Miyetti Allah Kautal Hore ta nesanta kanta da Jonathan
kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore reshen Jihar Neja ta nesanta kanta daga tabbatar wa Shugaba Goodluck Ebele Jonathan cewa zai samu kuri’un Fulanin kasar nan da Shugaban kungiyarsu na kasa Alhaji Abdullahi Bello Badejo da sauran mukarrabansa suka yi a fadar shugaban kasa a makon jiya. Jami’in hulda da jama’a na kungiyar reshen Jihar Neja […]
kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore reshen Jihar Neja ta nesanta kanta daga tabbatar wa Shugaba Goodluck Ebele Jonathan cewa zai samu kuri’un Fulanin kasar nan da Shugaban kungiyarsu na kasa Alhaji Abdullahi Bello Badejo da sauran mukarrabansa suka yi a fadar shugaban kasa a makon jiya.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar reshen Jihar Neja Malam Iliyasu Adamu Albishir ne ya sanar da haka yayin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya a Minna a ranar Litinin.
Ya ce “Ban ga dalilin da za mu zabi Shugaba Jonathan ba, alhali kowa ya san cewa muna da mai gaskiya Janar Muhammadu Buhari, wanda ilahirin ’yan Najeriya ke bukatar ya shugabance su, saboda ya tsayar da gaskiya a al’amuransa. Mu da muke da irin wannan mutumin yaushe za mu ce muna goyon bayan wanda bai san darajarmu ba?”
Ya bayyana a cikin dalilin da ya sa ba za su zabi Jonathan ba ya hada da yadda ya kasa magance matsalar tsaro, kasancewar ba a taba asarar rayuka da dukiyoyin jama’a a tarihin kasar nan ba kamar a irin wannan lokacin.
Ya bayyana takaicinsa ganin yadda Shugabansu na kasa ya yaudare su ya je fadar shugaban kasa domin yi masa albishir din da ba a sa shi ba.
“Mu dai daga Jihar Neja babu wanda ya yi shawara da mu. Ko da an shawarce mu ma, ba za mu yarda da haka ba.” Inji shi.
Ya ce dalilin haka suka daura damarar yi wa Janar Buhari kamfe daga ruga zuwa ruga, tare da ci gaba da wayar da kan Fulani yadda za su yi zabe ba tare da sun bata kuri’unsu ba.