‘Miyagun kwayoyi ne ke haifar da ayyukan badala’
An tunatar da dalibai kan illar da tu’ammali da kwayoyi ke haifarwa musamman lalata rayuwa ta zamo mara ramfani. Jami’ar Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Dokta Fatima Popoola ce ta bayyana haka a wurin taron fadakarwa da aka shirya wa daliban makarantun sakandare a Shiyyar Zariya da ya gudana a Makarantar ’Yan […]
An tunatar da dalibai kan illar da tu’ammali da kwayoyi ke haifarwa musamman lalata rayuwa ta zamo mara ramfani.
Jami’ar Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Dokta Fatima Popoola ce ta bayyana haka a wurin taron fadakarwa da aka shirya wa daliban makarantun sakandare a Shiyyar Zariya da ya gudana a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Kofar Gayan a Zariya
Dokta Fatima Popoola ta ce, akwai matukar damuwa kan yadda matasa da yara suke mu’amala da miyagun kwayoyi don cimma buri marar amfani a gare su da kuma al’ummarsu.
Ta ce, ya zama wajibi iyaye da al’umma su hada hannu da malamai da hukumomin da ke yaki da tauammali da miyagun kwayoyi domin ceto rayuwar matasa daga lalacewa.
Jami’ar ta kara da cewa, ba zai yiwu iyaye su zura ido ga ’ya’yansu kawai don soyayya har yaran su lalace su kuma fitini al’umma ba.
Dokta Fatima ta ce shaye-shayen miyagun kwayoyi na jefa matasa cikin ayyukan badala da suka hada da satar mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da kashe- kashen rayuka babu dalili da sauran ayyukan assha.
A jawabin jagoran taron kuma Shugaban Kungiyar Tabbatar da Zaman Lafiya a Najeriya (Adbocates for Biolence Free Society and Peaceful Coedistence Initiatibe Nigeria) wadda ta shirya taron, Malam Sani A-Kama-Kasa, wanda shi ne ya assasa kungiyar, ya ce wannan aiki da ya dauka ba wanda ya kallafa masa kuma yana yi ne da dan kudin fanshon da ake biyansa. Ya ce sai da ya nemi izini daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna saboda shirin ya shafi dalibai.
A cewarsa, Ma’aikatar Ilimi ta amince ya gudanar da taron a makarantunta 541 a fadin jihar.