Miyatti Allah ta gano shanun sata a Legas
Shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Miyyati Allah sun yi nasarar kame shanun sata a kasuwar shanu ta Abbatuwa da ke garin Agege, Legas. A cewar shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Muhammadu Juba Hardon Zuru a kwanakin baya ma kungiyar tasu a ta yi nasarar kame wasu shanu guda 29 da aka sato su daga Safana […]
Shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Miyyati Allah sun yi nasarar kame shanun sata a kasuwar shanu ta Abbatuwa da ke garin Agege, Legas.
A cewar shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Muhammadu Juba Hardon Zuru a kwanakin baya ma kungiyar tasu a ta yi nasarar kame wasu shanu guda 29 da aka sato su daga Safana ta Jihar Katsina zuwa Legas, inda bayan an gano su kungiyar ta hada kai da jami’an tsaro da Gwmnatin Jihar Katsina, aka mayar wa masu shanun, aka kuma dau kwararan matakai a kan masu hannu a harkallar.
“Sai ga shi an sato wasu shanun guda 60 daga Zariya, a inda aka kawo 38 nan Legas. Ana sauke su da kimanin minti 30, sai ga wasu 22 su ma an kawo su daga Jihar Zamfara. Hakan ne ya sa na garzayo da kaina na zo Legas, a yanzu bincike ya yi nisa mutanen da ake zargi da kawo shanun satar mun mika su a hannun ’yan sanda kana mun tura a mayar da shanun daga inda aka sato su,” inji Hardon Zuru, wanda ya kara da cewa shanun da aka sato daga Jihar Zamfara an yi hayar wani mutum da aka ba shi takardar shaida cewa shanun na gado ne amma da suka tsananta bincike sai suka gano abin ba haka ba ne, kuma shi mutumin da kansa ya tabbatar da cewa hayarsa aka dauko, aka ba shi wannan takardar domin ya ce shanun na gadonsu ne.
A karshen ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ganin kwararan matakan da ya dauka a lokacin da aka gano wadanda ke da hannu a harkallar shanun da aka sato daga garin Safana.
Shugaban kungiyar direbobin manyan motoci reshen Abbatuwa a Legas, Alhaji Muhammadu Bello Jibrin ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu sun shirya tsaf don magance matsalar dauko shanun sata da direbobi ke yi, ya kuma ba da tabbacin cewa da zarar matakan sun fara aiki, za a samu saukin wannan matsalar, sai dai ya ce a wasu wuraren da ake doro wa direbobin shanun, ba za su iya sanin ko na sata ba ne.
“Duk direban da muka samu ya dauko shanun a inda bai dace ba, za mu hukunta shi domin irin wannan mutum na sane da kayan sata ne,” inji shugaban direbobin.