je na yi wani kwas kan tsarin iyali da tazarar haihuwa.  Daga nan sai wata kungiya daga kasar Amurka ta nemi ma’aikatan jinya masu kokari wadanda za su yi kwas din koyon aikin jinya a jami’ar Atlanta da  ke Amurka. Bayan mun cik takardun ne Allah Ya ba mu sa’a aka zabe mu, mu biyu. Wannan kungiya ce ta dauki nauyinmu.
Iyali
 Bayan da na kammala makaranta aka yi mini  aure, kuma  ina da ’ya’ya har  da jikoki.
Burina a lokacin da nake karama
 Burina a lokacin da nake karama in zama lauya, amma mahaifina ya fi son na yi aikin asibiti. Dalilinsa shi ne aikin asibiti aiki ne mai albarka, kuma ya ce ya fahimci ina da shiru-shiru da kuma tausayi. Don haka aiki ne da ke bukatar mutum mai tausayi da son taimakon jama’a. Don haka na ajiye burin zama lauya na rungumi aikin jinya.
Ayyukan da na yi
Na fara aikin jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH). Daga nan sai wani kamfanin magunguna daga kasar Amurka  da ake kira Stlang Health ya nemi mai aikin jinya da za ta sayar masa da magungunan da yake yi. Sai aka kira mu a ma’aikatar kiwon lafiya muka yi jarrabawa, kuma Allah Ya ba ni nasara aka dauke ni. Daga nan aka kai ni shiyyar jihohin Arewa maso Gabas domin a lokacin kamfanin ya raba Najeriya kashi uku. A lokacin ina zuwa asibitoci da manyan shagunan sayar da magunguna ina sayar musu da magungunan da wannan kamfani yake yi.  Na yi aiki da wannan kamfanin na tsawon shekara biyar. Bayan nan, aka sake dauka ta aiki a wannan kamfani tsawon shekara uku. Daga nan na yi ritaya daga aiki na tsunduma cikin  harkokin siyasa.
kalubale
Na fuskanci kalubale a lokacin da nake aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH). kalubalen shi ne, ina mace, kana ina aikin asibiti kuma  zan je aikin dare na kwana, ga shi ina da yaro karami da nake shayarwa a gida. Hankalina yana gida wajen yaron da na bari, kuma hankalina yana wurin aiki. Na tsinci kaina a wannan hali. Don haka wannan babban kalubale ne da na fuskanta.
Bayan haka, babu abubuwan da za a yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan asibiti a Najeriya. Za ka ga mai jinya yana cikin mawuyacin hali, kuma za ka iya taimaka masa amma babu kayayyakin aiki. Babu shakka irin wadannan abubuwa kalubale ne a gare ni a lokacin da nake aikin asibiti.
Haka kuma a lokacin da na yi aiki a kamfani magunguna, a kullum ina cikin tafiye-tafiye kuma an rika sanya mini yawan adadin magunguna da ake son na sayar a wata uku. Domin kamfanoni masu zaman kansu haka suke. Idan mutum bai sayar da yawan adadin kayayyakin da ake son ya sayar ba, za a iya korarsa daga aiki. Amma ni a lokacin Allah Ya taimake ni har ina wuce yawan adadin magungunan da ake son na sayar.
Kuma irin suturun da mata suke sanyawa a yanki da kamfani ya kai ni sun sha bamban da suturun da mata suke sanya a nan Jos.  Babu shakka na sha wahala kafin na gano haka na koma sanya tufafin da ake sanyawa a wannan yanki.

Bayan haka, a lokacin da na shiga cikin harkokin siyasa, kamar yadda
ka sani ne mata ba su da yawa a cikin harkokin siyasa, kuma sau tari, idan maza suka ga mace ta shiga cikin siyasa sai su nemi bude mata ido, don su tsoratar da ita. Da farko da na shigo siyasa, maza sun bude mini ido, sai a raina na ce ba zan iya siyasa ba. Amma daga baya sai na kwantar da hankalina na ce musu ni sabuwa ce a siyasa, don haka su koya mini. Sai suka fara koya mini siyasa,  na koya, har ya zamanto ina kokarin wuce su. Wannan ma wani babban kalubale ne da na fuskanta.
Sha’awar  siyasa
Mahaifiyata ’yar siyasa ce, don haka ta yi iyakar kokarinta wajen ganin na shiga harkokin siyasa amma na ki. Ta tambaye ni mene ne dalilin da ya sanya ba na son shiga siyasa? Na ce mata babu gaskiya a cikin siyasa, akwai kama-karya da danniya da dai sauransu. Har mahaifiyata ta bar duniya ban shiga siyasa ba.
Amma daga baya,  mutum guda daya ne ya karfafa mini gwiwar shiga harkokin siyasa, wannan mutum kuwa shi ne, Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang.  Bayan mahaifiyata shi ne na biyu da ya ce in shiga harkokin siyasa.
A lokacin da nake aiki da kamfanin magunguna da na yi bayani a baya, na je Makurdi, na ji irin yadda mutanen wannan wuri suke yabawa kan ayyukan raya kasa da Gwamna Jonah Jang ya yi musu a lokacin da yake gwamnan soja a wurin. Don haka da Gwamna Jang ya ce in shiga siyasa nan take na shiga ba tare da bata lokaci ba, kuma  zan ci gaba da siyasa.
Nasarorin da na samu a rayuwa
Babu shakka na samu nasarori masu tarin yawa, misali a bangaren aikin asibiti da na yi.  Sau tari ina haduwa da mutanen da na yi wa jinya, suna cewa ai sun san ni a lokacin da nake aiki a JUTH, suka ce na taimaka musu lokacin da suka yi jinya. Akwai lokacin da na fito daga garin Bauchi zuwa Jos, sai na tsaya a garin Miyabarkatai don na sayi tumatir, sai ga wani mutum mai sayar da wake da wake  da dawa da masara da dai sauransu. Sai ya ce Madam na san ki a Jos a asibitin JUTH, akwai lokacin da na kwanta a asibitin na yi ciwo, kin sha wahala da ni kwarai domin har bayan gidana kika rika diba a lokacin. Sau tari ina haduwa da irin wadannan mutane da na taimakawa a lokacin da nake aikin asibiti suna yi mini godiya, wannan wata babbar nasara ce a gare ni.
Taimakona ga mata
A bangaren siyasa, akwai mata da yawa da na ce musu su zo su shiga siyasa. A yanzu da muke wannan magana da kai, akwai wasu daga cikin irin wadannan mata an ba su wasu mukamai. Ka ga wannan ma wata nasara ce a gare ni.
Bayan haka na taimaka wa mata da dama sun shiga makarantar koyan sana’a da matar gwamnan Jihar Filato ta bude. Ta hanyar cire kudi a aljihuna ina biya musu kudin makarantar ganin ba su da karfin biya. Haka kuma na tallafa wa  mata da dama wadanda mazajensu suka mutu da jari don su rika samun abin da za su ci. Har ila yau, a  wannan ma’aikata ta muhalli da nake kwamishina na ba da dama aikin shara.
Gamsuwa da shigar mata harkokin siyaya
Mata suna kokari wajen shiga ana damawa da su a harkokin kasar nan. Ka san kirge ana farawa  da daya ne kafin  aje biyu har zuwa dari da sauransu. Ai a da da kyar za ka ga mace tana siyasa, amma a yanzu ga mata nan sun shiga harkokin siyasa ana damawa da su, suna gogayya da maza a wani wurin ma har sukan buge maza. Ina fatar mata za su karu a harkokin siyasa a kasar nan.
kasashen da na kai ziyara
Bari na fara da kasashen Afrika. Na je kasar Jamhuriyar Benin da Ghana da Uganda da Kenya da Afrika ta Kudu. A kasashen Turai kuma na je Ingila da Amurka.
Abubuwan da nake sha’awa
Babban abin da yake ba ni sha’awa, wanda idan na gani nakan ji hankalina ya kwanta shi ne wuri mai tsafta.
Abincin da na fi so
Ina son tuwon shinkafa da miyar kuka ko miyar ganye.
Tufafi
Ina son tufafinmu na Afrika. Na fi na sanya dogon siket sannan in daura dankwali.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Bayan ba na nan ina so daga an ambaci sunana a rika cewa matar da taimaka wa jama’a, kuma garkuwa ga mata
Kirana ga mata
Su tashi su shiga harkokin siyasa domin mu gyara Najeriya na farko ke nan.
Kirana na biyu shi ne su rika kasancewa masu tsafta.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno