Miyagun hanyoyin mu’amala a dandalin abota (5)
“Mu Hadu a Whatsapp, Ya Fi Sirri!” Wannan shi ne galibin zancen samari da ‘yan mata idan suna son su fara hirar batsa ko aika wa juna hotunan batsa, yayin da suke hira ta Inbod a Facebook. Tsakanin Facebook da Whatsapp, kashi 70 cikin 100 na hirar samari da ‘yan mata duk ta batsa ce. […]
“Mu Hadu a Whatsapp, Ya Fi Sirri!”
Wannan shi ne galibin zancen samari da ‘yan mata idan suna son su fara hirar batsa ko aika wa juna hotunan batsa, yayin da suke hira ta Inbod a Facebook. Tsakanin Facebook da Whatsapp, kashi 70 cikin 100 na hirar samari da ‘yan mata duk ta batsa ce. Bayan hirar saurayi da budurwa a killace, akwai zauruka birjik a Whatsapp na mata zalla, ‘yan mata ke nan, da na maza zalla, samari ke nan, da na cakuden maza da mata marasa aure, da matan aure zalla, da na cakuden matan aure da zawarawa. A wasu lokuta akan samu budurwa daya ko biyu a zauren matan aure zalla, idan suna da uwa a gindin murhu ke nan. Akwai wata baiwar Allah da ta sanar da ni watanni biyu da suka gabata cewa, akwai wani zaure a Whatsapp da take ciki, ita kadai ce budurwa, duk sauran matan aure ne. Amma irin zantuttuka da hotuna da bidiyo da ake rabawa a zauren, a cewarta, baki ba zai iya fadarsu ba. Ba wannan kadai ba, ta ce hatta hirar mazajensu suna yi; labarai iri-iri. Da yanayin kwanciyar da aka yi da su da irin wadda suke so. Kai, zancen sai wanda ya ji.
Duk da cewa da manhajar “Whatsapp” da “Instagram” da kuma “Facebook” duk na kamfanin Facebook ne, amma ga alama manhajar Whatsapp tana rage wa sauran biyun tagomashi, wajen yawan jama’a da yawan masu hawa. Mene ne dalili? Saboda “Sirri”, kamar yadda samari da ‘yan mata ke fada. Wannan sirri da suke kira, idan ka duba duk za ka ga akwai shi a Instagram da Facebook Chat Application ma, to amma a ma’anance suna nufin saukin mu’amala ne, wajen karbar hotuna da bidiyo. In ba haka ba, ai kashi 90 cikin 100 na mutanenmu na amfani da wadannan manhajoji ne ta wayar salula. Tabbas in an kwatanta da Facebook, Whatsapp ya fi sirri, domin idan ka yi rubutu a shafinka a facebook duk abokanka na iya gani har su yi tsokaci. Haka zaurukan Facebook ma suke. To amma in haka ne, bai ma kamata a kwatanta biyun ba wajen sirri, domin ba yanayinsu daya ba. Wannan sharhi ni ne kawai nake yinsa, amma su a wajensu sun gane abin da suke nufi.
Galibin abin da ya fi yaduwa a wayoyin salularmu, musamman matasa, shi ne, hotuna da bidiyo na batsa. Ina maimaita wannan zance ne saboda tabbaci; halin da muka samu kanmu a ciki ke nan. Akwai zaurukan addini da yawa, birjik, amma abin da mutane ke yi ta bayan fage yana warware abin da suke fada ko tutiyar koyi da shi a zaurukan da suke ciki na addini ne.
Kamar yadda ake da matan aure da zawarawa masu yada tsiya a Whatsapp, haka ake da samari da ‘yan mata (maza da mata) da matasa maza masu aure, kai har da tsofaffi masu yada ashararanci ta manhajar Whatsapp. Domin galibin zaurukan da ke Whatsapp, asalinsu daga Facebook ne. Haka ma galibin kawancen da ke tsakanin jama’a a Whatsapp, duk asalinsa daga Facebook ne. Bayan haka, da yawa cikin masu amfani da manhajar Whatsapp suna amfani da Facebook ne kawai wajen neman abokan hira a Whatsapp, ta hanyar karbar lambobin wayarsu da suke amfani da ita wajen Whatsapp din. Sauran bayani kuma sai an hadu a can.
Mata-Maza ‘Yan Damfara
Daga cikin manyan rudu da ke makare a dandalin sada zumunta na zamanin yau akwai rashin hakikanin manufofin wadanda muke tare da su a matsayin abokai. Tabbas, idan abokanka galibi wadanda ka sani ne a zahiri, wannan matsalarka ragaggiya ce. Amma idan kashi 70 cikin 100 na abokanka a nan ka hadu da su, to, dole ne ka yi taka-tsantsan.
A nan ba cewa nake ka rika tuhumar duk wadanda ba ka sansu a zahirin rayuwa ba, ko kuma munana musu zato, a a. Amma dai ka tsaya a iya haddin alakar da kake tunanin ita ce asalin mahadinku. Wannan ba wai ga abokanka maza kadai ba, hatta mata – duk daya ne, wai makaho ya yi dare a kasuwa. Yadda ake samun mazambata cikin maza haka ake samun mazambata cikin mata, sosai ma kuwa. Wasu kuma mata-maza ne, ma’ana mata ne amma a siffar maza, ko maza ne, amma a siffar mata. Kuma ‘yan damfara.
Akwai wadanda ke bude shafi da sunan mata, kuma mata ne, amma manufarsu kawai ita ce nemo wa wasu mazajen wadanda za su yi maashaa’a da su. Wadannan kawalai mata ke nan. Akwai kuma kawalai maza, da sunan maza sosai. Sannan akwai wadanda maza ne su, amma sai su bude shafi da sunan mace, su rika tallar kansu a matsayin wani namijin ne daban, ga mata. Idan mace ta nuna tana so, sai su bata lambar wayarsu. Da zarar ta kira sai ya dauka, daman an gaya mata cewa namiji ne, ba matsala ke nan. Galibi wadannan sun fi yawa a zaurukan Facebook, saboda nan ne aka fi haduwa kuma kana iya ganin “Profile” din mutum warewake, inji Zage-zagi.
Akwai wanda ya bude shafi da sunan mace, yana hira da mata. Kashi 90 cikin 100 na abokansa mata ne. Hira yake da su, a matsayin mace ne shi. Ya ce musu sha’awa na damunsa, amma ya samu wani gaye da ke debe masa kewa wajen “sed chat” (hirar batsa don kawar da sha’awa), idan suna so zai iya hada su dashi. Da zarar sun amince sai ya tura musu lambar wayarsa, daman yana da lambobi kusan 5 daban-daban, kuma yana da wani shafi daban mai sunan namiji. Haka ya rika yi wa ‘yan mata da yawa da na sani, har a karshe Allah ya kawo karshen wannan shashanci nasa. Akwai kuma wanda ya bude shafi da sunan mace, yana neman abokai mata zalla. Da zarar an karbi abotarsa, sai ya turo sako tun fari, ya ce:
“Hajiya ki gafarceni, ni namiji ne, wanda ke debe wa manyan mata sha’awa da zawarawa, ta hanyar sed chat in suna so. Idan kina so to, amma in baki so, don Allah ki yi blocking dina kawai. Ba zagi. Na gode.”
Wata ‘yar uwa ta nuna mini irin wannan sako, da na bibiyi wannan tantiri, sai na ga namijin ne kamar yadda ya fada. Da yawa cikin mata sun rudu da shi, yana ta shashanci da su. Kuma bayan wannan shafi ma, yana da wani shafi da wata lambar wayar daban. Allah Ya kiyashe mu shashanci irin wannan. Wannan bangaren masu boye fuskokinsu ke nan da niyyar maashaa’a.