Miyetti Allah ta dakatar da shugabanta kan goyon bayan Jonathan

kungiyar Mitetti Allah Kautal Hore ta dakatar da shugabanta na kasa Alhaji Bello Abdullahi Badejo sakamakon yi ruwa da tsaki cikin al’umaran siyasa kasar nan.An bayyana dakatarwar ne a ranar Litinin cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar wadda Alhaji Wakili Ali Babangida ya sanya wa hannu.Shugabannin kungiyar da sakatarori da jiga-jigan kungiyar daga jihohi […]

Miyetti Allah ta dakatar da shugabanta kan goyon bayan Jonathan
Miyetti Allah ta dakatar da shugabanta kan goyon bayan Jonathan

kungiyar Mitetti Allah Kautal Hore ta dakatar da shugabanta na kasa Alhaji Bello Abdullahi Badejo sakamakon yi ruwa da tsaki cikin al’umaran siyasa kasar nan.
An bayyana dakatarwar ne a ranar Litinin cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar wadda Alhaji Wakili Ali Babangida ya sanya wa hannu.
Shugabannin kungiyar da sakatarori da jiga-jigan kungiyar daga jihohi 30 ne suka halarci tattaunawar kan batun shugaban kungiyar.
kungiyar ta ga baiken shugaban nata sakamakon kin shirya zabe bayan shekara hudu da yi wa kungiyar rijista, wanda hakan ya saba wa kundin tsarin kungiyar, inda doka ta ce a shirya zabe duk bayan shekara 3.
kungiyar ta zargi shugabanta da yin ruwa da tsaki cikin harkokin siyasar kasar nan, na baya-bayan nan shi ne goyon bayan Shugaba Goodluck Jonathan.
kungiyar ta ce ba da yawunta ya yi yanke wannan hukuncin ba, sannan al’amarin ya sanya kunya ta kama su.
A yanzu an nada kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Alhaji Lawal Ali Mai Mamman don a binciki laifuffukan da ake zargin shugaban kungiyar da aikatawa. An ba kwamitin wata daya ya gabatar da rahotansa.
A rantsar da shugabannin riko a karkashin shugabancin Dokta Ibrahim Abdullahi don ci gaba da gudanar da ayyukan kungiyar.
kungiyar ta ce ba ta adawa da duk wani mai neman mukamin siyasa a kasar nan, don haka ta bukaci mambobinta su goyi bayan duk dan takarar da suke so.