Mota cike da fasinjoji ta fada katuwar kwata a Legas

Wata mota cike da fasinjoji ta fada wata katuwar kwata da ke Oworonsoki a Legas.

Mota cike da fasinjoji ta fada katuwar kwata a Legas

Kwatar da motar ra fada a Legas Hoto: Punch

Wata mota cike da fasinjoji ta fada wata katuwar kwata da ke unguwar Oworonsoki a Jihar Legas.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin fasinjojin sun sami raunuka a hatsarin da ya faru ranar Litinin.

Kazalika, wasu ganau sun ce motar, wacce ba a kai ga tantance yawan mutanen da ke cikinta ba, ta kwace wa direban ne kafin ta fada cikin katuwar kwatar.

Ba a dai kai ga tantance inda motar ke kokarin zuwa ba lokacin da ta fada kwatar.

Yanzu haka dai ma’aikatan ceto na ci gaba da kokarin kai dauki ga fasinjojin da ke cikin motar.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, babu cikakkun bayanai a kan hatsarin.