Miyagun hanyoyin mu’amala a dandalin abota (4)

Bayani kan hanyoyin gane shafin gaskiya da na karya yana nan tafe. Barayin “Password” da “Hashtag”A baya mun yi magana kan yadda ake satar “Zati” da satar “Account.”  Abin da ke saukake hakan kuwa, shi ne, “Satar Password.”  Yadda ake satar “Password” haka kuma ake satar “Hashtag” a dandalin Twitter.  Kalmar “Hashtag” na nufin tambarin […]

Miyagun hanyoyin mu’amala a dandalin abota (4)
Miyagun hanyoyin mu’amala a dandalin abota (4)

Bayani kan hanyoyin gane shafin gaskiya da na karya yana nan tafe.

Barayin “Password” da “Hashtag”
A baya mun yi magana kan yadda ake satar “Zati” da satar “Account.”  Abin da ke saukake hakan kuwa, shi ne, “Satar Password.”  Yadda ake satar “Password” haka kuma ake satar “Hashtag” a dandalin Twitter.  Kalmar “Hashtag” na nufin tambarin da ake amfani da shi ne wajen yada sako a shafin Twitter.  Duk da cewa daga baya shafuka irin su: Google+ da Instagram da kuma Facebook sun fara amfani da shi.  Amma shafin Twitter ne yafi shahara da wannan tsari mai fa’ida matuka.  Ga yadda hashtag yake wajen siffa: #ZamanLafiyaMukeSo.  Ma’ana za ka ga rubutu ne mai dauke da tambarin hash (#) a farkonsa, kuma kalmomin a hade suke, babu tazara tsakaninsu.  Kuma a launin shudi yake bayyana.  Wannan, a takaice, shi ake kira “Hashtag.”
Yadda ake satan “Password” (Password Theft) haka dai kuma ake satar “Hashtag” a dandalin sada zumunta.   Me ake nufi da satar “Hashtag”?  Shi ne, bayan ka samar da hashtag dinka kana yadawa ta hanyar abokanka a shafinka ko nasu, sai a samu wani ko wasu su rika amfani da hashtag din, irinsa sak, amma dauke da wani sako wanda ko kusa ba shi da alaka da sakonka.  Wasu kan yi haka ne don kokarin batar da sakon da mai hashtag din ke son isarwa; ko don suna adawa da sakonsa, amma sun kasa bice haskensa ta wata hanya, ko kuma don kokarin neman shahara sanadiyyar saharar mai hashtag din.   Wannan tsari shi ake kira “Hashtag Hijacking.”  Kuma yana cikin abubuwan da suke kan yaduwa a shafuka irin su Twitter da Google+ da sauransu.  Daga cikin shahararrun Satar Hashtag akwai wanda kungiyar ISIS ta yi, sa’adda take kan ganiyar ta’addancinta a lardunan da ta mamaye tsakanin kasar Iraki da Siriya.  Akwai kungiyar rajin kare hakkin mata da ke kasashen Gabas-ta-Tsakiya da suka bude shafuka a dandalin Twitter, suna ta Allah-wadai da abin da suka kira take takkin mata ne.  Ana cikin haka sai wannan kungiya ta sace Hashtag din gaba daya, ta juyar da zancen zuwa wani batu daban.  Da zarar mutane sun nemi Hashtag din za su samu, amma kuma sai su ga wani zance ne da ba shi da alaka da abin da Hashtag din ke batu a kai.  A haka wannan kurkuruwar su ta narke.
Satar “Password” kuma, a daya bangaren, ruwan dare ne a dandalin abota.  Idan masu karatu ba su mance ba, a doguwar kasidar mu mai taken: “Tsarin Mu’amala da Password,” wadda ya zuwa yanzu mun rubuta shafuka 37 ne, na kawo bayanai kan asali da samuwar “Password,” da tsarin mu’amala da “Password,” sannan da hanyoyin da jama’a ke bi wajen zaben “Password” dinsu.  A wannan gaba ne na nusar damu irin sakacin da muke yi ko dai wajen zaben “Password” ko wajen killace ta da tsare ta daga idanun barayi.
A kullum sai an samu wani mai shafi a dandalin abota da aka sace “Password” dinsa; da saninsa ko ba da saninsa.  A kullum sai an samu masu shafuka a dandalin sada zumunta da ake sace “Password” dinsu, da saninsu ko ba da saninsu ba.  
A wani bincike na musamman da ya gudanar, Farfesa Olu Idris, wani kwararren masani a fannin kimiyya da fasahar sadarwa ta zamani ya gano musabbaban wannan matsala.  A karshe ya gano cewa, galibin masu mu’amala a shafukan sada zumunta na amfani da lambobin wayarsu ne a matsayin “Password”.  Wadanda aka fi sace “Password” dinsu cikin sauki su ne mata.  Ya kuma gano cewa, ta hanyar wadannan kafafen sada zumunta, galibin mutane, musamman ma mata, kan bayyana sirrinsu cikin hira da kake yi da su ba tare da sun ma fadaka ba.  Har wa yau, sanadiyyar sakaci, da yawa cikin mutane kan amince wa wadanda ba su ma taba saninsu ba balle hakikaninsu, su kuma ba su bayanai masu hadari ga rayuwarsu.  Labarin bai kare ba.  
Ya ce idan ka shiga shafukan sada zumunta gaba dayansu, kana iya ganin “Password” din jama’a ta ko ina; tsakanin sunayensu, da lambobin waya da suke sakawa a shafukansu, da alkunya ko lakubbansu, da rubutun da ke kan hoton profile dinsu, da nau’ukan bayanan da ke profile dinsu.  Duk, a cewar Farfesa Olu, idan ka bi wadannan bayanai da ke fili a shafukan jama’a, za ka samu da yawa cikinsu duk “Password” ne.  Wannan, a cewar Farfesan, kuskure ne.  Domin kalmar “Password” wajibi ne ta zama sirri ga kowa idan ba kai ba.  In kuwa haka ne, bai kamata a ce kalmar ko kalmomin da kake amfani da su a matsayin “Password” suna cikin bayanan da za a iya gani a Profile dinka ba, duk da cewa ba wanda ya san me kake nufi da su.

Mai Gida, Ina Matarka?
Daga cikin abin da ya fi tayar da hankali cikin munanan tasirin hanyoyin sada zumunta na zamani sanadiyyar rashin tarbiyya, akwai irin matsalar da matanmu na aure, Hausawa musamman suka samu kansu a ciki, musamman a dandalin Facebook.  Tabbas akwai matan aure da yawa a Facebook masu mutunci, masu yada ilimi na addini a zauruka da dama, masu nasiha ga ‘yan mata ‘yan bana-bakwai don kada su fada cikin tarkon shaidan a wannan dandali.  Wannan abu yana burgeni matuka, domin suna rage wa malaman addini aiki ne a zahirin rayuwa, musamman a Arewacin Najeriya.  Ayyukansu na tasiri sosai, domin suna amfani da irin lafazin da ‘yan matan ke iya fahimta ne, cikin sauki kuma.  Ina rokon Allah ya kara musu karfin gwiwa, da karin hakuri da juriya, wajen kara inganta wannan aiki nasu mai tasiri.
A daya bangaren kuma, akwai watsattsu, marasa mutunci, wadanda suka fitsara har suka fitsare wasu; tsakanin matan aure da zawarawa.  A yau an wayi gari yadda saurayi da budurwa ke kulla alaka ta soyayya, ai ta abubuwa marasa tsafta, haka matan aure ke kulla alakar soyayya irin na madigo, wanda ke farawa tun daga Facebook. Galibi sukan hadu ne a zaurukansu (Groups), inda ake tattaunawa.  Akwai kawalai mata masu hada waya.  Idan ke Hajiya ce kina son wata mace da za ku rika haduwa kuna soyayya irin ta madigo, akwai mai hadawa, duk ta wadannan zauruka.  Abin mamaki shi ne, asalin ire-iren wadannan zauruka an bude su ne don kulla zumunci tsakanin mata; za ka ga sakonni na wa’azi da nasiha, amma a cikin zauren ake samun juna.  Daga nan sai a koma Inbod a ta hirar shashanci.  Daga nan a rika hira a waya, musamman idan maigida ba ya gari.  Wata kan yi “chat” har zuwa karfe biyun dare da “masoyiyarta.”  Idan abin ya kasaita, suna ziyartar juna, ko da ba gari daya suke ba.  A wajen ziyarar ma a kwanta tare, a daki daya, a kan gado daya, ana ta shashanci, musamman idan maigida ba mazaunin gari ba ne.
Wasu matan auren kuma suna neman ‘yan mata ne, ‘yan makaranta, musamman ‘yan jami’a, su rika shashanci da su ta kafar Facebook, a karshe a kulla alakar ziyara, musamman lokacin da Uba ke tsammanin ‘yarsa na makaranta.  Akwai wacce ta shaku da wata bazawara tun a Facebook, suna gaisawa, aka fara shashanci a Inbod.  A karshe dai wannan budurwa ta kai mata ziyara, sai da tayi makonni shida a gidan wannan bazawara mai hali suna shashanci.  Akwai matan auren da ke abin a waya da Facebook kadai, amma a zahiri ba su haduwa.  Akwai wacce ba ta da sana’a sai neman ‘yan mata, kuma matar aure ce.  Idan ta samu wacce take so ta kafar Facebook, sai ta bukaci budurwar ta kawo mata ziyara, ita kuma ta kama Otal su kwana suna shashanci.  Mijinta ba mazaunin gida ba ne, a kudu yake aiki , ita kuma ya barta nan Arewa da yara.  Idan ma ta bukaci abokiyar shashanci, amma tace ba ta da kudin mota, tana iya tura mata kudi ta banki, ita dai bukatarta a hadu; kudi ba damuwarta ba ne.
Akwai matar auren da ta rantse wa abokiyar shashancinta, cewa wallahi tallahi tunda take da mijinta (tsawon shekaru 4), ba ta taba sanin meye sha’awa ba, kuma ba ya burgeta, ba ta ma sha’awarsa.  Ba ta san dadin sha’awa ba sai da ta hadu da abokiyar shashancinta.  Akwai matar auren da saboda shakuwa da irin wannan shashanci ya haddasa musu, idan daya ta yi fushi da daya, to, komai na gidan na iya shiriricewa.  Ta gwammace mijinta ya yi fushi da ita da a ce masoyiyarta ce.  Akwai wacce take gaya wa wata kawarta, cewa, mijinta ya taba kama ta da wata masoyiyarta, a kan gadonta, a dakinta, suna shashanci; a tube zindir dukkansu.  Da ya leka ya gansu, sai kawai ya koma falo, ya ce idan sun gama ta sanar da shi.  Da kawar ta tambayeta: “To ya ya aka kare?”  Sai ta ce wallahi ba abin da ya faru.  
Ire-iren wadannan mata asharararru sukan tona asiran mazajensu wajen kwanciya ga kawayensu na shashanci.  Akwai wacce da zarar mijinta ya gama saduwa da ita nan take za ta hau Facebook ta sanar da masoyiyarta, da irin tsarin da aka bi wajen aiwatar da abin.  Wadannan masu shashanci da mata ‘yan uwansu ke nan; ko dai zawarawa ko ‘yan mata ‘yan jami’a ko kuma kawayensu matan aure.
A dya bangaren kuma, akwai matan aure da ke haduwa da mazaje ta wadannan kafafe na sadarwa; ko dai tsofaffin samarinsu lokacin samartaka, ko kuma wasu da suka hadu da su.  Sukan kulla alaka da su sosai, ta hirar batsa, da aika hotuna, idan abin ya kasaita, akan hadu a waje (ko Otal ko wani wuri daban) don ya sadu da ita.  Wannan shi ya fi komai sauki ma, wai cire wando ta ka.  Akwai wanda ya hadu da wata matar aure ta Facebook, tana cikin kunci, kamar yadda ta sanar da shi, ba ta son mijinta ko kadan, kuma ita tana da karfin sha’awa, shi kuma yakan fita waje shashancinsa.  A karshe wannan saurayi wanda ko aure bai taba yi ba, ya gayyaceta wani gida a garin da suke, ya sadu da ita.  Akwai wanda duk sa’adda ya bukaci kwanciya da wata tsohuwar budurwarsa da ke da aure yanzu, bayan shashancin da suke yi ta waya da Facebook, sukan hadu a wani wuri ya sadu da ita.  Da aurenta har da yara.  
Wadannan labarai ne masu tayar da hankali, kuma tabbatattu.  Babbar manufar ita ce mu fahimci irin hadari da kuma mummunan tasirin da rashin tarbiyya ke haddasawa ga masu mu’amala da wadannan kafafen sadarwa.  Maigida, har wa yau kai nake tambaya: wai ina matarka take?