MMM kasaitacciyar Matsala! (2)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da matsalar matasan magidanta (MMM), watau na fitar maniyyi da wuri. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu fama da wannan matsala har su samu waraka, amin.4. Rashin sabawa ko kwarewa da ‘Ibadar Aure’Yadda za […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da matsalar matasan magidanta (MMM), watau na fitar maniyyi da wuri. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu fama da wannan matsala har su samu waraka, amin.
4. Rashin sabawa ko kwarewa da ‘Ibadar Aure’
Yadda za a magance rashin sabawa ko rashin kwarewa shi ne, sai mutum ya yi kokarin yawan aikatawa har sai ya saba, sabon da zai kai shi ga kwarewa, hanyar kwarewa kuwa sanin ilmin abin, ba mai iya kwarewa kan abin da bai da ilminsa, dole sai da koyo akan iya, don haka sai ma’aurata su hada kai su yi ta koyo tare, su lakanci abin sosai. Mutum ya fahimci yanayin sha’awarsa, ya fahimci me ke sa sha’awarsa ke saurin kaiwa gaci? Sannan ya fahimci yadda zai yi ya rika sa tana dadewa ba ta kai gacin ba. Koyo sai da hakuri da naci, don haka duk mai son ya kware a fannin ibadar aure dole sai ya nace kuma ya yi hakuri.
5 Tsananin jin lazzar sha’awa
Ga wanda ke ganin tsananin jin lazzar sha’awar ne ke haifar masa saurin fitar maniyyi da wuri sai ya gano abubuwan da ke sanya shi jin lazzar, shin tsananin so ne ko sha’awar matarsa? Ko wani abu ne da take yi masa, ko wani yanayi ne daban, ko kuwa jin lazzar a jikinsa ne ko al’aurarsa? Ko ma mene ne sai mutum ya yi kokari ya nemi hanyar raguwarsa, in wani abu ne da matarsa ke yi, sai ya ce ta daina har sai lokacin da ya zamana yana da cikkakken iko wajen iya jan ragamar sha’awarsa ta yadda ko ta yi abin ya san yadda zai sarrafa sha’awarsa har ya kasance bai samu wannan matsala ba. Sanya robali a al’aura na tsawon minti talatin a kullum na iya rage tsananin jin lazza mai dangane da al’aura.
6 Raunin jijiyoyin al’aura
Shan taba da sauran kwayoyin sa maye da kuma sabo da zinar hannu, duk dabi’u ne da ka iya raunatar da jijiyoyin al’aura da mazakutar da namiji, don haka daina wadannan dabi’u ne magungunan wannan matsala. Ta iya yiwuwa kuma wata kwayar cutar ce ta haifar wa mutum da wannan matsala, shi ya sa ya fi dacewa a ga likita kafin yanke wani hukunci daban. Za a iya magance raunin al’aura cikin sauki ta hanyar motsa jijiyoyin al’aura duk lokacin da aka je yin fitsari, maimakon a sake shi gaba daya sai a rika fitar da shi kadan-kadan. Da mutum ya saba kuma ya lakanci yanayin abin, zai gane mazaunin wannan jijiyoyi, da kuma yadda ake motsa su din, to ko ba lokacin fitsari ba sai ya rika motsa su, sau uku a rana, duk yi daya ya kasance ya motsa su sau sittin ko sama da haka.
7 Rashin kaurin ruwan maniyyi.
Wannan wata matsala ce da sabo da zinar hannu ke haifarwa, haka ma rashin wasu muhimman sinadarai masu gina jiki. In mutum yana cikin hali na yin zinar hannu a-kai-a-kai, do dole sai ya bari sannan ya ga ingancin ruwan maniyyinsa. In kuma ba wannan ne dalilin ba, to sai mutum ya kara kala-kalar kayan abinci masu kara ingancin maniyyi, irin su kwan salwa, diyan kabushi, kifi, kayan marmari da ganyayyaki. Da kuma abinci mai dauke da sinadarin carbohydrates kamar kowane kalar hatsi, gero masara dawa, shinkafa, dankalin hausa da sauransu.
8. Rashin iya jan ragamar sha’awa
Wannan dalilin yana bayan kowace irin matsalar fitar maniyyi da wuri, ko da mene ne sababinta kuwa, don in mutum ya iya jan ragamar sha’awarsa to ba yadda za a yi ya samu matsalar fitar maniyyi da wuri. Yawanci masu fama da wannan matsala sukan bari sha’awarsu na jan ragamarsu maimakon su ja ta. Duk mai son rabuwa da wannan matsalar sai ya dage ya san yadda ya yi sha’awarsa ta dawo karkashin ikonsa, ya zamana shi ke jan ragamarta, shi ke sarrafata duk yadda ya so, ba ita ba, don shi ke da ita, karkashin mulki da ikonsa take. Hanyar cim ma hakan kuma ita ce koyon dannewa da yin fada da ita duk lokacin da take kokarin kufcewa ta kai gaci ba tare da mutum ya shirya ba.
Sai sati na gaba bayani na zuwa kan dabarun da za a yi amfani da su wajen ganin an kware, kuma an gwanance wajen iya jan ragamar sha’awa yayin gabatarwar ibadar aure don magance wannan matsala. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.