Mohammed Salah ne ya lashe Gwarzon dan kwallon Afirka na BCC

Shahararren dan kwallon Masar Mohammed Salah ya samu nasarar lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana.  A ranar Litinin da ta wuce ne kafar watsa labaran BBC ya sanar da sakamakon gasar. ’Yan kwallo biyar ne suka fafata a kokarin lashe wannan gasa da suka hada da Mohammed Salah dan asalin Masar […]

Mohammed Salah ne ya lashe Gwarzon dan kwallon Afirka na BCC

Shahararren dan kwallon Masar Mohammed Salah ya samu nasarar lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana.  A ranar Litinin da ta wuce ne kafar watsa labaran BBC ya sanar da sakamakon gasar.

’Yan kwallo biyar ne suka fafata a kokarin lashe wannan gasa da suka hada da Mohammed Salah dan asalin Masar da  Pierre-Emerick Aubameyang, dan asalin Gabon da Naby Keita dan asalin Gini da Sadio Mane dan asalin Senegal da kuma bictor Moses dan asalin Najeriya.

A duk shekara ce gidan rediyon BBC yake shirya irin wannan gasa ga ’yan kwallon Afirka da ke buga kwallo a sassan duniya inda suke ba jama’a musamman masoya kwallon kafa dama wajen kada kuri’a don zabar Gwarzon dan kwallon.

Mohammed Salah, wanda tauraruwarsa ke haskakawa a bana, ya zuwa yanzu shi ne dan kwallon da ya fi  yawan zura kwallaye a gasar rukunin firimiyar Ingila bayan ya zura kwallaye 13.

Haka kuma Salah ne ya taimakawa Masar hayewa gasar cin kofin duniya a Rasha a karon farko tun bayan shekarar 1990 da hakan ta sa aka zabe shi.