MMM kasaitacciyar Matsala!
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, ina mana murnar idin karamar Sallah, Allah Ya sa mun dace da alheran cikin watan Ramadan, amin.A yau kuma inshaAllah, za mu gabatar da karin bayani kan matsalar matasan magidanta, watau ta fitar maniyyi da wuri lokacin gabatarwar ibadar aure; karo na hudu ke nan da […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, ina mana murnar idin karamar Sallah, Allah Ya sa mun dace da alheran cikin watan Ramadan, amin.
A yau kuma inshaAllah, za mu gabatar da karin bayani kan matsalar matasan magidanta, watau ta fitar maniyyi da wuri lokacin gabatarwar ibadar aure; karo na hudu ke nan da wannan fili zai yi bayani kan wannan matsala, saboda kasaitar da wannan matsala ta yi a cikin rayuwar aure, hakan ne ya sanya nake yawan samun tambayoyi daga masu karatu kan yadda za su tafiyar da wannan matsala. Da yawa sun yi kukan cewa ba su amfani da shafin intanet na facebook, ballantana su duba ma’ajiyar bayanan da suka wuce na wannan fili, a dalilin haka za mu kara gabatar da bayani kashi na hudu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Abubuwan da ke haifar da MMM da maganinsu
Kowace irin cuta, rauni ko wata matsalar da ta shafi jikin dan Adam, abu na farko da ya kamata mutum ya yi shi ne ya je asibiti don ya ga likita, su tattauna domin a gano ainihin abin da ya haifar masa da matsalar, domin kada a rika cuta daban magani daban, duk da dai bincike ya tabbatar yawanci sabo da zinar hannu kafin aure ne ke haifar da wannan matsala, tana iya yiwuwa kuma wasu matsalolin ne, kamar raunin jijiyoyin al’aura, wanda abubuwa daban-daban na iya haifar da shi, kuma dole sai da binciken likita ne za a iya gano ko mene ne ainihin abin da ya haifar da ita don a magance ta da irin maganin da ya dace. Shi ya sa ya fi alfanu musamman ga magidanci ya tabbata bai yi sabo da zinar hannu ba lokacin samartaka, wanda da ya yi kokarin ganin likita don a tantance ainihin abin da ke haifar masa da matsalar, za a iya ganowa cikin sauki.
Ga muhimman abubuwan da ka iya zama dalilin saurin fitar maniyyi da wuri, in mutum ya fahimci nasa dalilin, sai ya yi amfani da bayanin da zai zo kan wannan dalilin wajen neman warakar matsalarsa. Da fatan Allah Ya sa a dace, amin.
Sabo Da Zinar Hannu
Lokacin da matashi yake kokarin cimma biyan bukatar sha’awarsa da hannunsa, zuciyarsa a cike take da tsoron kada wani ya zo ya same shi a wannan hali, kuma hankalinsa a kagauce yake ya yi saurin ya gama don kada wani ya same shi, shi ya sa ma’aikatar hankalinshi ta saba da bayar da izini ga jijiyoyin sha’awa da su fitar da maniyyin nan da nan don kubutar da rayinta aukuwar wannan abu da ya cika shi da tsoro. To wannan sabo da matashi ya yi ga ma’aikatar hankalinsa na fitar da maniyyi da zarar sha’awa ta motsu, shike haifar masa matsalar MMM bayan ya yi aure.
Maganin warakar MMM a dalilin yi wa kai sabo da zinar hannu shi ne, saba ma kai, zuciya da ma’aikatar hankali da ibadar aure da uwargida kamar yadda aka yi musu sabo da zinar hannu. Wannan na nufin dagewa da yin abin a-kai-a-kai, da yin kokari ko yaushe a ga cewa lallai an danne an kara lokacin dadewar. Kada fargaba ko kunyar faruwar hakan ta sa mutum ya rika kaurace wa ibadar auren, dagewa zai yi ya nace ya kuma daure, sannan gami da cikakken hadin kai da taimakawa daga matar mutum, inshaAllahu cikin kankanen lokaci mutum zai ga bayan wannan matsala.
Tsananin doki
Ga wanda yake ganin tsananin dokinsa ne ke haifar masa da wannan matsala sai ya yi tunani kuma ya nisa cikin tunanin nasa ya ga shin me ke sa shi yin tsananin dokin? Tsananin yunwar ibadar auren ce ke sa masa haka? Ko dama can haka dabi’arsa take, watau shi mai tsananin kazar-kazar ne? To maganin wannan dai shi ne mutum ya fara gabatarwa a natse kuma ya cire duk wani hanzari daga ciki, kodayaushe ya ji dokinsa ya karu, to ya yi kokari ya danne shi ya ture shi ta hanyar karkatar da ma’aikatar hankalinsa daga wannan tunanin, yana iya dan dakatar da ibadar auren har sai ya ji dokin ya rage masa, hanya mai sauki ita ce mutum ya gantsara wa hannunsa ko dan yatsansa cizo, wannan zai dan sanyaya masa dokin har dai ya samu ya kai dadewar da yake son ya kai insha Allah.
Fargaba
Ga sabon magidancin da yake yawan fargabar iyawarsa ko kwarewarsa ta fannin ibadar aure har hakan ya haifar masa matsalar matasan magidanta. Maganin fargaba shi ne yin fatali da ita, da duk wani bakin shauki ko damuwa da faruwar fitar maniyyi da wuri ke haifarwa, kullum mutum ya sa tunani mai kyau game da abin cikin zuciyarsa. Sannan tattauna da matarsa, da fayyace mata damuwa da fargabar mutum game da abun shi ma wata hanya ce ta magance fargaba daga cikin zuciya. Faruwar abin na rana daya nasa wasu su yi ta fargabar yiwuwar maimaituwarsa, su rika ta ganin kodayaushe hakan ne dai zai faru, wannan fargaba ke sa kara aukuwar matsalar da haka har ta yi yawa, amma idan ba a yi fargaba ba tun farko, to akwai yiwuwar matsalar ba za ta maimaitu ba tun daga wancan na farkon.
Ma’assalam, sai sati na gaba insha Allah sauran bayani kan sauran dalilan da hanyoyin magance su. Da fatan Allah Madaukakin Sarki Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.