Miyetti Allah ta zargi sojoji da tsoratar da shaidunta a kan kashe Bafulatana a Abuja

kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yankin Birnin Tarayya, Abuja, ta zargi sojojin da ke gudanar da bincike a kan kashe wata Bafulatana mai tallar nono a Abuja da ake zargin wani soja da aikatawa, da tsoratar da shaidun da suka tanada a kan al’amarin bayan sun gayyace su a farkon makon nan. Wani […]

Miyetti Allah ta zargi sojoji da tsoratar da shaidunta a kan kashe Bafulatana a Abuja
Miyetti Allah ta zargi sojoji da tsoratar da shaidunta a kan kashe Bafulatana a Abuja

Marigayiya Binta Usmankungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yankin Birnin Tarayya, Abuja, ta zargi sojojin da ke gudanar da bincike a kan kashe wata Bafulatana mai tallar nono a Abuja da ake zargin wani soja da aikatawa, da tsoratar da shaidun da suka tanada a kan al’amarin bayan sun gayyace su a farkon makon nan. Wani jigo a kungiyar, Ardon Jiwa Alhaji Muhammadu Bello ne ya bayyana haka a yayin zantawa da Aminiya.
Ardon na Jiwa ya ce bayan sun amsa gayyatar ofishin binciken manyan laifuffuka (CID) na Rundunar ’Yan sandan Abuja a farkon makon nan, inda a can aka fara bincike kafin sojoji su amshi lamarin don yin nasu bincike kamar mako biyu yanzu, wasu sojoji uku da aka gabatar da su gare su a matsayin masu bincike, sun bukace shi ya yi masu bayanin yadda ya samu labarin kisan. “Na sanar da su cewa na samu labarin lamarin ne a daidai lokacin da na fara yin alwala don Sallar La’asar a ranar, kuma a lokacin ne na garzaya wurin inda na iske ta a mace,” inji shi.
Ya ce bayan ya yi bayani, sai suka koma bangaren shaidunsu inda suka tambayi na farko yadda ya shaida al’amarin, “Sun yi ta yi masa tambayoyi da ba su da hurumin yi tare da kokarin tsoratar da shi da nufin raunana masa gwiwa, mun bayyana masu rashin gamsuwarmu a kai, kuma ba a jima ba sai suka wuce suka bar mu a wurin. Saboda haka ina kira ga shugabanninsu su hanzarta mika wannan lamari ga kotu saboda ba za mu yarda da bincikensu ba bare hukuncinsu,” inji Ardon.
Aminiya ta gano cewa sojan da a ke zargi da kashe Bafulatanar Last Corporal Oge Itudo ba ya wurin a lokacin da aka gayyaci kungiyar Miyetti Allah.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, DSP Hyelhira Altine Daniel, ta tabbatar da ganawar sojojin da bangaren Fulanin, sai dai ta ce za su gabatar da lamarin a kotu da zarar sojojin sun dawo masu da wanda ake zargin don ya fuskanci hukunci.