‘Miyetti Allah uwa ce ga dukkan kungiyoyin Fulani’

Shugaban kungiyar Jumnati-Fulbe na kasa Sarkin Fulanin Igangan, Alhaji Salihu Kadiri, ya ce kungiyar Miyetti Allah, uwa ce ga dukkan kungiyoyin Fulani da ke Najeriya.Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa ’yan jarida karin bayani bayan kungiyarsu ta kammala taron shekara-shekara a garin Olorunda da ke Jihar Ogun a Lahadin makon jiya.Ya […]

‘Miyetti Allah uwa ce ga dukkan kungiyoyin Fulani’
‘Miyetti Allah uwa ce ga dukkan kungiyoyin Fulani’

Shugaban kungiyar Jumnati-Fulbe na kasa Sarkin Fulanin Igangan, Alhaji Salihu Kadiri, ya ce kungiyar Miyetti Allah, uwa ce ga dukkan kungiyoyin Fulani da ke Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa ’yan jarida karin bayani bayan kungiyarsu ta kammala taron shekara-shekara a garin Olorunda da ke Jihar Ogun a Lahadin makon jiya.
Ya ce wasu jama’a ne ke kokarin raba kawunan al’ummar Fulani, inda suke baza jitar-jitar cewa sun kafa kungiyarsu domin ta zama kishiya ga Miyetti Allah ne.
Ya ce “Mun kafa wannan kungiya ne domin hadin kan al’ummar Fulani da ci gabansu a Najeriya. Kuma, mun bayar da umarni ga reshen kungiyar na jihohi su rika zama suna yin taro domin tattaunawa a kan matsalolin ilmin makiyaya da samar da zaman lafiya a tsakaninmu da sauran jama’a musamman manoma.”
Mataimakin Shugaban kungiyar na kasa, Sarkin Fulanin Iguwa, Alhaji Adamu Oloru, ya ce sai sun yi binciken kwakwaf kafin su yi wa mutum rajista.
Ya ce, “Da farko muna karbar kowa ne ba tare da bincike ba, a yanzu mun sauya salo, domin sai mun yi binciken kwakwaf ga dukkan wanda yake so ya shiga cikin kungiyarmu.  Muna yin wannan binciken ne domin guje wa daukar bara-gurbi. Duk wanda muka samu da aikata wani laifin da ya fi karfin sasantawarmu, sai mu mika su shi ga jami’an tsaro.”
Mai masaukin baki Shugaban kungiyar reshen Jihar Ogun, Alhaji Abubakar Ibrahim Dende, ya nuna matukar farin ciki da irin hadin kai da suke samu a tsakaninsu da gwamnatin jihar.
Ya ce kungiyar tana da mambobi dubu 2 a Jihar Ogun
Babban sakataren kungiyar Jumnati Fulbe na kasa Alhaji Muhammadu Salihu Kaoje, ya ce sun shirya wannan taro ne domin wayar da kan al’ummar Fulani dangane da kyautata zamantakewa tsakaninsu da jama’ar garuruwan da suke da zama.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno