Miyatti Allah ta yi sabon shugaba a Kwara

kungiyar Fulani makiyaya ta Miyyati Allah ta yi zabe a Jihar Kwara, zaben da ya gudana a garin Ilori a karkashin jagorancin shugabanninta na kasa.Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Muhammadu Kirwa Hardon Zuru ya so a yi sulhu tun da fari kafin a kai ga yin zaben, domin samar da maslaha. Sai dai hakan ya […]

Miyatti Allah ta yi sabon shugaba a Kwara
Miyatti Allah ta yi sabon shugaba a Kwara

kungiyar Fulani makiyaya ta Miyyati Allah ta yi zabe a Jihar Kwara, zaben da ya gudana a garin Ilori a karkashin jagorancin shugabanninta na kasa.
Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Muhammadu Kirwa Hardon Zuru ya so a yi sulhu tun da fari kafin a kai ga yin zaben, domin samar da maslaha. Sai dai hakan ya ci tura, inda aka yi zaben wanda ya gudana cikin salama da ban al’ajabi, domin dan takarar da ya lashe zaben, Alhaji Usaman Adamu ya lashe duka kuri’un da dukkan jama’ar suka kada shi ko abokin takarar nasa, Alhaji Hassan Yusuf ya tashi ba kuri’a ko daya.
Sabon shugaban ya bayyana cewa zai dora daga inda ya tsaya kuma ya tabbatar wa da Fulanin Jihar Kwara cewa ba zai ba su kunya ba, zai samar masu ababen more rayuwa, kamar makarantu da asibiti. Ya yaba wa shugaban kungiyar na kasa, wanda a gabansa aka gudanar da w=annan zabe. Don haka ya yi kira ga abokin hamayyarsa da ya zo su hada kai don ci gaban Fulanin Jihar Kwara baki daya.
Shi ma shugaban kungiyar Miyyati Allah  na kasa,  Alhaji Muhammadu Kirwa Hardon Zuru, ya taya sabon shugaban kungiyar murna, inda ya bayyana cewa ayyukkan alheri da shugaban ya yi ne lokacin da yake shugabancin kungiyar, don haka ya yi kira a gare shi, ya dora daga inda ya tsaya kuma kungiyar Miyatti  Allah ta kasa ba ta san wani shugaba ba sai Alhaji Usman Adamu, don shi jama’a suka zaba. Ya kuma yi kira ga sarakunan Fulani na kasar nan, da su fidda tsoro su fidda bata garin Fulani, domin sun san su. “Mu kuma za mu kama maku, domin ba za mu yarda da bara-gurbi a tsakaninmu ba.”  Inji shugaban.