Mithun Chakraborty: Muhimman fina-finan da ya fito a rayuwarsa
Jarumin Indiya, wanda ya yi tashe a zamanin kuruciyarsa a matsayin gwanin rawa cikin fina-finai, Mithun Chakraborty ya fara fitowa cikin fim ne a shekarar 1976, kuma tun daga lokacin har zuwa yau din nan ana damawa da shi cikin sana’ar, duk kuwa da cewa ya manyanta a halin yanzu.A shekarar da ya fara fim, […]
Jarumin Indiya, wanda ya yi tashe a zamanin kuruciyarsa a matsayin gwanin rawa cikin fina-finai, Mithun Chakraborty ya fara fitowa cikin fim ne a shekarar 1976, kuma tun daga lokacin har zuwa yau din nan ana damawa da shi cikin sana’ar, duk kuwa da cewa ya manyanta a halin yanzu.
A shekarar da ya fara fim, 1976, Mithun ya fito cikin fina-finai biyu ne kacal, wato fina-finan Do Anjane da kuma Mrigayya. A shekarar 1977 kuwa, jarumin ya fito ne a cikin fim guda daya kacal, wato Mukti. A yayin da kuma ya fito cikin fina-finai uku a shekarar 1978, fina-finan Hamra Sansar da Mera Rakshak da Phool Khile Hain Gulshan Gulshan.
A shekarar 1979 kuwa, ya fito ne cikin fina-finai guda shida, wadanda suka hada da Amardeep Habari, Prem bibah, Suraksha, Tarana da kuma Tere Pyare Mein. A shekarar 1980 kuwa, ya samu fitowa cikin guda shida, su ne Patita, Sitara, Tadi, Chor, Aakhri Insaaf, Kasturi da kuma Khwab. Sai kuma a shekarar 1981, inda ya fito cikin fina-finai guda 11, wato Be-Shakue, Chamelee Memsaab, Dhuan, Ghamandee, Hum Paanch, Jeene Ki Arzoo, Laparwah, Main Aur Mera Haathi, Saahas, Sameera da kuma Wardat.
A shekarar 1982 kuwa, ya fito ne cikin fina-finai 8, sun hada da Ustadi Ustad Se, Aadat Se Majboor, Aamne Samne, Ashanti, Disco Dancer, Heeron Ka Chor, Shaukeen da kuma Sun Sajna. Sai kuma 1983, inda ya fito cikin fina-finai 9, wato Faraib, Humse Hai Zamana, Karate, Kaun Kaisey, Mujhe Insaaf Chahiye, Pasand Apni Apni, Takdeer, Woh Jo Hasina da kuma Takdeer Ka Badshah.
A 1984 kuwa, jarumin ya fito cikin fina-finai 11, wato Wanted, Baazi, Boder, Ghar Ek Mandir, Hanste Khelte, Jaakg Utha Insan, Jagir, Kasam Paida Karne Wale Ki, Marriage Bureau, Raksha Bandhan da kuma Tarkeeb. Sai kuma a shekarar 1985, inda ya fito cikin guda 11, su ne Gulami, Karishma Kudrat Ka, Karm Yudh, Maa Kasam, Pyar Jhukta Nahin, Pyari Behna, Aandhi Toofan, Aar Paar, Baadal, Bepanaah da kuma Chaar Maharathi. A 1986 kuwa, ya fito cikin guda daya ne kacal, wato Muddat.
Mithun ya fito cikin fina-finai guda 3 ne a 1987, wadanda kasance Dance Dance, Diwana Tere Naam Ka da kuma Mera Yaar Mera Dushman. A yayin da kuma a 1988 ya fito cikin guda 10 cur, wato Jeete Hain Shaan Se, Mar Mitenge, Pyar Ka Mandir, Rukhsat, Saazish, Sagar Sangam, Wakat Ki Awaz, Agnee, Commando da kuma Gangaa Jamuna Saraswathi. A shekarar 1989 kuma ya fito cikin guda 16, su ne kuwa Daata, Dana Paani, Dost, Garibon Ka Daata, Guru, Hisaab Khoon Ka, Hum Intezaar Karenge, Ilaaka, Ladaai, Meri Zabaan, Mil Gayee Manzil Mujhe, Mujrim, Prem Pratigyaa, Aakhri Ghulam, Bees Saal Baad da kuma Bhrashtachar.
A 1990 ma, fina-finai 10 ya fito, su ne Aakhri Badla, Agneepath, Dushman, Gunahon Ka Debta, Hum Se Na Takrana, Paap Ki Kamaee, Pati Patni Aur Tawaif, Pyar Ka Karz, Pyar Ke Naam kurban, Roti Ki Keemat da kuma Shandar. A 1991 kuwa ya fito cikin guda 5, wato Swarg Yahan Nark Yahan, Trinetra, Numbri Aadmi, Pyar Hua Chori Chori da kuma Pyar Ka Debta. Sai kuma a 1992, ya fito cikin guda 6, sun hada da Dil Aashna Hai, Ghar Jamai, Jhooti Shaan, Mere Sajna Saath Nibhana, Pitambar da kuma Rajoo Dada. 1993 kuma ya fito cikin guda 8, su ne Jeeban Ki Shatranj, Krishan Abtaar, Meherbaan, Pardesi, Phool Aur Angaar, Yugandhar, Aadmi da kuma Dalal.
A 1994, fina-finan da Mithun ya fito guda 9 ne, wato Jallad, Janta Ki Adalat, Krantikshetra, Naaraaz, Parmatma, Rakhwale, Tadipaar, Teesra Kaun da kuma Yaar Gaddar. A 1995 kuma ya fito cikin guda 6, wato Ahankaar, Diya Aur Toofan, Gunehgar, The Don, Zakhmi Sipahi da kuma Ab Insaaf Hoga. 1996, ya fito cikin guda 7, wato Angaara, Apne Dum Par, Bhishma, Danbeer, Jung, Nirbhay da kuma Rangbaaz.
A 1997 kuwa, jarumin ya fito ne cikin fina-finai hudu, wato Daadagiri da Jeeban Yudh da Jodidar da kuma Shapath. A shekarar 1998 kuwa, fina-finai 15 ya fito cikinsu, wadanda suka kasance Suraj, Swami bibekanand, Ustadon Ke Ustad, Yamraaj, Chandaal, Debtaa, Do Numri, Gudia, Gundaa, Hitler, Mafia Raaj, Mard, Military Raaj, Sher-E-Hindustan da kuma Shera. Haka kuma a shekarar 1999, Mithun ya fito cikin fina-finai tara ne, wato Phool Aur Aag, Sanyasi Mera Naam, Sautela, Sikandar Sadak Ka, Tabaahi (The Destroyer), Aaya Toofan (1999), Ganga Ki Kasam, Kahani Kismat Kid a kuma Maa Kasam. A yayin da kuma a shekarar 2000 ya fito cikin guda 12, wadanda suka hada da Aaj Ka Raban, Agniputra, Babu Badshah, Bhayaanak, Billa No. 786, Dada, Justice Chowdhary, Jwalamukhi, Kaali Topi Laal Rumaal, Meri Pyaari Bahania Banegi Dulhania, Sabse Bada Beiman da kuma Sultaan.
A shekarar 2001 kuwa, fina-finai 6 ya fito, wato Arjun Debaa, Baghaawat Ek Jung, Bhairab, Insaaf Ki Jung, Khatron Ke Khiladi da kuma Zahreela. Sai kuma a 2005, inda ya fito cikin guda uku kadai, wato Elaan, Classic da kuma Lucky. A 2006 kuwa, fina-finai hudu ya fito a ciki, su ne Chingaari, Dil Diya Hai, Kachchi Sadak da kuma Sun Zarra. A 2007 kuwa, ya fito cikin fim daya kawai, wato Guru. Haka ma a 2008, ya fito cikin guda shida, wato Zindagi Tere Naam, C Kkompany, Heroes, My Name Is Anthony Gonsalbes, Don Muthuswami da kuma Yubraaj. A 2009 kuwa Mithun ya fito cikin fina-finai guda 9, wadanda suka hada da Chandni Chowk To China, Zor Lagaa Ke Haiya, Luck, Chal Chalein, Baabarr, beer, Phir Kabhi, Raftaar da kuma Raakh. A shekarar 2010 kuwa fina-finai hudu Mithun ya fito a cikinsu, sun hada da Aap Ke Liye Hum, Buddham Sharanam Ghachammi, Yeh Sunday Kyun Aata Hai da kuma Golmaal 3. Wadannan ne adadin fina-finan da jarumin ya fito cikinsu ke nan a tsawon rayuwar sana’arsa ta wasan kwaikwayo.