Miyagun kwayoyi: Illolin Da Suke Haifarwa Ga Al’umma
A yau kuma MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta yi tsokaci ne game da illolin da tu’ammali da miyagun kwayoyi ke haifarwa ga al’umma. Ga abin da take cewa: Kowa ya san tabarbarewar tarbiya da shaye-shayen miyagun kwayoyi sun zama ruwan dare game duniya a wannan zamani namu, musamman a kasashe masu tasowa irin namu […]
A yau kuma MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta yi tsokaci ne game da illolin da tu’ammali da miyagun kwayoyi ke haifarwa ga al’umma. Ga abin da take cewa:
Kowa ya san tabarbarewar tarbiya da shaye-shayen miyagun kwayoyi sun zama ruwan dare game duniya a wannan zamani namu, musamman a kasashe masu tasowa irin namu na Afirika. Amma fa ba wai don ya zama abin so da kauna ba ne, a’a, abu ne da ya saba wa dokokin mafi yawan kasashen da ake aiwatar da su.
Mu dauki misali da tamu kasa Najeriya, me ya sa shaye-shaye ya zama abin so da yayi a tsakanin jama’ar kasarmu, alhalin dokar kasarmu ma ba ta yarda da hakan ba? Mu dai a namu ganin, muna ganin kamar matsalar ta samo asali ce daga sakacin bangarori uku, wato iyaye, hukuma da kuma su kansu masu shaye-shayen.
Dalilin da ya sa muke ganin kamar akwai sakacin iyaye a cikin tabarbarewar tarbiya da yawaitar ta’ammali da miyagun kwayoyin a cikin al’ummarmu shi ne, iyaye ne ke da alhakin kula da tarbiyyar al’umma ta fuskar ba da reno da tarbiyya mai kyau, ba da kariya da kuma bin duk wata hanya don inganta rayuwar yara, tun daga kuruciya har zuwa girma. Gaskiya wasu iyaye ba su da wani takamaiman tsari tsararre da suke bi don ganin sun samar da reno da tarbiya ingantattu ga yaransu. Haihuwar kawai ake yi ba tare da samar da wani cikakken tsarin kula da tarbiyyar yara ba. Yanzu iyaye sun daina janyo yaransu a jika ta yadda za su cusa musu tarbiyya da halaye na kwarai a zukatansu. Sai ka ga iyaye ba su kula da su san su waye abokai ko kawayen ’ya’yansu ba, ba su damu da ina ne wurin wasa, hira ko yawon ’ya’yansu ba. Idan dai aka yi kokari aka ga an sa yaro a makaranta shi ke nan an gama mai wuyar. Kowace irin dabi’a zai koya daga malaman ko daga sauran daliban makarantar, to bai zama abin sa ido ko kula daga iyayensa ba. Kuma mafi yawa irin wannan sakacin ne ke sa yaro ke afkawa cikin muguwar tarbiyyar miyagun abokansa saboda ba a gina masa katangar tarbiyya da za ta kare shi daga kowace muguwar dabi’a ba. Kai tsaye komi ya taba zuciyarsa, nan da nan sai ya yi tasiri a ransa. Daga nan idan ya yi rashin nasarar haduwa da mashayan abokai, kafin a ankara sun koya masa har ya dulmaya kuma raba shi da su abu ne mai matukar wuya. Dalilin shi ne kuwa saboda da su ya shaku ba da iyayensa ba.
To gaskiya mu sani, wannan sakaci ne babba, a takaice dai wannan shi ake kira da tabarbarewar tarbiyya. Abin da ya kamata mu iyaye mu yi shi ne, daga zarar yaro ya fara girma da wayau, sai mu jawo shi a jiki, mu rika yawan mu’amala da shi, kamar cin abinci, kai shi makaranta, zuwa masallaci ko yin Sallah tare da shi, kallo ko sauraren rediyo da talabijin da shi, taya shi aikin makarata, da dai sauran duk wasu mu’amalolin rayuwa da ya shafe shi. To daga nan ne za mu iya gina wa zuciya da kwakwalwarsa dukkan wani tsarin ginin da muke bukatar rayuwarsa ta tsayu a cikinsa. Ta nan ne za mu iya ba rayuwarsa dukkan wata kariya daga abin da muke jin tsoron ya faru da ita.
Amma ina, yanzu iyaye ba kowa ne keda lokacin rayuwar dansa ba, hidindimun neman abinci da son mulki da kwadayin jin dadin duniya sun rufe mana ido, ta yadda har ba mu iya gane cewa mun afka wani sakacin da zai wanzar mana da tashin hankalin rayuwa. Domin da zarar rayuwar danka ta lalace, wallahi ba ka sake jin dadin duk wani abin da kake yi wa fafutuka. Ko abin da ka tara, daga lokacin da dukkan tunanin ka ya koma a kan ta yaya za ka ga ka ceto rayuwar danka ka dawo da ita kan hanya. Don haka mu dai muke ganin da sabon gini gwamma yabe. Geza tun tana danyarta ake lankwasa ta.
Har wa yau muna ganin kamar ita ma hukuma akwai nata sakacin da take nuna wa al’ummarta, da ya janyo lalacewar tarbiyya dad a har tu’ammali da miyagun kwayoyi ya yawaita a kasarmu. Yanzu hukuma ta tsame hannunta daga cikin kula da tarbiyyar al’umma, ta kawo na mujiya ta sa mana; kowa tasa ta fisshe shi, kowa abin da ya ga dama shi yake yi wa kansa ko iyalinsa ko ma jama’arsa. Ba wani tsarin yaki da rashin tarbiyya da hukuma ke yi. A inda ma ta yi kokari ta kafa hukuma a kan yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi, kalubalen tabbatar da doka da oda da ya addabi hukumomin kasarmu ya sa da yawan dokokin hukumar ba su da wani tasiri. Hakan kuwa shi ya samar da yawaitar safarar kwayoyi da noman miyagun ganye, har ta kai ga dillancin su ya zama abin kawo kudi da arziki nan da nan cikin dare daya a wurin wasu bara-gurbin ’yan kasa.
Yanzu ina amfanin a ce babbar kasa kamar Najeriya mai arzikin yawan mutane da arzikin karkashin kasa da na koguna a ce ga jama’arta nan kara-zube, shuwagabanninmu suna kallon dillallan miyagun kwayoyi suna cin karensu ba babbaka, suna ta gurbata tunani da hankalin matasanmu, ana ta kashe mana makomar kasarmu da ta jama’armu ta hanyar cinikayyar miyagun kwayoyi, tun da dai kowa ya san irin illar da shaye-shayen miyagun kwayoyi yake haddasa wa mai yin sa da kuma koma bayan da yake janyo wa al’ummar da take dauke da masu yinsa.
Magana ta gaskiya, shuwagabanninmu ya kamata su duba baya, su tausaya wa mabiyansu, su nura da irin illar da shaye-shaye da rashin tarbiyya sukke janyo wa kasarmu. Kuma su sa tabaron hangen nesa, su tsinkayi irin bakar makomar da kasa da jam’armu ke fuskanta,ta dalilinsa.
Ya zama dole su ma matasan da suka maida shaye-shaye dabi’a, mu nuna musu damuwarmu a kansu, ganin cewar dakkansu ’yan uwanmu ne. Daga ’ya’yanmu sai kanne da yayyenmu ne su. Ta yaya ba za mu ji haushi da takaici ba? Ka daga kai ka kalli naka a buge cikin yanayin maye, ba ya iya tunanin amfanar wa kansa komai na ci gaban kansa ko na waninsa. Lafiyarsa ma tana cikin halin tsaka mai wuya, dukkan rayuwarsa ta zama a hargitse, ba natsuwa, ba fasali, ba tsari ko daya.
Abin haushin ma shi ne, mugayen dabi’un da shaye-shayen yake jefa wasu, irin su tsageranci, sace-sace da sauran su, domin wasu yanayin yakan sa su su rika satar kayan wasu don su sayi kayan maye. Wasu kuwa da suke nema sai ka ga ba su iya amfana wa kansu da komi cikin neman nasu sai dai su sha su bugu. To ina amfanin hakan? Me ya sa mashayi ba zai zauna ya yi tunani, shin da me ya amfana a lokacin da ya dauka yana shan miyagun kwayoyin? Na tabbata amsarka za ta zama babu. To idan ba ka daina yanzu ba sai yaushe? Haka za ka yi ta rayuwa har mutuwarka a lalace? To ka sani dainawar ita ce alheri a gare ka, domin ta haka ne kawai za ka samu damar zama mutumin kwarai, ta yadda za ka ji dadin rayuwarka. Inda za ka gane da hakan shi ne, ka yi kallo da idanun basira ka gani, lallai duk inda ka ga tsohon kwarai, to daga yaron kwarai ya faro kuma duk inda ka ga tsohon banza to yaron banza ya samar da shi.
Daga karshe muna rokon Allah Ya shirye mu, Ya ganar da mu da matasanmu su gane illolin shaye-shaye da rashin tarbiyyar ke haifarwa, su daina, amin.