Miyar gargajiya
Assalamu alaikum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar gargajiya. Na sanya mata suna ‘miyar gargajiya’ saboda irin ababen da na yi amfani da su a lokacin da nake hada miyar. Yana da kyau a matsayinki na mace watarana ki shiga dakin girki domin gwada […]
Assalamu alaikum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar gargajiya. Na sanya mata suna ‘miyar gargajiya’ saboda irin ababen da na yi amfani da su a lokacin da nake hada miyar. Yana da kyau a matsayinki na mace watarana ki shiga dakin girki domin gwada wata irin miya ko abinci wadda za ki ga ke kadai kika san da ita sannan miyar ta samu dandano wadda sai a gidanki kadai maigida yake iya samun irin wannan miyar. A yau na kawo muku irin tawa hadin kuma na sanya mata suna miyar gargajiya. A sha karatu lafiya.
Abubuwan da za a bukata
• Kifin karfasa
• ‘shrimps’
•Kifin ‘cray fish’
• Gwaza guda uku kanana
• Albasa
• Attarugu
• Man ja
• Magi
• Kori
• Ganyen kori
Hadi
A dora ruwa a wuta sannan a zuba gwaza a ciki kada a bare bawonta sannan a jira ta nuna sosai sannan a bare sai a ajiye a gefe. Bayan haka sai a wanke kifin karfasa sannan a yayyanka kamar gida uku. A markada kifin ‘crayfish’ da attarugu sannan a zuba akan kifin sannan a soya man ja da albasa sai a rage wutar sannan a zuba kifin su dan soyu sannan a zuba jajjagen attarugun a ciki da magi da kayan kamshi sannan a zuba ruwa kadan dai-dai yadda zai dafa kifin sannan a rufe tukunyar.
Bayan kifin ya nuna sai a zuba ‘shrimps’ din sai a tsame kifin kamin a zuba ‘shimps’sannan sai a kara ruwa kadan a rufe har sai ya nuna sannan a cire shi a tukunyar sai a bare gwazan a farfasa ko a dan jajjaga yadda zai yi laushi sannan a zuba a tukunyar domin miyar ta yi kauri. Za a iya saka magi idan bai ji ba.
A dauko wannan dafaffen kifin a zuba hade da ‘shrimps’ da ganyen kori domin su dan tafasa na minti biyu sannan a sauke tukunyar a wuta.
Za a iya cin wannan miyar da sakwara ko tuwon shinkafa. A ci dadi lafiya.