Mnangagwa zai gaji Mugabe

Tsohon mataimakin Robert Mugabe ne zai gaji tsohon Shugaban kasar, wanda kuma ya taba kasancewa babbabn na hannun daman Mugabe. Emmerson Mnangagwa wanda ake wa lakabi da “Kada” saboda rashin tsoronsa, yana da shekara 75 a duniya. Kuma shi ma tsohon dan gwagwarmaya ne. BBC ta ruwaito wani mai magana da yawun jam’iyyar Zanu-PF yana […]

Mnangagwa zai gaji Mugabe

Tsohon mataimakin Robert Mugabe ne zai gaji tsohon Shugaban kasar, wanda kuma ya taba kasancewa babbabn na hannun daman Mugabe.

Emmerson Mnangagwa wanda ake wa lakabi da “Kada” saboda rashin tsoronsa, yana da shekara 75 a duniya. Kuma shi ma tsohon dan gwagwarmaya ne.

BBC ta ruwaito wani mai magana da yawun jam’iyyar Zanu-PF yana cewa zai karasa wa’adin Mugabe ne kafin a yi zabe na gaba, cikin watan Satumban badi.

BBC ta rairayo kadan daga cikin tarihin Mnangagwa kamar haka:

Ana yi masa lakabi da “kada” saboda iya ruwansa a fagen siyasa

Ya samu horon soja a China da Masar

Ya sha azabtarwa a hannun dakarun Rhodesia bayan “gungun matasan kadoji” da yake jagoranta sun kaddamar da hare-hare

Ya taimaka wajen jan ragamar yakin kwatar ‘yancin Zimbabwe a 1970

Ya zama jagoran leken asiri lokacin yakin basasan 1980, wanda aka kashe dubban fararen hula, sai dai ya musanta duk wani hannu a kashe-kashen kiyashi, inda ya dora alhakin kan rundunar soja

Ana kallonsa a matsayin muhimmin jami’in da ke kulla tsakanin sojoji da hukumomin leken asirin kasar da kuma jam’iyyar Zanu-PF

Ana zarginsa da zama ummul aba’isin hare-haren da aka kai wa magoya bayan ‘yan adawa bayan zaben 2008

Jagoran adawar Zimbabwe, Morgan Tsbangirai ya ce ya zama jazama yanzu a fito da wani tsari da zai tabbatar da yin zabuka cikin gaskiya da adalci.

Emmerson Mnangagwa ya tsere daga kasar bayan Shugaba Robert Mugabe ya kore shi daga mulki saboda zargin “rashin biyayyarsa”.

Matakin ne ya ingiza sojojin kasar yin dirar mikiya inda suka yi wa Shugaban daurin talala a gidansa da ke Harare.