Miyetti Allah ta ƙaddamar ’yan banga 1,100 a Nasarawa
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta kaddamar da jami’an tsaron sa-kai 1,144 da nufin yakar masu garkuwa da mutane da satar dabbobi da ayyukan ’yan bindiga a Jihar Nasarawa.
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta kaddamar da jami’an tsaron sa-kai 1,144 da nufin yakar masu garkuwa da mutane da satar dabbobi da ayyukan ’yan bindiga a Jihar Nasarawa.
Shugaban kungiyar na kasa, Abdullahi Bello Bodejo, ya ce an kafa rundunar jami’an tsaron ce domin taimakawa wajen samar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.
Da yake kaddamar da ’yan bangar a garin Lafia, babban birnin jihar, Abdullahi Bello Bodejo ya yi kira ga rundunar sojin sama da ta kasa da ’yan sanda da su ba su haɗin kai a yayin gudanar da ayyukansu.
A cewarsa, “an kafa ’yan bangar makiyaya ne a matsayin wani bangare na bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, tafiya tare da juna, da kuma yaki da matsalar satar shanu, ’yan bindiga da kuma yunwa da talauci.
- Abin Da Ya Sa Rashin Tsaro Ke Neman Cinye Abuja
- Dokar Najeriya ta haramta biyan kuɗin fansa — Ministan Tsaro
“Za su taimaka wajen dakile wadannan barazana da kuma samar da tsaro da aminci ga al’ummomin manoma da makiyaya a fadin jihar nan.”
Bodejo ya ce an zabo ’yan bangan ne daga yankunansu domin dawo wa al’umma da nutsuwa ta hanyar taimaka wa jami’an tsaron gwamnati wajen yakar ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka hana al’umma sakat.
Hakan a cewarsa zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta yanayin tsaro a jihar.
Daga nan ya ce, “’yan bangan su sani cewa wajibi ne ku hada kai ku yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro wajen zakulo bata-garin a cikin al’umma, sannan a kawo karshen zargin zalunci da ake wa al’umma ko daukar alhakin wadanda ba su aikata laifi ba saboda abin da bata-garin cikinsu suka aikata.”
Shugaban kungiyar ya jinjina wa gwamnatin Jihar Nasarawa da hukumomin tsaro bisa hadin kai da goyon bayan da suka bayar wajen samar da ’yan bangan.
“An yi taka tsantsan wajen saboda da tantance mambobin bisa yadda doka ta tanada.
“An samar da su ne domin su kara taimakawa a aikin da hukumomin tsaro ke yi a cikin al’umma domin amfanin kasa,” in ji shi.
Ya kuma ja hankalin jami’an da su guji shiga ayyukan laifi, aikinsu shi ne taimakon jami’an tsaro.
Tun da farko, wakilin Kwamandan Bataliyar Tsaron Shugaban Kasa, Laftanar-Kanar Inuwa Bala, ya gargadi su da su kasance masu halaye na gari, su guji wuce gona da iri a aikinsu.
Inuwa wanda ya samu wakilcin Manjo M. A. Sani ya kuma ba su tabbacin samun hadin kan sojojin sama na kasa da kuma ’yan sanda a aikin samar da tsaro a jihar.
Shi ma Abdulaziz Aliyu, wakilin Kwamishina ’yan sandan jihar, Umar Shehu Nadada, ya yaba da samae da ’yan bangan domin aiki da hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.