Modric da Ronaldo da Salah ne za su fafata a Gwarzon dan kwallon duniya na bana
A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da sunayen ’yan kwallo uku da za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon kafa na duniya da aka fi sani da Ballon D’ or. Gasar za ta gudana ne a ranar Litinin 24 ga wannan wata da muke […]

A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da sunayen ’yan kwallo uku da za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon kafa na duniya da aka fi sani da Ballon D’ or.
Gasar za ta gudana ne a ranar Litinin 24 ga wannan wata da muke ciki a birnin Landan.
Sai dai wannan shi ne karon farko da za a yi gasar ba tare da dan kwallon FC Barcelona kuma haifaffen Ajantina Lionel Messi ba a shekaru 10 da suka gabata.
Yayin da FIFA ta zabi Lucas Modric, dan kulob din Real Madrid kuma haifaffen Kuroshiya ne saboda kwazon da ya nuna a Gasar cin kofin duniya, inda ya taimaki kasarsa Kuroshiya kai wa wasan karshe a karon farko a tarihin gasar sannan ya taimaki kulob din Real Madrid na Sifen lashe kofunan gasar zakarun kulob na Turai sau uku a jere. Ronaldo kuma an zabe shi ne saboda ya taimaki kulob din Real Madrid na Sifen lashe kofunan zakarun kulob na Turai sau uku a jere, kuma shi ne dan kwallon da ya fi kowane dan kwallo yawan zura kwallaye a raga a tarihin gasar. Sannan ya yi kokari a gasr cin kofin duniya inda ya zura kwallaye uku a raga a wasansu na farko da kasar Sifen.
Shi kuma Mohammed Salah an zabe shi ne bayan ya samu nasarar zura kwallaye 42 a raga a kakar wasan da ta wuce, kuma ya kafa sabon tarihi a gasar firimiyar Ingila bayan ya zura kwallaye 32.
Wadannan dalilai ne ya sa Hukumar FIFA ta zabi wadannan ’yan kwallo da za su fafata a tsakaninsu kafin a fitar da zakara.
Sai dai a makon jiya ne Lucas Modric ya lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Nahiyar Turai. Kuma sun fafata ne tare da wadannan ’yan kwallo.
Yanzu dai masoya kwallon kafa sun zuba ido su ga wanda za a zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon kafa na duniya a bana. Ronaldo da Lionel Messi ne suka taba lashe gasar har sau biyar amma Lucas Modric da Mohammed Salah ba su taba lashe wannan kyauta ba.