Morocco ta janye jakadanta daga Najeriya

kasar Morocco ta kira jakadanta daga Najeriya, bayan da hukumomin kasar suka zargi mahukuntan Najeriya da kokarin sanya Sarki Mohammed na 6 na Morocco a cikin harkar yakin neman zaben kasar nan da za a gudanar a wannan wata. Ma’aikatar Harkokin Wajen Morocco ta musanta cewa Sarkin ya tattauna da Shugaba Goodluck Jonathan ta wayar […]

Morocco ta janye jakadanta daga Najeriya
Morocco ta janye jakadanta daga Najeriya

kasar Morocco ta kira jakadanta daga Najeriya, bayan da hukumomin kasar suka zargi mahukuntan Najeriya da kokarin sanya Sarki Mohammed na 6 na Morocco a cikin harkar yakin neman zaben kasar nan da za a gudanar a wannan wata.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Morocco ta musanta cewa Sarkin ya tattauna da Shugaba Goodluck Jonathan ta wayar tarho, kamar yadda aka yayata a Najeriya.
Sai dai Najeriya ta ce an tattauna a tsakanin shugabannin biyu kuma ta musanta zargin cewa tana son amfani da Sarkin ne wajen neman kuri’un Musulmi a zabe mai zuwa.
Morocco ta ce, tana son fadi “da kakkarfar murya cewa babu wata tattaunawa da ta gudana a tsakanin shugabannin biyu. Hakiaka Sarkin ya ki amincewa da bukatar gwamnatin Najeriya ne saboda wani bangare ne na yakin zaben cikin gidanta.” Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Morocco (MAP) ya ruwaito.
Ta kara da cewa, “Masarautar Morocco ta nuna rashin jin dadinta da damuwa kan wannan rashin gaskiya wanda ya saba wa dabi’ar sauke nauyin shugabanci da ya wajaba a tsare a dangantakar kasashen biyu. Sakamakon hakan mun kira Jakadan Morocco daga Abuja nan take domin tattaunawa da shi.”
Fadar Morocco ma ta nuna mamaki kan yadda Najeriya ta shata karyar cewa an tattauna ta tarho a tsakanin Sarki Mohammed na 6 da Shugaban Najeriya alhali ba a yi hakan ba.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta tabbatar da janye Jakadan na Morocco, inda kakakin ma’aikatar Ode Ogbole ya ce ya karanta labarin janye jakadan a kafafen watsa labarai na intanet.
Masana diplomasiyya na ganin matakin na Morocco bai rasa nasaba da batun ’yancin kasar Saharawi da Najeriya ke goyon baya da kuma yadda Najeriya ta juya baya ga batun ba kasar Palasdinu ’yanci a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya.
Shugaba Jonathan zai fafata da Janar Muhammadu Buhari, a zaben Shugaban kasa na ranar 28 ga Maris din nan, lamarin da ake ganin shi ya sa Jonathan ke kokarin nuna akwai kyakkyawar dangantaka a tsakaninsa da kasashen Musulmi don ya samu goyon bayan Musulmin Najeriya a zaben.