Miyetti Allah ta bukaci a yi bincike kan kisan Fulani a yankin Saminaka
kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kasa ta bukaci gwamnati ta yi bincike kan kisan gillar da aka yi wa wasu Fulani, a ranar Labarar makon da ya gabata a kusa wani kauye mai suna Kunkuru da ke yankin Saminaka a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna. kungiyar ta bayyana wannan bukata ce […]
kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kasa ta bukaci gwamnati ta yi bincike kan kisan gillar da aka yi wa wasu Fulani, a ranar Labarar makon da ya gabata a kusa wani kauye mai suna Kunkuru da ke yankin Saminaka a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna. kungiyar ta bayyana wannan bukata ce a wani taron manema labarai da ta kira a garin Kaduna.
Da yake yi wa ’yan jarida karin bayani dangane da wannan al’amari, babban sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Baba Usman Ngelzarma ya bayyana cewa su dai wadannan Fulani da soja suka yi wa kisan gilla bayan da suka azabtar da su a kusa da wannan kauye, suna kan hanyar tafiya da dabbobinsu, bayan da suka taso daga kudancin kasar nan za su tafi yankinsu a Jihar Jigawa.
Ya ce wannan lamari wani babban abin takaici ne, kuma wani shiri ne na ganin an karar da al’ummar Fulani makiyaya.
kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro su binciko wadanda suka aikata wannan aika-aika domin a hukunta su, kuma ta bukaci a biya diyya ga iyalan Fulanin da aka yi wa kisan gilla.
A wata sabuwa kuma mai martaba Sarkin Saminaka, Alhaji Musa Muhammad Sani ya nuna takaicinsa kan kisan gillar da aka yi wa Fulanin a yankin masarautarsa. Sarkin ya nuna takaicin nasa ne a lokacin da shugabannin al’ummar Fulani makiyaya suka kai masa ziyara a fadarsa kan wannan al’amari.
Ya ce, “Ya kamata jami’an tsaro su fahimci mu al’ummar wannan yanki muna zaune lafiya da junanmu, domin a duk Jihar Kaduna babu inda ake zaune lafiya kamar wannan yanki. Don haka wannan abu da ya faru wani babban abin takaici ne”.
Ya yi kira ga jami’an tsaron su yi adalci kan aikin da ya kawo su yankin. Daga nan ya yi kira ga al’ummar yankin su cigaba da tsayawa kan gaskiya da kuma zaman lafiya a tsakaninsu.
Tuni dai kwamitin da majalisar dokokin Jihar Jigawa ta kafa don binciken wannan al’amari, ya ziyarci garin Saminaka, don binciken wannan al’amari.
A lokacin da kwamitin ya ziyarci garin na Saminaka, ya gana da Sarki da sauran shugabannin karamar Hukumar Lere.