Miyagun hanyoyin mu’amala a dandalin abota (3)

Garin Neman Gira…dan Adam akwai son kyale-kyale.  Haka Allah ya halicce shi.  Akwai wata karamar manhaja dake yawo a dandalin abota, musamman na Facebook, wacce ke baka damar sauya lauyin shafinka daga shudi zuwa ja, ko wani launi da kake so.  Sai dai kuma, a yayin da ka latsa wannan manhaja don tayi maka wannan […]

Miyagun hanyoyin mu’amala a dandalin abota (3)

Garin Neman Gira…
dan Adam akwai son kyale-kyale.  Haka Allah ya halicce shi.  Akwai wata karamar manhaja dake yawo a dandalin abota, musamman na Facebook, wacce ke baka damar sauya lauyin shafinka daga shudi zuwa ja, ko wani launi da kake so.  Sai dai kuma, a yayin da ka latsa wannan manhaja don tayi maka wannan hidima, za ta bukaci cewa ka bata damar isuwa zuwa ga bayananka da ke “Profile”, da zarar ka amince shi ke nan, an mallake shafinka.  Ba za ka gane ba.  Domin manhaja ce ta kasuwanci.  Lokaci zuwa lokaci idan kai mai lura ne, za ka rika ganin sakonni a kan farfajiyar shafinka (Timeline), da hotuna, ko bidiyo, wadanda ba kai ka rubuta ba.  Mafi muni ma shi ne, wasu na iya zama hotunan batsa ne.  A duk sa’adda suka cillo maka irin wannan sako, zai zarce cikin dukkan Zaurukan da kake cikinsu, idan a Facebook ne, wato: Groups.   Kwanakin baya shugabannin Zauren Dandalin Ilmantarwa da Nishadantarwa da ke Facebook sun bukaci in duba musu wani daga cikin mambobin zauren, wadanda duk rubutun da aka aiko, sai a ga ya yi ta’aliki (Comment) da hotunan batsa, masu munin gani. Kusan duk inda ka duba haka za ka gani.  Ransu ya baci matuka.  A zaton su dan iska ne, wanda bai da sana’a a Facebook sai yada hotunan batsa.  Don haka suka ce in cire shi gaba daya, sannan in kore shi (Banning).
Da na hau na duba, tabbas abin ba dadi, wai mahaukaci ya ci kashi.  Sai na bi “Profile” dinsa, na ga lafiya kalau; babu bayanai masu nuna dan iska ne.  Ba ma wannan ba, dalibin ilimi ne na addini, kamar yadda bayanai suka nuna.  Da na hau farfajiyar shafinsa (Timeline), sai na ga ashe wata ce daga cikin abokansa, wacce aka gurbata shafinta sanadiyyar aikin dandatsanci, daga can aka samu damar shiga shafinsa shi ma.  Duk da haka dai dole tasa na cire shi baki daya, don kada ya gurbata shafukan sauran mambobin da ke zauren. Mafi girman matsala a yanayi irin wannan shi ne, hukumar Facebook na iya rufe shafinka gaba daya sanadiyyar wannan matsala, domin manhajarsu za ta rika nuna musu cewa, babu abin da kake yadawa a shafukan jama’a sai hotunan batsa, wanda kuma hakan ya saba wa ka’idojin mu’amala da ka rattafa hannu akai sa’adda kake rajistar shafinka.

Reful na Tikitin Jirgin Sama
A dandalin Facebook akwai shafuka na bogi masu dimbin yawa, kamar yadda bayanai suka tabbatar, kuma muka sha nanatawa.  Daga cikin ire-iren wadannan shafuka akwai wadanda ke dauke da tayi ga jama’a, cewa: duk wanda ya “So” (Like) ko “Yada” (Share) wani hoto ko bidiyo da aka turo, to, za a ba shi tikitin jirgin sama kyauta!  Wannan ya fi shahara ne a galibin kasashen Turai.  Sai dai dole mu fadaka mu ma, domin idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, sai ka nemi kogi ka yi alkafira a cikinta don jike naka gemun.
Tsarin “Like” da “Share” a Facebook suna da amfani sosai, kamar yadda kuma suke da matukar cutarwa, ga wanda bai iya mu’amala da su ba. Idan ka ga irin wadannan hotuna ko bidiyo ko bayanai masu dauke da irin wannan tayi na cewa, idan ka “Like” ko kayi “Share” din shafin, za a ba ka kyautar abu kaza, kada ka latsa.  Domin ire-iren wadannan shafuka da suke dauke da wannan tayi shafukan karya ne.  Watakila ka ce mini ai shafuka ne na kamfanonin jiragen sama sanannu, irin su: “British Airways” ko “KLM” ko “katar Airways” ko “Emirate Airways.”  Ko kuma, a daya bangaren, ka ga kamfanoni irin su: “Arik Air” ko “Chanchangi Airlines” ko “IRS Airlines” ko kuma “Azman Air,” a Najeriya ke nan.  Eh, sunayen kamfanoni ne da ake da su, amma shafukan da ke yin wannan tayin, shafukan bogi ne; ba shafukan hakikanin kamfanonin ba ne.  Masu wannan ta’ada mummuna suna gina shafin yanar sadarwa ne na musamman, mai dauke da bayanai iri daya sak, da na kamfanin da suke son kwafowa, sannan su hankado bayanan da suke son yaudarar jama’a da su dauke da adireshin wannan shafi na bogi.  Wannan tsari shi ake kira “Phishing” a fannin ilimin kariyar bayanai a zamanin yau.  Idan ka ga haka, kada ka matsa “Like” kuma kada ka yi “Share,” in kuwa ba haka ba, za ka gwammace kidi da karatu.  Ma’ana, da zarar ka matsa za a zarce da kai ne shafin can na bogi da aka tsara, sannan a bukaci bayanan katin asusunka na banki (ATM Card) da lambar wayarka da sauran bayanai masu mahimmanci a rayuwarka.  Kafin kasan me ke faruwa, aikin gama ya gama.  Watakila bayan karanta wannan bayani ka ce, “To ai yanzu na waye, zan matsa in je can shafin in ga abin da ke faruwa.”  Wannan kuskure ne mai girman gaske.  Domin ba ka da aminci a hakan ma, kana iya zuwa ka rudu da irin tsarin da suka yi amfani da shi na yaudara.  Ka sani, mai son kayanka ya fi ka dabara.  Jama’a, mu fadaka!
Karbar abokai barkatai
Dandalin abota irin na zamani kamar kasuwa ce, wadda a cikinta jama’a kan hadu daga ko’ina a duniya.  Wannan kasuwa dai tana da hanyar shiga da ta fita, sannan akwai ka’idojin mu’amala da hukumar kasuwar ta sa.  Amma me jama’a ke sayarwa, ko me suke tallatawa, ko me suke aiwatarwa a ciki, ko kuma mutanen kirki ne ko na banza a kasuwar, duk ba damuwar hukumar kasuwar ba ne, har sai an kai mata kara.  Illa dai tana da jami’an tsaro da ke shawagi a kasuwar, musamman daga kofar shiga ko kofar fita.  Wannan ya sa jabun mutane da jabun shafuka suka fi yawaita a gidajen yanar sadarwar sada zumunta na Intanet.  In kuwa haka ne, shin, mai karatu, ko ka taba zama ka lura da su waye kake mu’amala da su a shafukanka na sada zumunta?
Babbar manufar bude shafukan sada zumunta musamman na Facebook, shi ne don mutane da suka san junansu a gari guda, ko wata makaranta da suka taba yi, ko wani taro da suka taba haduwa na addini ko kasuwanci, su samu damar sake haduwa da juna don sadarwa da alakarsu ta ci gaba.  Amma ba a bude wadannan shafuka don yin mu’amala ko abota da mutumin da ba ka taba saninsa ba.  Amma haka lamarin yake a yanzu?  A a.
Idan ka yi rubutu a shafinka na Facebook misali, jama’a na iya ganin rubutun ta dayan dalilai hudu ne.  Abokanka (Friends) na iya gani, saboda a hankalce su ne amintattun mutane a gare ka.  Na biyu, abokanan abokanka (Friends of Friends) na iya gani, saboda amincin da ke tsakanin abokanka da su.  Na uku, duk wanda ya ci karo da shafinka a Facebook yana iya ganin abin da ka rubuta a farfajiyar shafinka (Timeline), idan ka bar tsarin a “Public” ke nan.  Sannan a karo na karshe, kana iya rubuta bayanai ka boye shi, a shafinka, ba tare da kowa ya iya gani ba sai kai kadai (Only Me).  Wadannan su ne tsare-tsare da suka shafi sirrin bayanai a Facebook, wadanda mai shafi ke rubutawa.  
A ka’ida idan ka bude sabon shafi a Facebook, babu wanda zai iya ganin bayanan da kake rubutawa a shafinka sai kai da abokanka kadai.  Sai idan ka canja wannan tsari.
Duk wannan dogon bayani dai ina so in jawo hankulanmu ne kan hadarin da ke tattare da abin da muke yi a Facebook musamman, ko Twitter, ko LinkedIn ta bangaren yada bayanai da wadanda ke iya isa ga bayananmu.
Daga cikin manyan matsalolin da ke jawo hasarar dukiya da mutunci a dandalin abota akwai yawan karbar abokai barkatai ba tare da tantancewa ba.  Tabbas ba abu ba ne mai yiwuwa a ce dole sai wanda ka sani a zahirin rayuwa kadai za ka yi abota da shi ba, amma kuma wannan ba lasisi bane wajen kabar kowane irin kwamacala da sunan aboki.  Masu neman abota da mutum a dandalin sada zumunci sun kasu kashi-kashi; akwai masu neman abota don karuwa da kai, musamman idan ka shahara wajen rubuce-rubuce masu fa’ida a addini da rayuwa.  Wannan daidai ne kuma yana da kyau.  Wannan ya fi shahara a bangaren malaman addini da siyasa da sauran fannonin ilimi.  Akwai masu nemanka da abota kawai don sun sanka a suna sanadiyyar shahara ko sun taba jin sunanka a wajen wasu amma basu taba ganinka ba.  Wannan, ta wata fuskar kuskure ne, musamman idan ba mutanen kwarai ba ne su, ko kai da ake nemanka da abotar ba mutumin kirki ba ne.  Wannan ya fi shahara a bangaren ‘yan fim, da marubuta littafan soyayya, da shahararrun ‘yan siyasa da ‘yan jarida.  
Har wa yau, akwai masu nemanka da abota saboda su samu damar kusantarka don wata manufa mummuna.  Wannan ya fi shahara a bangaren ‘yan dagaji, masu mugun nufi ke nan.  Suna kusantar ‘yan siyasa kamar yadda suke kusantar shahararrun mata da maza da ke wadannan wurare.  Akwai kuma masu nemanka da abota kawai don sun ga garinku daya, ko jiharku daya, ko kunyi makaranta daya – ko da ba tsararku  ba ne – ko kuma kuna da ra’ayin siyasa ko addini iri daya.  Akwai kuma masu nemanka da abota ba don komai ba sai don kyawun hoton da ka sa a shafinka, ko hotunanka da ya gani, ko irin nau’in sunanka.  Wannan ya fi shahara a bangaren mata, inda mazaje, musamman samari ke nemansu da abota saboda kyawun hoton da ke shafukansu ko sunayensu kawai, ba don wata karuwa mai fa’ida ba.  A karo na karshe kuma, akwai masu nemanka da abota don manufar kasuwanci.  Da zarar ka karbe su kawai za su yi ta jefo maka tallace-tallace a shafinka da sunan “Tagging.”
Duk wanda za ka karbe shi a matsayin aboki, dole ne kasan daga ina yake?  Idan ka taba saninsa, shin, mutumin kirki ne?  Idan ba ka taba saninsa ba, akwai alamar gyaruwa tare da shi?  Ta dalilin wa ya sanka?  Mutum nawa ne kuka hada a matsayin abokai tsakaninka da shi (Mutual Friends)?  In kun hada abokai, wasu iri ne?  Masu mutunci ne?  Wadanne irin hotuna ne a shafinsa?  Shin, hakikanin hotonsa ya sa?  In eh, a wace siffa yake?  In a’a, hoton meye a profile dinsa?  Akwai nau’ukan hotuna kusan 100 a Facebook, wadanda duk inda na gansu, na san jabun hotuna ne, kuma masu shafukan ba hakikaninsu ba ne, kuma dole dayan biyu; ko dai ya zama ‘yan madigo ne ko wani kato ne ya bude shafin da sunan mata.  Ka sani, irin yanayin abokanka irin yanayinka.  Masu iya magana na cewa, sai hali ya yi daidai ake abota.  Ana iya gane nagartarka ne da zamaninka, da kuma irin mutanen da ka zauna da su.  Shi ya sa, a tunani mai saiti na addini, babu wadanda suka kai Sahabban Annabawa nagarta bayan gushewar Annabawan.