Monaco ta ɗauki Paul Pogba
A watan Maris ɗin bara ne aka dakatar da Pogba shekara huɗu, sakamakon zargin shan abubuwan ƙara kuzarin jiki.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Monaco ta ƙulla yarjejeniyar kaka biyu da tsohon ɗan wasan Manchester United da kuma Juventus, Paul Pogba.
Pogba mai shekara 32 ya koma a matakin wanda bai da kwantiragi tun daga watan Nuwamba, bayan da Juventus ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninsu bisa fahimtar juna.
- Nijeriya ce kasa ta 12 mafi talauci a duniya — IMF
- Yadda na hannun daman ’Yar’Adua ya yi tuggun hana ni zama shugaban ƙasa — Jonathan
A watan Maris ɗin bara ne aka dakatar da Pogba shekara huɗu, sakamakon zargin shan abubuwan ƙara kuzarin jiki a wasan ƙungiyar da Udinese.
Amma yanzu zai koma taka leda bayan da aka rage hukuncin zuwa wata 18, sakamakon ɗaukaka ƙara a watan Oktoba.
Ya fara taka leda a Manchester United daga nan ya koma Juventus a 2012.