MOPPAN ta sulhunta matan Kannywood da Naziru Ahmad
MOPPAN ta yi gaggawar kiran taron sulhun ne kafin lamarin ya kara kazancewa.
Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Najeriya (MOPPAN) ta yi taron sulhu tsakanin Kungiyar Matan Kannywood (K-WAN) da fitaccen mawakin Kannywood kuma jarumi, Naziru M. Ahmad.
Shugaban MOPPAN na kasa, Dokta Ahmad Sarari, shi ne ya kira taron da ya gudana ranar Litinin a Jihar Kano don sulhunta bangarorin biyu a kan rikicin da ya barke a tsakaninsu.
- Masari ya haramta ayyukan kungiyar ’Yan Sa-Kai a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Abin da Abba Kyari Ya Fada Kafin A Kama Shi
Naziru wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Waka ya yi ikirarin cewa akwai wasu lokutan da a Kannywood ba a sanya mace a fim sai ta ba da kanta.
Hakan ce ta fusata K-WAN inda ta ba shi wa’adin kwanaki uku da ya janye wannan kalamin nasa ko kuma ta maka shi a kotun shari’ar Musulunci a kan tuhumar bata suna.
A dalilin haka ne MOPPAN ta yi gaggawar kiran taron kafin lamarin ya kara kazancewa kamar yadda Mujallar Finafinan Kannywood ta ruwaito.
Shugabar K-WAN, Hauwa A. Bello, da shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa (AFMAN), Sani Sule Katsina, na daga cikin mahalarta taron.
Shi ma Naziru Sarkin Waka ya halarta da yayansa, Misbahu M Ahmad, Ibrahim Mandawari, Kabiru Maikaba da sauransu sun halarci taron.
Aminiya ta ruwaito cewa, duk wannan dai na zuwa ne bayan shafe kwanaki ana caccakar juna tare da nuna wa juna yatsa kan maganar kudin da ake biyan jarumai a masana’antar Kannywood wacce Ladin Cima da aka fi sani da Tambaya ta Malam Mamman ko Mama Tambaya kamar yadda abokan aikinta ke kiranta, ta soma.