MNDPR ta rufe gidan mai da ke sayarwa sama da farashin gwamnati

Hukumar ta gano wasu gidajen man sai an ba da cin hancin N1000 kafin a bada man.

MNDPR ta rufe gidan mai da ke sayarwa sama da farashin gwamnati

Gidan Mai

Hukumar Kula da Farashin Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta rufe gidan man Conoil a Kano kan sayar da fetur sama da farashin da gwamnati ta kayyade.

Shugaban ofishin NMDPRA na shiyyar Kano, Aliyu Samani, ne ya ba da umarnin rufe gidan man saboda saba ka’ida.

Kazalika, NMDPRA ta ba da umarnin a gaggauta fito da man da ta gano an boye a wasu manyan gidajen mai a Kano a sayar wa jama’a.

Hakan ya faru ne a lokacin da Samani ya jagoranci jami’an hukumar da ’yan jarida zuwa aiwatar da aikinsu a cikin birnin.

Jami’in ya bayyana cewa, doka za ta yi aiki a kan duk gidan man da aka gano ya boye fetur ko yana sayarwa sama da farashin gwamnati, kana a tilasta masa fitar da man ya sayar wa jama’a.

Ya kara da cewa, muddin dillalan mai suka yi abin da ya kamata, babu dalilin da za a fuskanci karancin fetur da kuma tsadarsa kamar yadda ake fuskanta yanzu.

Ya ce, daga farkon Disamba zuwa yanzu, dillalan mai na Kano sun samu litar fetur miliyan 30.7 kwatankwacin tanka 641.

Don haka ya ce, dillalan ba su ba da goyon bayan da ya dace wanda hakan ya sa kungiyar dillalan mai (IPMAN), ta samu damar sayar da fetur N300 kan lita.

Ya ce, yayin gudanar da aikin, sun gano yadda wasu gidajen man ke boye man, wasunsu kuwa na sayar da man fiye da farashin da aka kayyade.

Haka nan, ya ce sun gano cewa a wasu gidajen man sai an ba da cin hancin N1000 kafin a sayar wa mutum da man.