Morocco ta zama tawagar farko da ta kai kwata-final a Gasar Kofin Duniya
Morocco za ta kara da Faransa a wasan daf da na kusa da na ƙarshe, bayan da Faransa ta doke Paraguay da ci 1-0.
‘Yan wasan Morocco suna murna a wasan da suka lallasa Canada
Morocco ta zama tawaga ta farko da ta tsallaka zuwa wasan daf da na kusa da na ƙarshe a Gasar Kofin Duniya ta FIFA, bayan ta lallasa Canada da ci 3-0 a wasan zagaye na 16 da aka buga a Houston ranar Asabar.
A halin yanzu, Morocco da Masar ne kaɗai suka rage daga cikin ƙasashen Afirka da ke ci gaba da fafatawa a gasar.
- Boko Haram sun kai hari tare da ƙone motoci 4 a Yobe
- Hayaƙin janareta ya yi ajalin saurayi da budurwa a Kuros Riba
Azzedine Ounahi ne ya zura ƙwallaye biyu na Morocco, kafin wanda ya maye gurbinsa, Soufiane Rahimi, ya ƙara na uku a ƙarshen wasan.
Morocco za ta kara da Faransa a wasan daf da na kusa da na ƙarshe, bayan da Faransa ta doke Paraguay da ci 1-0.
Idan Morocco ta yi nasara a kan Faransa, za ta kai wasan kusa da na ƙarshe a Gasar Kofin Duniya karo na biyu a jere, bayan nasarar da ta samu a gasar ta 2022.
A ɓangaren Canada kuwa, duk da cewa ta buga ɗaya daga cikin manyan wasanninta a tarihin ƙwallon ƙafa, ta zama ƙasa ta farko daga cikin ƙasashen uku masu masaukin baƙuncin gasar da aka fitar daga gasar.
Sauran ƙasashen da ke karɓar baƙuncin gasar, wato Mexico da Amurka, har yanzu ba su buga wasanninsu na zagaye na 16 ba.
Mexico za ta kara da Ingila a ranar Lahadi, yayin da Amurka za ta kara da Belgium a ranar Litinin.