Monama miliyan shida sun samu irin shinkafa ta tsarin intanet

Kimanin manoma miliyan shida ne suka ci gajiyar sabon irin shinkafa da Gwamnatin Tarayya ta raba ta hanyar yin amfani da tsarin intanet a shekarun baya.Ministan harkokin noma da bunkasa karkara, Audu Ogbeh, shi ne ya yi ikirarin yayin da yake gabatar da jawabi a lokacin kaddamar da shirin hadin gwiwa kan hankokin noma, wanda […]

Monama miliyan shida sun samu irin shinkafa ta tsarin intanet
Monama miliyan shida sun samu irin shinkafa ta tsarin intanet

Kimanin manoma miliyan shida ne suka ci gajiyar sabon irin shinkafa da Gwamnatin Tarayya ta raba ta hanyar yin amfani da tsarin intanet a shekarun baya.
Ministan harkokin noma da bunkasa karkara, Audu Ogbeh, shi ne ya yi ikirarin yayin da yake gabatar da jawabi a lokacin kaddamar da shirin hadin gwiwa kan hankokin noma, wanda kungiyar Synergos Nigeria ta shirya da tallafin cibiyar Bill and Melinda Foundation da kuma Ma’aikatar Harkokin Noma da Bunkasa Karkara, a Abuja.
Ministan, wanda Minista a ma’aikatar, Heineken Lokpobiri ya wakilta, ya ce hakan ya haifar da karuwar girbin shinkafa da ta kai tan miliyan biyu a shekarar 2015.
Ya kara da cewa an samu karuwar shinkafa da kashi biyu a shekarar 2011 zuwa kashi 21 a shekarar 2015.
Ya bayyana cewa a yanzu an samu shinkafar da ta kai tan miliyan daya da dubu arba’in da daya da dari biyu a shekara.
Minsitan ya bayyana cewa gwamnati na sa ran fadada cibiyoyin sheke shinkafa da ta kai ta kimanin tan dubu dari shida da biyu da dari takwas a shekara.
Ya bayyana cewa gwamnati na sa ran bude wasu sababbin cibiyoyin sheke shinkafar guda bakwai a sassa da dama na kasa baki daya.
Ya ci gaba da cewa sababbabin cibiyoyin gyaran shinkafar za su samar da tan dubu dari hudu da talatin da tara a shekara kari a kan sauran cibiyoyin da ake da su a kasa baki daya.
Ya kara da cewa duk wannan ci gaba da aka samu zai taimaka kwarai da gaske wajen tabbatar da dogaro da kai wajen noman shikafa a kasa baki daya.
A ganinsa, ci gaban da aka samu zai dakatar da fasakwaurin shinkafa da ake yi wanda a cewarsa yana da illa ga lafiyar ’yan Najeriya.