Mithun Chakraborty ya zama dan majalisa
A makon jiya ne likkafar dan fim din nan na Indiya Mithun Chakraborty ta ci gaba, inda aka zabe shi a matsayin dan majalisa.Kamar yadda sanarwar ta gabata, an zabe shi ne a matsayin daya daga cikin ’yan majalisar da ake kira da lakanin ‘Rajya Sabha’ na jam’iyyar ‘All India Trinamool Congress.’ Shugaban jam’iyyar, wanda […]

A makon jiya ne likkafar dan fim din nan na Indiya Mithun Chakraborty ta ci gaba, inda aka zabe shi a matsayin dan majalisa.
Kamar yadda sanarwar ta gabata, an zabe shi ne a matsayin daya daga cikin ’yan majalisar da ake kira da lakanin ‘Rajya Sabha’ na jam’iyyar ‘All India Trinamool Congress.’ Shugaban jam’iyyar, wanda kuma shi ne minista mai kula da Yammacin Bengal, Mamata Banerjee ne ya bayar da sanarwar.
Ko yaya Mithun ya ji da wannan muhimmin mukami da ya samu na siyasa kuma zai bar harkar fim ne ya koma siyasa gadan-gadan? Tambayoyin da manema labarai suka yi masa ke nan, inda shi kuma ya amsa da cewa ba zai taba barin harkar fim ba a rayuwarsa domin siyasa.
“Harka ta farko da ke cikin rayuwata, ita ce harkar fim kuma ita zan ci gaba da ba muhimmanci, domin kuwa ita ce take samar mani abinci a rayuwa. Haka kuma sana’ar ce dai ta samar mani suna da daukaka. Zan ci gaba da harkar fim kuma ita zan ci gaba da martabawa a rayuwata,” inji dan wasan, wanda a zamanin kuruciyarsa ya kasance gwanin rawa a fim.
An tambaye shi ko ta yaya zai rika hada fim da siyasa kuma ya ba kowace harka hakkinta, sai ya amsa da cewa: “A lokacin da nake cikin fim, zan yi fim ne kawai. A matsayina na dan wasa, zan tsaya kai da fata in aikata abin da fim din ya bukace ni in aikata. Idan kuma na zo bangaren siyasa, zan iya kokarina in kula da hakkokin jama’a daidai gwargwado. Ke nan, yanzu Mithun ya zama biyu ke nan.” Inji dan was an.