Miyar kubewa danya
Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan alheri, kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar miyar kubewa danya. Mutane da dama na da irin nasu nau’in girka wannan miyar, don haka na kawo muku irin yadda mu kuma muke girka namu girkin domin canza dandano wa maigida. Yawan samun […]
Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan alheri, kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar miyar kubewa danya. Mutane da dama na da irin nasu nau’in girka wannan miyar, don haka na kawo muku irin yadda mu kuma muke girka namu girkin domin canza dandano wa maigida. Yawan samun dandano iri daya a girki na da fitan rai domin yana ginsar mutane. Yana da kyau a koyi salo daban-daban na girka wannan miyar. A sharba lafiya.
Abubuwan da za’a bukata
• Kubewa
•Busashen kifi
• Kanwa
• Attarugu
• Albasa
• Magi
•Nama
•Tafarnuwa
• Man ja.
Hadi
Da farko dai wannan miyar ana yinta ne a talauce. Domin idan kayan hadi ya yi yawa, miyar ba ta cika yin dadi ba. A wanke kubewa sannan a kankare a na’urar kankare kubewa ko kuma a yayyanka, sannan a zuba a turmi a daka, tare da kanwa kadan har sai kubewar ta yi laushi sosai sannan a kwashe a ajiye a kwano daban. Bayan haka a zuba ruwan zafi a busashen kifi sannan a cire kaya a wanke ya fita sosai. A yayyanka albasa sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.
A zuba ruwa a tukunya a silala nama da gishiri da albasa. Bayan nama ta yi laushi sannan a kara ruwa kadan a zuba kifin da jajjagen attarugu da tafarnuwa da albasa ya yi ta tafasa har sai kifin ya nuna sannan a dauko wannan jajjagen kubewar da kanwa a zuba a cikin ruwan. Haka za a yi ta juyawa har sai kubewar ta fara nuna sannan a daka magi iya adadin da ake bukata a zuba. Sannan a ci gaba da juyawa har sai magin ya narke a miyar sannan a sauke.
Za a iya shan wannan miyar da tuwon masara ko tuwon semo da tuwon shinkafa.