Miyetti Allah ta yunkuro don kawo karshen satar shanu
Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta ci alwashin hada kai da jami’an tsaro don dakile masu garkuwa da mutane da kuma satar dabbobi. Da yake yi wa mahalarta taron kungiyar jawabi a jiya a garin Minna, Mataimakin Shugaban Kungiyar na Yankin Arewa ta Tsakiya, Alhaji Idris Gidado Bebeji, ya ce kungiyar ba za ta zauna […]
Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta ci alwashin hada kai da jami’an tsaro don dakile masu garkuwa da mutane da kuma satar dabbobi.
Da yake yi wa mahalarta taron kungiyar jawabi a jiya a garin Minna, Mataimakin Shugaban Kungiyar na Yankin Arewa ta Tsakiya, Alhaji Idris Gidado Bebeji, ya ce kungiyar ba za ta zauna ta na kallon bata-garin Fulani suna bata musu suna ta hanyar aikata laifuka.
Bebeji ya bayyana takaicnsa dangane da ake samun karuwar matasan Fulanin da suka aikata laifin garkuwa da mutane.
Ya kara da cewa kungiyar na daukar matakan da suka dace don kawo karshen lamarin.
Ya ba da tabbacin cewa kungiyar za ta tallafa wa jami’an tsaro da ’yan bangar da za su rika taimaka wa da bayanan da za su dakile ayyukan bata-garin
Ya bukaci jami’an tsaro kada su bayar da belin duk wanda suka kama da hannu dumu-dumu a cikin aikata laifuka don ya zama darasi ga sauran mutane.
Kungiyar ta ce nan ba da jimawa ba za ta dirarwa iyayen da suka ki sanya ’ya’yansu makarantar boko.